Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 12/14 pp. 2-3
  • Yadda Za Mu Gudanar da Nazari da Kyau

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Mu Gudanar da Nazari da Kyau
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Taimaka wa Dalibinka Ya Cancanci Yin Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Yadda Za Ka Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma—Sashe na Biyu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ka Mai Da Hankali Ga ‘Iyawarka Ta Koyarwa’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yadda Za Ka Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma​—Sashe na Daya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 12/14 pp. 2-3

Yadda Za Mu Gudanar da Nazari da Kyau

1. Wane hakki ne masu shela suke da shi yayin da suke yin nazari da mutane?

1 Babu mutumin da zai iya bauta wa Jehobah idan Jehobah bai “jawo shi” ba. (Yoh. 6:44) Duk da haka, wajibi ne masu shela su yi iyakacin ƙoƙarinsu wajen taimaka wa mutane su kusaci Ubansu wanda ke cikin sama. (Yaƙ. 4:8) Hakan zai bukaci yin shiri sosai. Karanta sakin layi da kuma yin tambayoyin da ke cikin littafin kawai ba zai taimaka wa ɗalibanmu su fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma su sami ci gaba ba.

2. Idan muka gudanar da nazari da kyau, mene ne za mu cim ma?

2 Gudanar da nazari da ɗalibanmu da kyau ya ƙunshi taimaka musu (1) su fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki, (2) su yarda da koyarwar Littafi Mai Tsarki, kuma (3) su bi koyarwar Littafi Mai Tsarki. (Yoh. 3:16; 17:3; Yaƙ. 2:26) Zai iya ɗaukan watanni kafin mu taimaka wa ɗalibinmu ya bi waɗannan matakan. Amma, kowannensu zai taimaka masa a dangantakarsa da Jehobah kuma ya sa ya keɓe kansa don yin nufin Jehobah.

3. Mene ne ƙwararrun malamai za su cim ma ta wajen yi wa ɗalibansu tambayoyin da za su sa su faɗi ra’ayinsu?

3 Mene Ne Ra’ayin Ɗalibin?: Idan muna so mu san ko ɗalibinmu yana fahimtar abin da yake koya kuma ya yarda da shi, wajibi ne mu ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa, maimakon mu yi ta masa jawabi. (Yaƙ. 1:19) Shin ya fahimci bayanin Littafi Mai Tsarki a kan batun da kuke tattaunawa? Zai iya yin bayani a kan batun ba tare da karantawa daga cikin littafinsa ba? Mene ne ra’ayinsa a kan abin da ya koya? Shin ya yarda cewa koyarwar Littafi Mai Tsarki tana da amfani? (1 Tas. 2:13) Shin ya fahimci cewa ya kamata ya yi gyara a rayuwarsa saboda abubuwan da yake koya? (Kol. 3:10) Domin mu cim ma waɗannan maƙasudan, muna bukatar mu yi tambayoyin da za su sa ɗalibanmu su faɗi ra’ayinsu sa’an nan mu saurari amsarsu.—Mat. 16:13-16.

4. Me ya kamata mu yi idan yana yi wa ɗalibinmu wuya ya fahimci wani batu ko kuma ya bi abin da ya koya daga Littafi Mai Tsarki?

4 Ba shi da sauƙi mutum ya canja halinsa ko kuma yadda ya saba tunani. (2 Kor. 10:5) To idan ɗalibinmu bai yarda da abin da ya koya ba ko kuma ya ƙi yin amfani da shi fa? Muna bukatar mu ba shi lokaci don Kalmar Allah ta ratsa zuciyarsa kuma ruhu mai tsarki ya taimaka masa. (1 Kor. 3:6, 7; Ibran. 4:12) Maimakon mu tilasta masa ya fahimci batun ko kuma ya bi koyarwar Littafi Mai Tsarki, zai fi kyau mu bar wannan batun kuma mu ci gaba da nazarin. Yayin da muka ci gaba da koyar da shi cikin haƙuri da ƙauna, mai yiwuwa a kwana a tashi zai yi gyarar da ta dace.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba