Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 1/15 pp. 24-28
  • Sun Sami Cancantar Samun Ja-gora Zuwa Maɓulɓulan Ruwaye Na Rai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sun Sami Cancantar Samun Ja-gora Zuwa Maɓulɓulan Ruwaye Na Rai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Taro Mai Girma Sun Nuna Bangaskiyarsu
  • Ceto Daga Cikin Tsanani Zuwa Sabuwar Duniya
  • Taro Mai Girma a Gaban Kursiyin Jehovah
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Su Waye Ne Taro Mai Girma?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Taro Mai Girma Suna Yabon Allah da Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Sun Cancanci Samun Mulki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 1/15 pp. 24-28

Sun Sami Cancantar Samun Ja-gora Zuwa Maɓulɓulan Ruwaye Na Rai

“Ɗan rago . . . za ya bishe su kuma wurin maɓulɓulan ruwaye na rai.”—R. YOH. 7:17.

1. Ta yaya Kalmar Allah ta bayyana shafaffun Kiristoci, kuma wane hakki ne Yesu ya ba su?

KALMAR ALLAH ta kira shafaffun Kiristocin da suke kula da abubuwa na Kristi a duniya “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” Sa’ad da Kristi ya bincika “bawan nan” a shekara ta 1918, ya ga cewa waɗannan shafaffu a duniya suna da aminci wajen yin tanadin “abincinsu [na ruhaniya] a lotonsa.” Shi ya sa Shugabansu, Yesu, ya naɗa su “bisa dukan mallaka tasa.” (Ka karanta Matta 24:45-47.) Saboda haka, shafaffu suna yi wa masu bauta wa Jehobah a nan duniya hidima kafin su sami gadōnsu na samaniya.

2. Ka kwatanta mallakar Yesu.

2 Shugaba yana da iko a kan dukiyarsa, kuma yana iya yin amfani da su yadda ya ga dama. Mallakar Yesu Kristi, Sarkin da Jehobah ya naɗa ta ƙunshi dukan abubuwan Mulki da ke duniya. Wannan ya ƙunshi “taro mai-girma” da manzo Yohanna ya gani a wahayi. Yohanna ya kwatanta taro mai girma kamar haka: “Duba, . . . ga taro mai-girma, wanda ba mai-ƙirgawa, daga cikin kowane iri, da dukan kabilai da al’ummai da harsuna, suna tsaye gaban kursiyin da gaban Ɗan ragon, suna yafe da fararen riguna, da ganyayen dabino cikin hannuwansu.”—R. Yoh. 7:9.

3, 4.Ta yaya taro mai girma suke da gata na musamman?

3 Waɗanda suke cikin taro mai girma sune Yesu ya kira ‘waɗansu tumakina.’ (Yoh. 10:16) Suna da begen zama a aljanna a duniya har abada. Suna da tabbaci cewa Yesu “za ya bishe su . . . wurin maɓulɓulan ruwaye na rai” kuma “Allah kuma zai share musu dukan hawaye.” Domin wannan begen sun “wanke rigunansu, suka faranta su cikin jinin Ɗan ragon.” (R. Yoh. 7:14, 17) Sun ba da gaskiya ga hadayar Yesu kuma saboda haka suna sanye da ‘fararen riguna.’ Sun zama masu adalci da yake su abokan Allah ne kamar Ibrahim.

4 Bugu da ƙari, tun da yake Allah yana ɗaukan taro mai girma na waɗansu tumaki da ke ƙaruwa masu adalci ne, suna da begen samun tsira a halakar wannan zamani a lokacin babban tsanani. (Yaƙ. 2:23-26) Suna iya kusantar Jehobah, kuma a matsayin rukuni suna da bege mai kyau na tsira a Armageddon. (Yaƙ. 4:8; R. Yoh. 7:15) Taro mai girma ba wani rukuni ba ne dabam, amma sun yarda su yi bauta a ƙarƙashin ja-gorancin Sarki na samaniya da kuma ’yan’uwansa shafaffu da ke duniya.

5. Ta yaya ne waɗansu tumaki suke goyon bayan shafaffu ’yan’uwan Kristi?

5 Shafaffun Kiristoci sun fuskanci hamayya kuma za su ci gaba da fuskantar hakan daga duniyar Shaiɗan. Duk da haka, suna iya dogara ga taimakon abokansu taro mai girma. Da yake shafaffu Kiristoci kaɗan ne suka rage a yanzu, taro mai girma suna ƙaruwa sosai a kowace shekara. Shafaffu ba za su iya kula da kowace ikilisiyoyi 100,000 da ke dukan duniya ba. Wani taimakon da shafaffu suke samu daga wajen waɗansu tumaki shi ne, mazan da suka ƙware a cikin taro mai girma suna hidima a matsayin dattawa na ikilisiya. Suna taimaka wa wajen kula da miliyoyin Kiristocin da ke ƙarƙashin kulawar “bawan nan mai-aminci mai-hikima.”

6. Ta yaya ne aka annabta taimakon da wasu tumaki suke ba shafaffun Kiristoci?

6 Annabi Ishaya ya annabta goyon baya na son rai da waɗansu tumaki suke ba shafaffun Kiristoci. Ya rubuta: “Hakanan Ubangiji ya faɗi, Ɗawainiyar Masar, da kayan ciniki na Kush, da su Sabeanawa, dogayen mutane, duk za su ƙetaro su zo wurinka, su zama naka kuma; za su bi bayanka.” (Isha. 45:14) A alamance, Kiristocin da suke da begen zama a duniya a yau suna bin rukunin shafaffen bawa da kuma Hukumar Mulki ta wajen bin shugabancinsu. A matsayinsu na masu “ɗawainiya,” waɗansu tumaki da son rai da kuma dukan zuciyarsu suna amfani da ƙarfinsu da dukiyarsu don tallafa wa aikin wa’azi na dukan duniya da Kristi ya ba shafaffun mabiyansa da ke duniya.—A. M. 1:8; R. Yoh. 12:17.

7. Menene ake koya wa taro mai girma?

7 Yayin da suke taimaka wa ’yan’uwansu shafaffu, ana koyar da taro mai girma don su zama tushen sabuwar al’ummar da za ta rayu bayan Armageddon. Dole ne wannan tushen ya kasance mai ƙwari, kuma waɗanda suke cikinsa suna bukatar su ba da kansu kuma su bi umurnin Shugabansu. An ba kowane Kirista damar ya nuna cewa zai yi abin da Sarki, Yesu Kristi, ya ce. Ta wajen ba da gaskiya da kuma nuna aminci a yanzu, Kirista zai nuna cewa zai saurara sosai sa’ad da Sarkin ya ba shi umurni a sabuwar duniya.

Taro Mai Girma Sun Nuna Bangaskiyarsu

8, 9. Ta yaya ne taro mai girma suke nuna bangaskiyarsu?

8 Wasu tumaki abokan shafaffun Kiristoci sun nuna bangaskiyarsu a hanyoyi masu yawa. Na farko, suna tallafa wa shafaffu wajen sanar da bisharar Mulkin Allah. (Mat. 24:14; 28:19, 20) Na biyu, sun ba da kansu da son rai su bi umurnin da Hukumar Mulki yake tanadinsa.—Ibran. 13:17; Ka karanta Zechariah 8:23.

9 Na uku, babban taro suna tallafa wa ’yan’uwansu shafaffu ta wajen bin mizanai masu adalci na Jehobah. Suna iya ƙoƙarinsu su nuna “ƙauna . . . , farinciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, [da] kamewa.” (Gal. 5:22, 23) A yau, wataƙila nuna irin waɗannan halayen maimakon “ayyukan jiki” ba sanannen abu ba ne. Duk da haka, taro mai girma sun ƙudurta cewa za su guje wa “fasikanci . . . , ƙazanta, lalata, bautar gumaka, sihiri, magabtaka, husuma, kishe-kishe, hasala, tsatsaguwa, rabuwa, hamiya, hasada, maye, nishatsi da irin waɗannan.”—Gal. 5:19-21.

10. Wane ƙuduri ne taro mai girma suka yi?

10 Tun da yake mu ajizai ne, yana iya zame mana ƙalubale mu nuna halaye na ruhaniya, mu guje wa ayyuka na jiki, kuma mu ƙi matsi na wannan duniyar Shaiɗan. Duk da haka, mun ƙudurta cewa ba za mu ƙyale sanyin gwiwar da muka yi domin kasawarmu, ɗan kurakuran da muka yi, ko kuwa naƙasan da muke da shi ya shafi bangaskiyarmu ko kuwa ya rage ƙaunar da muke yi wa Jehobah ba. Mun san cewa Jehobah zai cika alkawarin da ya yi, wato, zai kāre taro mai girma a lokacin babban tsanani.

11. Waɗanne dabaru ne Shaiɗan yake amfani da su don ya raunana bangaskiyar Kiristoci?

11 Duk da haka, muna mai da hankali a kowane lokaci domin mun san cewa Iblis ne maƙiyinmu na ainihi, kuma ba ya gajiya da wuri. (Ka karanta 1 Bitrus 5:8.) Ya yi ƙoƙarin yin amfani da ’yan ridda da sauransu don ya ruɗe mu mu yarda cewa koyarwar da muke bi ba gaskiya ba ce. Amma wannan dabarar ba ta yi aiki ba. Hakazalika, ko da yake a wasu lokatai tsanantawa tana rage aikin wa’azi, amma a yawancin lokaci hakan na ƙarfafa bangaskiyar waɗanda ake tsanantawa. Saboda haka, Shaiɗan yana yawan amfani da dabarun da yake ganin cewa za su ba shi dama mai kyau na raunana bangaskiyarmu. Yana amfani da sanyin gwiwa. An yi wa Kiristoci na ƙarni na farko gargaɗi game da wannan haɗarin sa’ad da aka ce masu: “Ku lura da shi [Kristi] wanda ya jimre da wannan irin jayayyar mutane masu-zunubi a kansa.” Me ya sa? “Domin kada ku gaji, ku yi suwu cikin rayukanku.”—Ibran. 12:3.

12. Ta yaya ne shawarar Littafi Mai Tsarki take ƙarfafa waɗanda suka yi sanyin gwiwa?

12 Ka taɓa jin kamar ka daina bauta wa Jehobah? A wasu lokatai kana jin cewa ka kasa? Idan haka ne, kada ka ƙyale Shaiɗan ya yi amfani da yadda ka ke ji ya hana ka bauta wa Jehobah. Yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, addu’a, halartar taro da kuma yin tarayya da ’yan’uwa Kiristoci a kai a kai zai ƙarfafa ka kuma ya hana ka ‘yin suwu cikin rayuwarka.’ Jehobah ya yi alkawarin taimaka wa waɗanda suke bauta masa su sami ƙarfi, kuma mun san zai cika alkawarinsa. (Ka karanta Ishaya 40:30, 31.) Ka mai da hankali ga hidimar Mulki. Ka guje wa abubuwan da za su cinye lokacinka kuma ka mai da hankali ga taimaka wa wasu. Da haka, za ka sami ƙarfin jimrewa duk da sanyin gwiwa.—Gal. 6:1, 2.

Ceto Daga Cikin Tsanani Zuwa Sabuwar Duniya

13. Wane aiki ne ke gaban waɗanda suka tsira a Armageddon?

13 Bayan Armageddon, marasa aminci masu yawa da za a ta da daga matattu za su bukaci a koya masu umurnin Jehobah. (A. M. 24:15) Suna bukatar a koyar da su game da hadayar fansa ta Yesu, dole ne a koyar da su yadda za su yi imani da wannan hadayar don su sami amfaninta. Suna bukatar su ƙi ra’ayoyi na addinan ƙarya da suke da shi a dā, kuma suna bukatar su ƙi hanyar rayuwarsu ta dā. Dole ne su koyi yadda za su kasance da sabon hali da ke bayyana Kiristoci na gaskiya. (Afis. 4:22-24; Kol. 3:9, 10) Wasu tumakin da suka tsira a wannan lokacin suna da aiki mai yawa da za su yi. Abin farin ciki ne a yi irin wannan hidimar ga Jehobah, inda babu matsi da abubuwan da ke ɗauke hankali a wannan muguwar duniyar!

14, 15. Ka kwatanta hirar da za ta kasance tsakanin waɗanda suka tsira daga babban tsanani da kuma amintattun da aka ta da daga matattu.

14 Bayin Jehobah masu aminci da suka mutu kafin hidimar Yesu a duniya su ma suna da abubuwa masu yawa da za su koya a wannan lokacin. Za su san kowanene Almasihun da aka yi alkawarinsa wanda suka yi ɗokin gani amma hakan bai yiwu ba. A rayuwarsu ta dā sun nuna suna son Jehobah ya koyar da su. Ka yi tunanin irin farin ciki da gatan da za a samu na taimaka masu, alal misali, mu bayyana wa Daniel cikar annabce-annabcen da ya rubuta amma bai fahimce su ba!—Dan. 12:8, 9.

