Makarantar Hidima ta Allah ta 2015 Za Ta Taimaka Mana Mu Kyautata Koyarwarmu
1 Dauda marubucin zabura ya ce: “Bari batutuwan bakina, da tunanin zuciyata, su zama abin karɓa a gare ka, Ya Ubangiji, dutsena da mai-fansana.” (Zab. 19:14) Mu ma muna so furucinmu ya zama abin karɓa ga Jehobah domin gata ne babba a gare mu mu furta kalmomin gaskiya a cikin ikilisiya da kuma sa’ad da muka fita wa’azi. Makarantar Hidima ta Allah tana ɗaya daga cikin hanyoyin da Jehobah yake koyar da mu don wa’azi. Ana gudanar da wannan makarantar kowane mako a ikilisiyoyi sama da 111,000 a faɗin duniya. Makarantar ta taimaka wa ’yan’uwa maza da mata daga al’adu da kuma yanayin rayuwa dabam-dabam su zama ƙwararrun masu shela da suka iya koyarwa da hujjoji masu kyau da basira da kuma gaba gaɗi.—A. M. 19:8; Kol. 4:6.
2 An ɗauko batutuwan da ke cikin tsarin ayyuka na 2015 ne daga ƙasidar nan “Abubuwan da Za Mu Koya Daga Kalmar Allah” da Littafi Mai Tsarki da kuma Hasumiyar Tsaro [wp]. Ƙari ga haka, an yi gyara a yawan lokacin da aka ayyana don tattauna darussa daga Karatun Littafi Mai Tsarki da kuma Jawabi na 1. Sakin layin da ke gaba suna ɗauke da waɗannan gyarar da kuma umurni a kan yadda za a gudanar da makarantar.
3 Darussa Daga Karatun Littafi Mai Tsarki: Ɗan’uwan da aka ba shi wannan jawabin zai tattauna darasi guda mai kyau daga karatun Littafi Mai Tsarki na makon cikin minti biyu daidai. Idan ya shirya da kyau, zai tattauna darasin da zai amfani ikilisiyar cikin lokacin da aka ayyana masa. Bayan haka, za a ba masu shela minti shida don su yi kalami cikin sakan 30 ko ƙasa da hakan a kan darussa masu kyau da suka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na makon. Yin kalami mai kyau cikin sakan 30 zai bukaci mu shirya da kyau kuma mu guji yin dogon bayani. Hakan kuwa horarwa ce mai kyau kuma zai ba ’yan’uwa da yawa damar faɗin darussan da suka koya daga binciken da suka yi.
4 Jawabi Na 1: An rage yawan lokacin da aka ayyana don karatun Littafi Mai Tsarki zuwa minti uku ko ƙasa da hakan kuma an rage yawan ayoyin da za a karanta. Ya kamata waɗanda za su yi karatu su karanta nassin sau da sau kuma su saurari kansu yayin da suke hakan don su ji yadda suke furta kalmomi kuma su tabbata cewa karatun ya fita sarai yadda za a fahimta. Zai dace dukan mutanen Jehobah su ƙoƙarta su iya karatu da kyau da yake karatu yana da muhimmanci a ibadarmu. Hakika muna murna sosai domin yadda yaranmu suke karatu da kyau! Muna yaba wa iyaye don yadda suke taimakon yaransu su iya karatu.
5 Jawabi Na 2: Wannan jawabi ne na minti biyar da za a ba ’yar’uwa. Ya kamata ta yi bayani a kan jigon da aka ba ta. Idan jawabin daga ƙasidar nan Abubuwan da Za Mu Koya Daga Kalmar Allah ne, to ta yi amfani da wani tsari na yin wa’azi a yankin kuma ta yi shi yadda zai dace da yanayin yankin. Za ta iya karanta nassosi da suke da nasaba da batun da suke tattaunawa. Mai kula da makaranta zai ba ta mataimakiya guda.
6 Jawabi Na 3: Wannan jawabi ne na minti biyar da za a iya ba ɗan’uwa ko ’yar’uwa. Idan ’yar’uwa ce aka ba wannan jawabin, ta yi shi yadda ake yin Jawabi Na 2. Idan kuma ɗan’uwa ne, ya gudanar da shi yadda maza suke yin jawabi kuma ya shirya shi yadda zai amfani masu sauraro. Ɗalibin ya yi bincike a kan jawabin kuma ya yi amfani da nassosin da suka dace.
7 Sabon Salon Yin Jawabi Na 3 don ’Yan’uwa Maza: Idan jawabin daga ƙasidar nan Abubuwan da Za Mu Koya Daga Kalmar Allah ne, ɗan’uwan zai yi jawabin kamar yana gudanar da ibada ta iyali ko kuma yana wa’azi. A yawancin lokatai mai kula da makaranta ne zai ba ɗalibai mataimakinsu da kuma tsarin da za su yi amfani da shi. Mataimakin ya zama wani daga iyalin ɗalibin ko kuma wani ɗan’uwa a cikin ikilisiyar. Ɗalibin zai iya yin amfani da ƙarin nassosi da za su ba da ƙarin haske a kan batun da yake tattaunawa. A wasu lokatai za a ba dattawa wannan jawabin, kuma dattawan ne za su zaɓi mataimakinsu da tsarin da za su yi amfani da shi. Babu shakka, ikilisiya za ta ƙarfafa sosai da ganin dattawa suna yin gwaji tare da wani a cikin iyalinsu ko kuma ikilisiya don nuna yadda ake koyarwa.
8 Shawara: Bayan kowane jawabi, mai kula da makarantar ya yi amfani da minti biyu ya yaba wa ɗalibin kuma ya ba da shawara daidai yadda ya dace, bisa ga abin da ke cikin littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education. Sa’ad da mai kula da makaranta yake gabatar da ɗalibi, kada ya ambata abin da ake bukatar ɗalibin ya yi aiki a kai. Amma bayan ɗalibin ya gama aikinsa, mai kula da makarantar ya yaba masa kuma ya ambata sashen da aka ba ɗalibin ya yi aiki a kai. Ƙari ga haka, zai ambata abin da ya sa ɗalibin ya yi aikinsa da kyau ko kuma dalilin da ya sa zai dace ɗalibin ya daɗa yin ƙoƙari a wannan fannin.
9 Kowane ɗalibi yana iya samun fom ɗin shawara a cikin nasa littafin Benefit From Theocratic Ministry School Education a shafuffuka na 79 zuwa 81. Bayan ɗalibi ya yi jawabinsa, mai kula da makaranta zai shigar da bayanin da ya dace a cikin littafin ɗalibin kuma bayan taron zai tambayi ɗalibin ko ya yi aikin da ke cikin sashen da aka ba shi. Bayan taron ko kuma a wani lokaci dabam, mai kula da makarantar zai yaba wa ɗalibin ko kuma ya ba shi shawarar da za ta taimaka masa. Ya kamata yabawa da kuma shawarar da kowane ɗalibi yake samu su taimaka masa ya sami ci gaba.—1 Tim. 4:15.
10 Idan ɗalibi ya ci lokaci, mai kula da makarantar ko kuma wani da aka zaɓa ya buga ƙararrawa ko dai wani abin da zai ɗan yi ƙara don ya sanar da ɗalibin cewa lokacinsa ya ƙure. Ɗalibin ya ba da haɗin kai ta wajen kammala jimlar da yake yi sa’an nan ya bar dakalin.—Ka duba littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 282, sakin layi na 4.
11 Ana ƙarfafa dukan waɗanda suka cancanci shiga Makarantar Hidima ta Allah su yi hakan. (Ka duba littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 282, sakin layi na 6.) Wannan makarantar ta taimaka wa mutanen Jehobah su ƙware a koyarwa da kuma yin shelar bisharar Mulkin Allah da gaba gaɗi da ladabi kuma cikin ƙauna. Hakika, waɗanda suke amfana daga koyarwar Allah suna kawo ɗaukaka ga Jehobah kuma hakan yana faranta masa rai sosai.—Zab. 148:12, 13; Isha. 50:4.
Ka riƙa bin shawara don ka sami ci gaba