Ta Yaya Ne Za Mu Iya Zaɓan Abokan Kirki?
Jehobah ya halicci ’yan Adam ne su yi cuɗanya da kuma abuta da juna. (Mis. 18:1, 24) Wajibi ne mu zaɓi abokan kirki idan muna son abuta da muke yi ya amfane mu. (Mis. 13:20) Idan ƙaunar Allah ce ta sa mutane suka ƙulla abuta, dangantakarsu za ta yi ƙwari sosai. Misalai 17:17 ta ce: “Aboki kullayaumi ƙauna ya ke yi, kuma an haifi ɗan’uwa domin kwanakin shan wuya.” Sa’ad da abokan kirki suka sami saɓani tsakaninsu, za su bi da juna a hanyar da za ta faranta wa Jehobah rai. Ta yaya za mu iya zaɓan abokan kirki?
Masu iya magana sun ce, zama da maɗaukin kanwa, shi yake kawo farin kai. Saboda haka, yana da muhimmanci mu nuna hikima sa’ad da muke zaɓan waɗanda za mu yi abuta da su. Idan muka ƙulla abuta da waɗanda suke ƙaunar Jehobah kuma muka ƙaunaci waɗanda Allah yake ƙauna, za mu yi abokan kirki. Saboda haka, mu riƙa zaɓan abokan da za su taimaka mana mu kyautata abuta da ta fi muhimmanci a rayuwarmu, wato, dangantakarmu da Allah!—Zab. 15:1, 4; Isha. 41:8.