Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp20 Na 3 p. 6
  • Ta Yaya Mahaliccinmu Ya Bayyana Mana Abin da Zai Yi?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Mahaliccinmu Ya Bayyana Mana Abin da Zai Yi?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • AKWAI NASSOSI MASU TSARKI A KO’INA
  • Wane Irin Littafi Ne Baibul?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • ‘Ruhu Mai Tsarki ne Ya Motsa Su’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Littafi Mai Tsarki Sako Ne Daga Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Mene ne Ma’anar Kalmar Nan Annabci?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
wp20 Na 3 p. 6
Wani dan kasuwa yana gaya wa sakatarensa abin da zai rubuta a cikin wasika, sakataren kuma yana rubutawa a kwamfuta.

Kamar yadda ɗan kasuwa yake amfani da sakatarensa don ya rubuta saƙo, haka ma Allah ya yi amfani da maza masu aminci ya sa su rubuta saƙonsa a cikin Nassosi Masu Tsarki

Ta Yaya Mahaliccinmu Ya Bayyana Mana Abin da Zai Yi?

Tun lokacin da Allah ya halicci mutane, ya soma magana da su ta wurin mala’iku da kuma annabawa. Ƙari ga haka, ya sa an rubuta saƙonsa ga ’yan Adam da kuma alkawuran da ya yi musu. Allah ya gaya mana cewa za mu iya yin farin ciki a nan gaba. To, a ina ne za ka ga alkawuran da Allah ya yi mana a yau?

A cikin Nassosi Masu Tsarki ne aka rubuta alkawuran Allah. (2 Timoti 3:16) Ta yaya Allah ya sa annabawa su rubuta saƙonsa? (2 Bitrus 1:21) Allah ya taimaka musu su san saƙon ta hanyar mu’ujiza, sa’an nan suka rubuta shi. Za mu iya kwatanta shi da abin da manyan ’yan kasuwa sukan yi a yau. Idan ɗan kasuwa yana so ya aika saƙo, yakan sa sakatarensa ya rubuta masa saƙon. Ko da yake sakataren ne ya rubuta, saƙon na ɗan kasuwan ne. Hakazalika, duk da cewa Allah ya yi amfani da mutane su rubuta saƙon da ke cikin Nassosi Masu Tsarki, saƙon da ke ciki nasa ne.

AKWAI NASSOSI MASU TSARKI A KO’INA

Saƙon da Allah ya turo mana yana da amfani sosai, shi ya sa Allah ya tabbata cewa “kowace al’umma, da zuriya da yare,” sun same saƙon. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 14:⁠6) Ana samun Nassosi Masu Tsarki, gabaki ɗayansu ko rabinsu a yaruka fiye da 3,000. Allah ne ya sa hakan ya yiwu. Babu wani littafin da aka fassara zuwa yaruka da yawa haka a duniya.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba