Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp16 Na 3 p. 3
  • Yadda Za Mu Jimre Sa’ad da Wani Ya Rasu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Mu Jimre Sa’ad da Wani Ya Rasu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Makamantan Littattafai
  • How Can Others Help?
    Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
  • ”Ku Yi Kuka Tare da Masu-Kuka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • How Can I Live With My Grief?
    Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
  • Yadda Za Ka Sami Ta’aziya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
wp16 Na 3 p. 3
Wata tana kuka

ABIN DA KE SHAFIN FARKO

Yadda Za Mu Jimre Sa’ad da Wani Ya Rasu

“Allah ya san abin da ya fi dacewa da mu, ƙawata. . . . Kada . . . ki yi . . . kuka.”

Abin da aka gaya wa wata mai suna Barbara ke nan, sa’ad da ake jana’izar mahaifinta da ya rasu sanadiyyar hatsarin mota.

Barbaraa ta shaƙu da mahaifinta sosai kafin ya rasu. Shi ya sa abin da ƙawarta ta gaya mata bai ta’azantar da ita ba. Ta riƙa tunani cewa: “To, rasuwa ce ta fi dacewa da shi?” Shekaru bayan haka, Barbara ta rubuta abin da ya faru a littafi kuma ta gane cewa har ila, ba ta daina makoki ba.

Barbara ta kuma gane cewa yana ɗaukan lokaci kafin a daina makoki, musamman ma idan an shaƙu sosai da mutumin kafin ya rasu. Littafi Mai Tsarki ya ce mutuwa “magabciyar ƙarshe” ce. (1 Korintiyawa 15:​26, Littafi Mai Tsarki) Mutuwa tana zuwa ba zato ba tsammani kuma hakan yana sa mu baƙin ciki sosai. Ba yadda za mu iya guje mata. Ba abin mamaki ba ne idan muka rasa na yi bayan wani ya rasu.

Wataƙila ka taɓa tunani cewa: ‘Yaushe zan daina makokin nan? Ta yaya zan sami ta’aziya? Yaya zan iya ta’azantar da wasu da suke makoki? Zan ƙara ganin dangina ko abokaina da suka rasu kuwa?’

[Ƙarin bayani]

a An canja sunan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba