Tsarin Ayyuka na Makon 29 ga Oktoba
MAKON 29 GA OKTOBA
Waƙa ta 13 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 260 zuwa shafi na 262 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Hosiya 8-14 (minti 10)
Bitar Makarantar Hidima ta Allah (minti 20)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 108
Minti 15: “Yadda Za Ku Amfana Daga Rukuninku na Wa’azi.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Sa’ad da kake tattauna akwatin da ke shafi na 6, ka ɗan gana da wani ɗan’uwa da ya yarda a yi amfani da gidansa don yin taron fita wa’azi. Ta yaya yake shiri kowane mako don a gudanar da taron a gidansa? Me ya sa yake farin ciki cewa ana yin taron fita wa’azi a gidansa?
Minti 15: “Abubuwa Biyar da Za Su Taimaka Mana Mu Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki da Mutane.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Bayan ka tattauna sakin layi na 6, ka ba wa masu sauraro dama su yi kalami a kan yadda Allah ya albarkace su a ƙoƙarin da suka yi na soma nazari da mutane.
Waƙa 122 da Addu’a