DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MARKUS 9-10
Wahayi da Ke Ƙarfafa Bangaskiya
Ka yi tunanin yadda Yesu ya ji sa’ad da Ubansa na sama ya gaya ma wasu almajiransa cewa yana ƙaunarsa a lokacin da ya canja kamanni. Hakan ya ƙarfafa Yesu don ya iya jimre wahalar da zai sha ba da daɗewa ba. Ban da haka ma, wahayin ya sa Bitrus da Yaƙub da kuma Yohanna sun ƙara gaskata cewa Yesu ne almasihun da aka yi alkawarinsa kuma ya dace da suka saurare shi. Bayan shekaru 32, Bitrus ya faɗi yadda wannan lamarin ya sa ya ƙara gaskata da “annabci” da ke Littafi Mai Tsarki.—2Bi 1:16-19.
Ko da yake mu ba mu ga wahayin nan ba, amma muna shaida cikarsa. Yesu Sarki ne mai iko da yake sarauta a sama. Nan ba da daɗewa ba, zai gama “cin nasara” kuma hakan zai sa mu yi rayuwa a sabuwar duniya.—R. Yoh 6:2.
Ta yaya ganin cikar annabcin Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa bangaskiyarka?