Tsarin Ayyuka na Makon 28 ga Janairu
MAKON 28 GA JANAIRU
Waƙa ta 29 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 300 zuwa shafi na 302 sakin layi na 8 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Matta 16-21 (minti 10)
Na 1: Matta 17:22–18:10 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Mene Ne ‘Alherin’ Jehobah da Joshua Ya Ga Cikarsa?—Josh. 23:14 (minti 5)
Na 3: Ba Mu Tsira Ba Idan Muka Ci Gaba da Yin Zunubi Bayan Mun Samu Ceto—td 12B (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 134
Minti 5: Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko. Ka sa a yi amfani da gabatarwar da ke shafi na 4, don gwada yadda za a soma nazari a Asabar ta farko a watan Fabrairu. Ka ƙarfafa dukan ’yan’uwa su yi hakan.
Minti 25: “Fiye da Kome Kuma, Ku Himmantu ga Ƙaunar Juna Gaya.” Sashen tambayoyi da amsoshi da aka ɗauko daga ƙasidar nan, Ka Zauna a Faɗake! A Kan Me? Me Ya Sa Ya Fi Gaggawa Yanzu? Ka gabatar da sashen ta wajen tattauna bayanin da ke sakin layi na ɗaya. Ta wajen amfani da tambayoyi don nazari da ke shafi na 31, ka tattauna sakin layi na 1-20 da ke shafuffuka na 28-31. Ka kammala ta wajen tattauna bayanin da ke sakin layi na ƙarshe. Ka ƙarfafa ’yan’uwa su kalli bidiyon nan Our Whole Association of Brothers don su sami ƙarin bayani.
Waƙa ta 53 da Addu’a