Ayyuka na Makon 2 ga Afrilu
MAKON 2 GA AFRILU
Waƙa ta 8 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafuffuka na 158 zuwa 160 (minti 25)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Irmiya 17-21 (minti 10)
Na 1: Irmiya 21:1-10 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Mene ne Yadda Shaiɗan Yake Sarauta Ya Nuna? (minti 5)
Na 3: Sarautar Mulkin Za Ta Soma Yayin da Magabtan Kristi Suke Mulki—td 33B (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 87
Minti 10: Sanarwa. Ka yi amfani da gabatarwa da ke wannan shafin don ka gwada yadda za a soma nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta farko a watan Afrilu.
Minti 15: Bukatu na ikilisiya.
Minti 10: Hanyoyin ba da Mujallunmu a Watan Afrilu. Tattaunawa. Ka yi amfani da minti ɗaya ko biyu don tattauna wasu cikin talifofin da mutane a yankinku za su so. Bayan haka, ka ba ’yan’uwa damar su faɗi tambayar da za su yi wadda za ta sa masu gida su yi sha’awar batun da suke gabatarwa da kuma nassin da za su karanta wanda ya yi daidai da kan maganar da ke bangon Hasumiyar Tsaro. Ka yi hakan da Awake! kuma idan da lokaci ka zaɓi wani talifi dabam a cikin mujallun don ka tattauna shi. Ka sa a gwada yadda za a ba da kowannensu.
Waƙa ta 99 da Addu’a