Dandalinmu na Intane—An Tsara Shi Ne don ’Yan’uwa da Kuma Wasu Su Amfana
Yesu ya umurce mu cewa mu yi wa’azin bisharar Mulkin a dukan “duniya domin shaida ga dukan al’ummai.” (Mat. 24:14) Don a taimaka mana mu ‘cika hidimarmu,’ an mai da dandali na watchtower.org da jw-media.org da kuma jw.org, zuwa dandali guda. Ƙari ga haka, an canja fasalin dandalin kuma aka ba shi suna jw.org.—2 Tim. 4:5.
“Cikin Iyakar Duniya”: Wajen kashi ɗaya cikin uku na mutanen duniya suna amfani da Intane. Intane ya zama abin yin bincike na musamman wa matasa da yawa. Dandalinmu yana ɗauke da amsoshi na ƙwarai ga tambayoyi game da abubuwan da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, yana ɗauke da bayanai game da ƙungiyarmu kuma mutum zai iya aika saƙo cikin sauƙi cewa yana son nazarin Littafi Mai Tsarki na gida kyauta. Yana sa mutane da suke zama a ɓangarorin duniya da babu Shaidun Jehobah su sami damar jin bisharar Mulkin.
“Dukan Al’ummai”: Wajibi ne mu tanadar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki cikin harsuna dabam-dabam idan har muna son mu ba da shaida ga “dukan al’ummai.” Masu shiga dandalin jw.org za su iya samun bayanai a cikin harsuna wajen 400. Babu wani dandalin da za a sami bayanai a cikin harsuna da yawa kamar dandalinmu.
Ku Yi Amfani da Shi Yadda Ya Dace: Ba a buɗe wannan sabon Dandalin jw.org don yi wa mutane wa’azi kawai ba. Shaidun Jehobah ma za su amfana daga dandalin. Idan kuna shiga Intane, muna ƙarfafa ku ku shiga dandalin jw.org. Ga yadda za a yi amfani da shi.
[Hotunan da ke shafi na 3]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
Ku Gwada Shiga Dandalin
1 Ku rubuta www.pr418.com a wannan fili da ake sa adireshi a shafin Intane daga kwamfutarku.
2 Ku bincika dandalin ta wajen shiga duk wani kan magana da kuke so a saman shafin ko a gefen shafin ko kuma a cikin shafin.
3 Ku gwada shiga dandalin jw.org da waya mai Intane ko kuma wata na’urar tafi da gidanka. Shafin zai daidaita kansa da fuskar ƙaramar na’urar, amma bayanan da ke ciki ɗaya ne.