DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZAKARIYA 1-8
‘Ku Riƙe Rigar Bayahude’
8:20-23
Maza goma daga cikin dukan harsunan al’ummai za su kama rigar Bayahude, su ce: “Za mu tafi tare da ku.” A waɗannan kwanaki na ƙarshe, mutane daga dukan al’umma sun soma bauta wa Jehobah tare da shafaffu
A waɗanne hanyoyi ne waɗansu tumaki suke goyon bayan shafaffu a yau?
Suna yin wa’azi da zuciya ɗaya
Suna tallafa wa aikin da gudummawar kuɗi