Babi Na Goma Sha Uku
Taro Mai Girma a Gaban Kursiyin Jehovah
1. (a) Menene dole bayin Allah kafin lokatan Kirista ko kuma 144,000 za su ɗanɗana kafin su samu ladarsu? (b) Menene zai yiwu ga “taro mai-girma” da suke rayuwa a wannan lokaci?
BAYIN Allah masu aminci daga Habila zuwa Yohanna Mai Yin Baftisma sun saka yin nufin Allah farko a rayuwarsu. Duk da haka, duka sun mutu, suna jirar tashi daga matattu zuwa rai a duniya cikin sabuwar duniya ta Allah. Waɗanda za su yi sarauta da Kristi cikin Mulki na samaniya, 144,000, su ma dole su mutu kafin su samu ladarsu. Amma, Ru’ya ta Yohanna 7:9 ta nuna cewa a cikin waɗannan kwanaki na ƙarshe, da akwai “taro mai-girma” daga dukan al’ummai da ba za su ɗanɗana mutuwa ba amma za su kasance da begen rayuwa har abada a duniya. Kana cikinsu ne?
Gano Taro Mai Girman
2. Menene ya kai ga fahimi mai kyau game da taro mai girma na Ru’ya ta Yohanna 7:9?
2 A shekara ta 1923, bayin Jehovah sun gano cewa “tumaki” na almarar Yesu da ke a Matta 25:31-46 da “waɗansu tumaki” da ya ambata a Yohanna 10:16, mutane ne da za su sami gatar rayuwa har abada a duniya. A shekara ta 1931 waɗanda aka yi wa alama a goshi a Ezekiel 9:1-11 aka fahimci cewa waɗanda suke da bege na zama a duniya ne su ma. Sai kuma a shekara ta 1935 an gano cewa taro mai girma tana ɓangare ne na ajin waɗansu tumaki da Yesu ya yi zancensu. A yau, wannan taro mai girma sun kai miliyoyi.
3. Me ya sa furcin nan “tsaye gaban kursiyin” ba ya nufin aji na samaniya?
3 A Ru’ya ta Yohanna 7:9, ba a sama aka ga taro mai girman ba. Cewa suna “tsaye gaban kursiyin” Allah bai bukaci kasancewarsu cikin sama ba. Su dai Allah yana ganinsu ne. (Zabura 11:4) Gaskiyar cewa taro mai girma, “wanda ba mai-ƙirgawa,” ba aji na sama ba ne ya bayyana ta wajen gwada da adadinsa marar iyaka da abin da ke rubuce a Ru’ya ta Yohanna 7:4-8 da kuma Ru’ya ta Yohanna 14:1-4. Inda aka nuna cewa adadin da aka ɗauka daga duniya zuwa sama, 144,000 ne.
4. (a) Menene ne “babban tsananin” da taro mai girma za su tsira daga ciki? (b) Yadda aka rubuta a Ru’ya ta Yohanna 7:11, 12, wa ke lura da taro mai girma kuma suna sujjada tare da su?
4 Ru’ya ta Yohanna 7:14 ta ce game da taro mai girma: “Su ne waɗanda suka fito daga cikin babban tsananin.” Sun tsira wa bala’i mafi girma cikin tarihin mutane. (Matta 24:21) Yayin da suke godiya ga Allah da kuma ga Kristi domin ceto, sai dukan halittu cikin sama su haɗu da su wajen faɗin: “Amin: Albarka, da ɗaukaka, da hikima, da godiya, da daraja, da iko, da ƙarfi, ga Allahnmu har zuwa zamanun zamanai. Amin.”—Ru’ya ta Yohanna 7:11, 12.
Za Su Tabbatar Sun Cancanci Tsira
5. Yaya za mu san abin da ake bukata domin a kasance cikin sashen taro mai girma?
5 Yadda za a kāre taro mai girma cikin babban tsananin da zai auku ya jitu da mizanan adalci na Jehovah. An tattauna dalla-dalla halayen da za a san waɗanda za a cece su da shi a cikin Littafi Mai Tsarki. Domin haka, yana yiwuwa ga waɗanda suke son adalci su aikata yanzu domin su nuna cewa sun cancanci su tsira. Menene dole waɗannan za su yi?
6. Me ya sa za a iya kwatanta taro mai girma daidai da tumaki?
6 Tumaki suna da taushi kuma suna biyayya. Saboda haka, lokacin da Yesu ya ce yana da waɗansu tumaki da ba sa cikin aji na sama, yana nufin mutane da ba kawai suna son su zauna har abada ba a duniya amma da za su bi koyarwarsa ne. “Tumakina suna jin muryata, na kuwa san su, suna biyona kuma,” in ji shi. (Yohanna 10:16, 27) Waɗannan ne mutane da suka saurari kuma cikin biyayya suka yi abin da Yesu ya ce, suna zama almajiransa.
7. Waɗanne halaye mabiyan Yesu ke bukatar su koya?
7 Waɗanne halaye kuma kowanne cikin waɗannan mabiyan Yesu ke bukatar su koya? Kalmar Allah ta amsa: “Ku tuɓe, ga zancen irin zamanku na dā, tsohon mutum . . . ku yafa sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya.” (Afisawa 4:22-24) Suna koyon halaye da ke daɗa ga haɗin kan bayin Allah—“ƙauna . . . , farinciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa.”—Galatiyawa 5:22, 23.
8. Menene taro mai girma za su fuskanta yayin da suke goyon bayan raguwar?
8 Babban garke suna tallafa wa adadi ɗan kaɗan na waɗanda suke da bege na samaniya, da suke ja-gorar aikin wa’azin. (Matta 24:14; 25:40) Waɗansu tumaki suna ba da wannan goyon bayan ko da yake sun sani cewa za su sadu da hamayya domin a farawar wannan kwanaki na ƙarshe, Kristi Yesu da mala’ikunsa sun jefo da Shaiɗan da aljanunsa daga sama. Wannan yana nufin “kaiton duniya . . . domin Shaiɗan ya sauko wajenku, hasala mai-girma kuwa gareshi, domin ya sani sauran zarafinsa kaɗan ne.” (Ru’ya ta Yohanna 12:7-12) Domin haka, Shaiɗan ya ƙarfafa hamayyarsa a kan bayin Allah da yake ƙarshen wannan zamanin ya yi kusa.
9. Yaya nasarar bayin Allah take a yin wa’azin bisharar, kuma me ya sa?
9 Duk da mugun tsanani, aikin wa’azi yana ci gaba da bunƙasa. Daga dubbai kalilan na masu wa’azin Mulki a ƙarshen Yaƙin Duniya na I, yanzu da akwai miliyoyi, domin Jehovah ya yi alkawarin: “Babu alatun da aka halitta domin ciwutanki da za ya yi albarka.” (Ishaya 54:17) Har ma wani da ke cikin majalisa ta Yahudawa ya fahimci cewa ba za a ci nasara kan aikin Allah ba. Ya gaya wa Farisawa a ƙarni na farko game da almajiran: “Ku ƙyale su: gama idan wannan shawara ko wannan aiki na mutane ne, za ya rushe: amma idan na Allah ne, ba za ku iya rushe su ba, kada a iske ku kuna yaƙi har da Allah.”—Ayukan Manzanni 5:38, 39.
10. (a) Mecece “shaida” a goshin waɗanda ke na taro mai girma ke nufi? (b) Ta yaya bayin Allah suke biyayya ga “murya daga sama”?
10 An nuna taro mai girma cewa an saka musu shaidar tsira. (Ezekiel 9:4-6) ‘Shaidar’ tabbaci ne cewa sun keɓe kai ga Jehovah, almajiran Yesu da suka yi baftisma, kuma suna fama don su koyi mutuntaka irinta Kristi. Suna biyayya ga “murya daga sama” da ta ce game da daular addinan ƙarya ta dukan duniya ta Shaiɗan: “Ku fito daga cikinta, ya al’ummata, domin kada ku yi tarayya da zunubanta, kada ku sha rabon annobanta.”—Ru’ya ta Yohanna 18:1-5.
11. A wace muhimmiyar hanya ce waɗanda ke na taro mai girma suke nuna cewa su bayin Jehovah ne?
11 Sai kuma Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yohanna 13:35) Akasin wannan, waɗanda suke cikin addini ɗaya suna kashe ’yan’uwansu a yaƙi, sau da yawa domin kawai sun fito daga al’ummai dabam dabam! Kalmar Allah ta ce: “Inda ’ya’yan Allah sun bayyanu ke nan, da ’ya’yan Shaiɗan: dukan wanda ba shi aika adalci ba, ba na Allah ba ne, da wannan kuma wanda ba ya yi ƙaunar ɗan’uwansa ba. . . . Mu yi ƙaunar junanmu: ba kamar Kayinu wanda shi ke na Shaiɗan, ya kashe ɗan’uwansa.”—1 Yohanna 3:10-12.
12. A babban tsananin, yaya Jehovah zai bi da dukan ‘itatuwa’ na addinai da ke ba da ɓātattun ’ya’ya?
12 Yesu ya ce: “Kowane itacen kirki ya kan fitarda ’ya’yan kirki; amma ɓātacen itace ya kan fitarda munanan ’ya’ya. Itacen kirki ba ya iya fito da munanan ’ya’ya ba, ɓātacen itace kuma ba ya iya fito da ’ya’yan kirki ba. Kowane itacen da ba ya fito da ’ya’yan kirki ba a kan sare shi, a jefa a wuta. Bisa ga ’ya’yansu fa za ku sansance su.” (Matta 7:17-20) ’Ya’yan da addinan wannan duniyar suke bayarwa sun sansance su ɓātattun ‘itatuwa,’ ne da ba da daɗewa ba Jehovah zai halaka su a babban tsananin.—Ru’ya ta Yohanna 17:16.
13. Yaya ne taro mai girma suka nuna cewa cikin haɗin kai suna “tsaye gaban kursiyi” na Jehovah?
13 Ru’ya ta Yohanna 7:9-15 sun jawo hankali zuwa ga abubuwa da ke kai ga ceton taro mai girma. An nuna su cikin haɗin kai a “tsaye gaban kursiyi” na Jehovah, suna ɗaukaka ikon mallakarsa na dukan sararin halitta. Sun “wanke rigunansu, suka faranta su cikin jinin Ɗan ragon,” suna nuna sun fahimci hadayar Yesu na kafarar zunubi. (Yohanna 1:29) Sun keɓe kansu ga Allah kuma sun nuna haka ta wajen wankan nitsarwa a ruwa. Da haka suna more tsayawa mai tsarki a gaban Allah, da fararen tufafi ke alamta, suna yi masa “bauta kuma dare da rana.” Akwai hanyoyi ne da za ka kawo rayuwarka daidai cikin jituwa da abin da aka kwatanta a nan?
Fa’idodi da ke a Yanzu
14. Menene wasu fa’idodi da ke zuwa ga bayin Jehovah a yanzu ma?
14 Wataƙila ka lura da fa’idodi na musamman da waɗanda suke bauta wa Jehovah suke samu a yanzu. Alal misali, sa’ad da ka koya game da nufe-nufen Jehovah na adalci, ka fahimci cewa da akwai bege mai kyau a nan gaba. Saboda haka, yanzu kana da ma’anar rayuwa—ka bauta wa Allah na gaskiya da bege mai kyau na rai madawwami a duniya ta aljanna. Hakika, Sarki Yesu Kristi “za ya bishe [taro mai girma] kuma ta wurin maɓulɓulan ruwaye na rai.”—Ru’ya ta Yohanna 7:17.
15. Ta yaya Shaidun Jehovah suke amfana daga bin mizanan Littafi Mai Tsarki game da siyasa da kuma al’amura na ɗabi’a?
15 Fa’ida ta ban sha’awa da taro mai girma suke morewa ita ce ƙauna, haɗin kai, da kuma jituwa da ya kasance a tsakanin bayin Jehovah a dukan duniya. Da yake dukanmu na ci daga abinci ɗaya na ruhaniya, mu duka muna biyayya ga dokoki ɗaya ne da kuma mizanai na cikin Kalmar Allah. Abin da ya sa ke nan siyasa da ra’ayoyi na ƙasashe ba sa raba mu. Kuma, muna riƙe mizanan ɗabi’a da Allah ke bukata daga wurin mutanensa. (1 Korinthiyawa 6:9-11) Domin haka, maimakon kasancewa da tarna, jayayya, da kuma lalata da ke ko’ina cikin wannan duniyar, mutanen Jehovah suna more abin da ake kira aljanna ta ruhaniya. Ka lura da yadda aka kwatanta wannan a Ishaya 65:13, 14.
16. Duk da matsaloli da ake fuskanta a rayuwa, taro mai girma wane bege suke da shi?
16 A’a, mutanen da ke bayin Jehovah, ba kamilai ba ne. Wahalar rayuwar duniya tana shafan su, kamar su shan wuya ko kuma wahalar yaƙi na ƙasashe. Suna kuma fuskantar ciwo, wahala, da kuma mutuwa. Amma suna da bangaskiya cewa a cikin sabuwar duniya, Allah zai “share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙinzuciya, ko kuka, ko azaba.”—Ru’ya ta Yohanna 21:4.
17. Ko da me zai faru da mu a yanzu, wane irin abu ke jiran waɗanda suke bauta wa Allah na gaskiya?
17 Ko idan ka yi rashin ranka yanzu saboda tsufa, ciwo, hatsari, ko kuma tsanani, Jehovah zai tashe ka zuwa rai a cikin Aljanna. (Ayukan Manzanni 24:15) Sai ka ci gaba da more biki na ruhaniya cikin Sarautar Alif ta Kristi. Ƙaunarka ga Allah za ta ƙaru yayin da ka ga nufe-nufensa suna cika. Albarka ta jiki da Jehovah zai tanadar za ta ƙara ƙaunarka a gare shi kuma. (Ishaya 25:6-9) Lallai a nan gaba mutanen Allah za su samu abubuwa da yawa da ke jiransu!
Maimaita Abin da Aka Tattauna
• Da wace aukuwa ta musamman Littafi Mai Tsarki ya haɗa taro mai girma?
• Idan muna so mu kasance da gaske tsakanin taro mai girma da Allah yake sonsu, menene dole ne mu yi a yanzu?
• Yaya albarkar da taro mai girma suke morewa a yanzu da wadda za su mora a sabuwar duniya ta Allah ke da muhimmanci a gare ka?
[Hoto a shafi na 123]
Miliyoyin taro mai girma suna haɗa kai wajen bauta wa Allah na gaskiya