Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp20 Na 3 pp. 4-5
  • Mahaliccinmu Mai Ƙauna Ya Damu da Mu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mahaliccinmu Mai Ƙauna Ya Damu da Mu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • 1. MAHALICCINMU NE YAKE SA RANA TA YI HASKE
  • 2. MAHALICCINMU NE YAKE SA A YI RUWAN SAMA
  • 3. MAHALICCINMU NE YAKE BA MU ABINCI DA RIGUNA
  • Ka Bidi Mulkin Allah, Ba Abin Duniya Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Wanda Ya Halicci Dukan Abubuwa
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
wp20 Na 3 pp. 4-5
Fitowar rana daga kan tuddai.

Mahaliccinmu Mai Ƙauna Ya Damu da Mu

1. MAHALICCINMU NE YAKE SA RANA TA YI HASKE

Da a ce babu hasken rana, ya kake ganin rayuwa za ta kasance? Hasken rana ne yake taimaka wa itatuwa su fitar da ganyaye da furanni kuma su ba da ’ya’ya. Ƙari ga haka, rana tana taimaka wa itatuwa su ja ruwa daga ƙasa zuwa ganyayensu ta jijiyoyinsu, a ƙarshe, sai ruwan ta fita ta bi iska.

Hoton gonar shayi a kan tudu da aka dauka daga sama.

2. MAHALICCINMU NE YAKE SA A YI RUWAN SAMA

Allah ne yake ba da ruwan sama, kuma ruwa ne yake sa mu sami abinci. Allah yana ba mu ruwan sama da damina mai albarka, yana ƙosar da mu da abinci, kuma yana sa mu yi farin ciki.

Wani tsuntsu a kan itace yana kokarin cafke ’ya’yan itace da suke fadowa.

3. MAHALICCINMU NE YAKE BA MU ABINCI DA RIGUNA

Magidanta da yawa sukan damu a kan yadda za su samar wa iyalansu abinci da sutura. Nassosi Masu Tsarkia sun ce: “Ku dubi tsuntsaye mana, ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa tara a rumbuna. Duk da haka Ubanku na sama ne yake ciyar da su. Ba ku fi su daraja ba?”​—Matiyu 6:​25, 26.

“Ku dubi fulawar daji yadda suke girma . . . , ina gaya muku, ko Sarki [Sulemanu] da dukan darajarsa, bai taɓa ado kamar ɗaya daga cikinsu ba. To, idan har Allah zai yi wa ciyawar daji ado haka . . . , balle ku?”​—Matiyu 6:​28-30.

Tun da Allah zai iya ba mu abinci da sutura, ba shakka, zai iya taimaka mana mu sami abin biyan bukata. Idan muna yin abin da Allah yake so, zai iya taimaka mana mu sami abinci ko ya taimaka mana mu sami aikin da zai ba mu abin biyan bukata.​—Matiyu 6:​32, 33.

Hakika idan muka yi tunani a kan rana da ruwan sama da tsuntsaye da kuma furanni, za mu ga ƙwaƙƙwarar dalilin da zai sa mu ƙaunaci Allah. A talifi na gaba, za mu ga abin da Mahaliccinmu ya yi don ya isar da saƙonsa ga ’yan Adam.

a A duk inda aka ambata Nassosi Masu Tsarki, ana nufin Attaura da Zabura da Linjila.

Mahaliccinmu yana “sa rana ta yi haske” kuma yana aiko da “ruwan sama.”​—MATIYU 5:45

Mahaliccinmu yana ƙaunarmu sosai kuma ya damu da mu. Yana kula da mu kamar yadda uba mai ƙauna yake kula da iyalinsa. A Nassosi Masu Tsarki, an kwatanta Allah a matsayin Mai karimci, wanda “ya san abin da kuke bukata kafin ma ku roƙe shi.”​—Matiyu 6:8.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba