Tsarin Ayyuka na Makon 27 ga Mayu
MAKON 27 GA MAYU
Waƙa ta 6 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 6 sakin layi na 11-18 da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Yohanna 12-16 (minti 10)
Na 1: Yohanna 12:20-36 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Yadda Muka Amfana Daga Rahamar Allah—td 32C (minti 5)
Na 3: Me Ya Sa Aka Kira Jehobah “Allah na Salama”?—Rom. 15:33 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 98
Minti 5: Ku Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko. Jawabi. Ka sa a nuna yadda za a iya amfani da bangon baya na Hasumiyar Tsaro wajen soma nazari a Asabar ta farko a watan Yuni. Ka ƙarfafa dukan ’yan’uwa su gwada hakan a wannan watan.
Minti 15: Yin Ban Ruwa ga Irin da Muka Shuka. (1 Kor. 3:6-9) Ka tattauna waɗannan tambayoyin da ke gaba: (1) Me yake sa ku farin ciki sa’ad da kuka koma ku ziyarci mutane? (2) Waɗanne ƙalubale ne kuke fuskanta sa’ad da kuka koma ku ziyarci mutane? (3) Ta yaya za ku shawo kan waɗannan ƙalubalen? (4) Ta yaya za mu sami taimako idan yana mana wuya mu koma don mu ziyarci mutane? (5) Mene ne kuke yi don ku tuna suna da adireshin wani da yake sha’awar saƙonmu da batun da kuka tattauna da shi da littattafan da kuka ba shi da dai wasu bayanai? (6) A wace hanya ce kuke yin shiri don koma ziyara? (7) Me ya sa yake da kyau ku ware lokaci a kowane mako don ku koma ku ziyarci mutane?
Minti 10: “Ku Yi Amfani da Bidiyo Wajen Koyarwa.” Tattaunawa. Ka gayyaci masu sauraro su faɗi yadda suka amfana wajen kallon bidiyonmu kafin su zama Shaidu.
Waƙa ta 101 da Addu’a