15 Babu shakka, duk da cewa waɗanda aka ta da daga matattu suna da abubuwa masu yawa da za su koya a wurinmu, mu ma muna da tambayoyi masu yawa da za mu yi masu. Za su iya gaya mana abubuwan da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki da ba a bayyana su dalla-dalla ba. Zai zama abin ban sha’awa mu ji labarai game da Yesu daga wurin ɗan ƙanwar mamarsa, Yohanna Mai Yin Baftisma! Abubuwan da muka koya daga waɗannan shaidu masu aminci babu shakka zai sa mu fahimci Kalmar Allah fiye da yanzu. Bayin Jehobah masu aminci da suka mutu, har da wasu cikin taro mai girma da suka mutu a wannan lokaci na ƙarshe, za su sami “tashi mafi kyau.” Sun soma hidimarsu ga Jehobah a duniyar da Shaiɗan ke sarauta. Za su sami farin cikin ci gaba da yin hidimarsu a yanayi mafi kyau a sabuwar duniya.—Ibran. 11:35; 1 Yoh. 5:19.

16. In ji annabci, ta yaya Ranar Hukunci za ta soma?

16 A Ranar Hukunci, za a buɗe naɗaɗɗun littattafai. Za a haɗa su da Littafi Mai Tsarki don a yi wa waɗanda suka rayu hukunci game da cancantarsu na samun rai na har abada. (Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 20:12, 13.) A ƙarshen Ranar Hukunci, kowane mutum ya riga ya samu dama mai yawa na nuna matsayinsa a batun ikon mallaka. Zai miƙa kai ne ga tsarin Mulki kuma ya ƙyale Ɗan Rago ya yi masa ja-gora zuwa “maɓulɓulan ruwaye na rai”? Ko kuwa zai ƙi miƙa kansa ga Mulkin Allah? (R. Yoh. 7:17; Isha. 65:20) A wannan lokacin, dukan waɗanda suke duniya sun riga sun sami damar yanke shawara, ba tare da zunubin da muka gada ko kuwa mahalli marar kyau ba. Babu wanda zai iya tuhumar hukunci na ƙarshe da Jehobah zai yi. Mugaye kaɗai ne kawai za a halaka har abada.—R. Yoh. 20:14, 15.

17, 18. Wane irin ɗoki da ke cike da farin ciki ne shafaffun Kiristoci da wasu tumaki suke yi game da Ranar Hukunci?

17 Da yake shafaffun Kiristoci a yau sun riga sun cancanci samun Mulki, suna ɗokin yin sarauta a Ranar Hukunci. Wannan gata ne mai girma a gare su! Wannan begen ya motsa su su bi shawarar da Bitrus ya ba ’yan’uwansu na ƙarni na farko: “Ku daɗa bada anniya garin ku tabbatadda kiranku da zaɓenku: gama idan kun yi waɗannan abu, ba za ku yi tuntuɓe ba daɗai: gama hakanan za a ba ku shigowa mai-yalwa zuwa cikin madawamin mulki na Ubangijinmu da Mai-cetonmu Yesu Kristi.”—2 Bit. 1:10, 11.

18 Wasu tumaki suna yi wa ’yan’uwansu shafaffu farin ciki. Sun ƙudurta tallafa masu. Domin su abokan Allah ne a yau, suna iya ƙoƙarinsu a hidimar Allah. A Ranar Hukunci, za su yi farin cikin tallafa wa tsarin Allah da dukan zuciyarsu yayin da Yesu yake yi masu ja-gora zuwa maɓulɓular ruwaye na rai. A ƙarshe, za su cancanci zama bayin Jehobah na duniya har abada.—Rom. 8:20, 21; R. Yoh. 21:1-7.

Ka Tuna?

• Menene mallakar Yesu ya ƙunsa?

• Ta yaya ne taro mai girma suke tallafa wa ’yan’uwansu shafaffu?

• Waɗanne gata da bege ne taro mai girma suke morewa?

• Menene ra’ayinka game da Ranar Hukunci?

[Hoto a shafi na 25]

Taro mai girma sun wanke rigunansu kuma sun faranta su cikin jinin Ɗan rago

[Hoto a shafi na 27]

Menene za ka so ka koya daga amintattun da aka ta da daga matattu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba