Anini Biyu
Wata muhimmiyar hanyar da muke tallafa wa ayyukanmu a dukan duniya ita ce ta wurin ba da gudummawa don aikin wa’azi a dukan duniya. Idan ba mu da kuɗi mai yawa fa?
Akwai lokacin da Yesu ya ga wata gwauruwa talaka tana saka gudummawar anini biyu a cikin ma’ajin haikali. Ƙaunar da take yi wa Jehobah ne ya sa ta yi gudummawar “daga talaucinta, . . . iyakar abin zaman garinta.” (Mar. 12:41-44) Abin da Yesu ya faɗa ya nuna cewa Allah ya ɗauki gudummawar da ta bayar da muhimmanci sosai. Hakazalika, Kiristoci a ƙarni na farko sun ɗauki ba da gudummawa a matsayin gata. Shi ya sa Kiristoci mawadata da talakawa duk suka yi gudummawa daidai ƙarfinsu. Manzo Bulus ya ba da misalin ’yan’uwa a Makidoniya, waɗanda duk da ‘talaucinsu ainu sun nace suna roƙon a yarda’ su ba da gudummawa.—2 Kor. 8:1-4.
Saboda da haka, ko da “anini biyu” ne kawai za mu iya bayarwa, bari mu tuna cewa idan aka haɗa waɗannan gudummawar, za su zama kuɗi mai yawa. Idan muka ba da gudummawa da zuciya ɗaya, Ubanmu na sama mai karimci zai yi farin ciki, domin “Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.”—2 Kor. 9:7.