Bitar Makarantar Hidima ta Allah
Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 29 ga Oktoba, 2012. An saka kwanan watan da za a tattauna waɗannan bayanan domin ku yi bincike sa’ad da kuke shirya Makarantar Hidima ta Allah kowane mako.
1. Mene ne bagadin da Ezekiyel ya gani a wahayi yake wakilta? (Ezek. 43:13-20) [10 ga Satumba, w07 8/1 shafi na 30 sakin layi na 11]
2. Mene ne ruwan kogin da Ezekiyel ya gani a wahayi yake wakilta? (Ezek. 47:1-5) [17 ga Satumba, w07 8/1 shafi na 31 sakin layi na 3]
3. Kayan lambun da matasa huɗu ’yan Yahuda suka ci ne ya sa fuskarsu ta yi kyau? (Dan. 1:11-15) [24 ga Satumba, w07 9/1 shafi na 18 sakin layi na 5]
4. Mene ne babban icen da Nebuchadnezzar ya gani a mafarkinsa yake wakilta? (Dan. 4:10, 11, 20-22) [1 ga Oktoba, w07 9/1 shafi na 19 sakin layi na 3]
5. Mene ne littafin Daniyel 9:17-19 ya koya mana game da addu’a? [8 ga Oktoba, w07 9/1 shafi na 20 sakin layi na 6-7]
6. Wane alkawari ‘mai ƙwari’ ne ya ci gaba da ci har ƙarshen makonni 70 na shekaru, ko shekara ta 36 A.Z.? (Dan. 9:27) [8 ga Oktoba, w07 9/1 shafi na 20 sakin layi na 5]
7. Mene ne za mu iya kammalawa daga abin da mala’ika ya gaya wa Daniyel cewa “sarkin mulkin Persia” ya yi tsayayya da shi? (Dan. 10:13) [15 ga Oktoba, w11 10/1 shafi na 4, sakin layi na 1-2]
8. Su wane ne ilimin Littafi Mai Tsarki zai sa su “haskaka” a kwanaki na ƙarshe? (Dan. 12:3, 4) [15 ga Oktoba, w10 7/15 shafi na 21 sakin layi na 8]
9. Da Gaske ne cewa Hosea ya auri mace wadda daga baya ta zama fasiƙa? (Hos. 1:2-9) [22 ga Oktoba, w07 10/1 shafi na 13 sakin layi na 6]
10. Wane darasi mai muhimmanci ne ya kamata mu koya daga littafin Hosiya 6:6? [22 ga Oktoba, w07 10/1 shafi na 15 sakin layi na 3; w05 12/1 shafi na 10 sakin layi na 11-12]