DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 14-15
Ya Ciyar da Dubbai Ta Hannun Mutane Ƙalila
Kafin a yi Idin Ƙetarewa a shekara ta 32 bayan haihuwar Yesu, Yesu ya yi wata mu’ujiza wadda an rubuta a littafin Matta da Markus da Luka da kuma Yohanna.
Ta wannan mu’ujizar, Yesu ya yi wani abu da har yanzu yana yi.
Ko da yake burodi biyar da kifi biyu ne kawai mabiyan Yesu suke da su, Yesu ya umurce su su ciyar da dubban mutane
Yesu ya ɗauki burodin da kifin, ya yi addu’a kuma ya rarraba wa mabiyansa. Mabiyansa kuma suka ba wa mutanen
Mutanen sun ci sun ƙoshi har abincin ya rage. Yesu ya ciyar da dubban mutane ta wurin mutane kaɗan, wato mabiyansa
Yesu ya ce a kwanaki na ƙarshe, zai naɗa wasu da za su riƙa ba da ‘abinci a lotonsa.’—Mt 24:45
A shekara ta 1919, Yesu ya naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” wato wani ƙaramin rukunin Kiristoci shafaffu da za su ja-goranci “iyalin gidansa,” wato waɗanda za su ci abincin
Ta wajen wannan ƙaramin rukunin shafaffu, Yesu yana ciyar da mutane kamar yadda ya yi a ƙarni na farko
Ta yaya zan nuna cewa na sani kuma ina daraja hanyar da Yesu yake amfani da ita wajen taimaka mana mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah?