“Fiye da Kome Kuma, Ku Himmantu ga Ƙaunar Juna Gaya”
Ƙauna da kuma zumunci da muke mora tsakanin ’yan’uwa albarka ne daga Jehobah. (Zab. 133:1) Shi ya sa kusan shekaru dubu biyu da suka shige, manzo Bitrus ya rubuta cewa: “Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. Saboda haka sai ku kame kanku, ku natsu, domin ku yi addu’a. Fiye da kome kuma, ku himmantu ga ƙaunar juna gaya.” (1 Bit. 4:7, 8, Littafi Mai Tsarki) Muna morar dangantaka mai kyau da ’yan’uwa da suke kama da iyayenmu da kuma ’yan’uwa da muka fito daga gida ɗaya domin muna cikin ƙungiyar Jehobah. (Mar. 10:29, 30) Duk da haka, saboda yanayi dabam-dabam, saɓani yakan taso tsakanin mu da ’yan’uwanmu. Shin, me za mu yi don mu ci gaba da ƙaunar ’yan’uwanmu a wannan duniyar da rashin ƙauna ta zama ruwan dare? Wannan sashen taron zai taimaka mana mu fahimci ma’anar shawarar da manzo Bitrus ya bayar a 1 Bitrus 4:7, 8. Ƙari ga haka, zai taimaka mana mu nuna ƙauna ga ’yan’uwanmu Kiristoci da kuma wasu.
Muna ƙaunar juna musamman domin “ƙauna ta Allah ce.” (1 Yoh. 4:7) Ƙauna abu ne mai kyau kuma Jehobah ne Tushenta. Jehobah ya aiko Ɗansa ya mutu a kan gungumen azaba “domin mu rayu ta wurinsa,” saboda haka, shi ne ya fara ƙaunar mu. (1 Yoh. 4:9) Ta yaya za mu nuna cewa muna nuna godiya don irin ƙaunar da Allah ya nuna mana? Littafin 1 Yohanna 4:11 ya ce: “Masoya, idan Allah ya ƙaunace mu haka nan, ya kamata mu kuma mu yi ƙaunar junanmu.” (1 Yoh. 4:11) Saboda haka, ba taimakon Jehobah muke yi ba sa’ad da muka yi ƙaunar ’yan’uwanmu. A maimakon haka, shi yake taimakon mu shi ya sa ya kamata mu yi masa godiya domin yadda ya albarkace mu da haɗin kai da kuma zumunci a cikin ƙungiyarsa. Ƙari ga haka, muna nuna wa maƙwabtanmu ƙauna ta wajen gaya musu “bishara ta alheri” domin muna musu kallon waɗanda za su iya zama masu bauta wa Jehobah a nan gaba. (Isha. 52:7) Yayin da muke gab da ƙarshen wannan duniya da babu ƙauna, bari mu ci gaba da nuna ƙauna musamman ga ’yan’uwanmu duka a faɗin duniya!