Tsarin Ayyuka na Makon 22 ga Disamba
MAKON 22 GA DISAMBA
Waƙa ta 15 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 17 sakin layi na 17-23 da akwatin da ke shafi na 177 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Joshua 9-11 (minti 10)
Na 1: Joshua 9:16-27 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Kada Miji Ya Yarda Matarsa Ta Hana Shi Bauta wa Allah—td 21C (minti 5)
Na 3: Ya Kamata Abokanmu Su Ƙaunaci Allah—lr babi na 44 (minti 5)
Taron Hidima:
JIGON WATA: Ku fito da abubuwa “masu kyau” daga ajiya mai kyau da aka ba mu.—Mat. 12:35a.
Waƙa ta 119
Minti 5: Bukatun ikilisiya.
Minti 25: “Makarantar Hidima ta Allah ta 2015 Za Ta Taimaka Mana Mu Kyautata Koyarwarmu.” Mai Kula da Makarantar Hidima ta Allah ne zai tattauna wannan sashen. Idan ya so, ya sa a karanta wasu sakin layi kafin a tattauna su. Ka yi magana a kan gyarar da aka yi a kan Jawabi Na 1, da lokacin da aka ƙayyade don tattauna darussa daga Karatun Littafi Mai Tsarki, da kuma shawarar da mai kula da makaranta zai bayar. Ka sa a karanta sakin layi na 7, kuma bayan an tattauna shi, ka sa wani dattijo ya nuna yadda yake gudanar da ibada ta iyali da matarsa da yaransa, kuma ya yi amfani da ƙasidar nan Abubuwan da Za Mu Koya Daga Kalmar Allah, shafi na 14. Ka ƙarfafa dukan masu shela su yi amfani da abin da ake koya mana a Makarantar Hidima ta Allah kuma su riƙa amfani da littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education.
Waƙa ta 117 da Addu’a