Rayuwa Cikin Sabuwar Duniya ta Salama
Yayin da ka duba yanayi da yake wannan warƙa, yaya ka ke ji? Zuciyarka ba ta yi sha’awar salama, farin ciki, da ni’ima da ake gani a nan ba? Lallai tana yin haka. Amma mafarki ne kawai, ko kuwa ƙage a gaskata cewa waɗannan yanayi za su kasance a duniya?
Ƙila yawancin mutane suna tunani haka. Abubuwa da ake gani yau su ne yaƙi, yin laifi, yunwa, ciwo, tsufa—a ambata kaɗan kawai cikinsu. Duk da haka, akwai dalilin bege. Littafi Mai-Tsarki ya yi magana cewa a nan gaba, “bisa ga alkawarin [Allah], muna sauraron sababbin sammai da sabuwar duniya, inda adalci ya ke zaune.”—2 Bitrus 3:13; Ishaya 65:17.
Waɗannan “sababbin sammai” da “sabuwar duniya,” in ji Littafi Mai-Tsarki, ba sababbin sammai ko sabuwar duniya ta zahiri ba ce. Duniya da sammai na zahiri an yi su cikakku, kuma Littafi Mai-Tsarki ya nuna cewa za su kasance har abada. (Zabura 89:36, 37; 104:5) “Sabuwar duniya” za ta zama jam’iyyar mutane masu adalci da za su zauna a duniya, “sababbin sammai” kuma za su zama cikakken mulkin sama, ko gwamnati, da za ta yi sarauta bisa wannan jam’iyyar mutane na duniya. Amma da wani ma’ana a gaskata cewa “sabuwar duniya,” ko kuwa sabuwar duniya mai ɗaukaka, tana yiwuwa?
To, ka yi la’akari da gaskiyar cewa irin waɗannan yanayi masu kyau bangare ne na nufin Allah na asali domin wannan duniya. Ya sa mutane biyu na farko cikin Aljanna ta duniya a Adnin kuma ya ba su aiki mai ban al’ajabi: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya, ku mallake ta.” (Farawa 1:28) I, nufin Allah ne a garesu su haifi ’ya’ya kuma daga baya su faɗaɗa Aljannarsu a dukan duniya. Ko da yake daga baya sun zaɓi su yi wa Allah rashin biyayya, da haka sun nuna ba su dace ba don rayuwa na har abada, nufin Allah na asali bai canja ba. Kuma dole zai cika a sabuwar duniya!—Ishaya 55:11.
Gaskiya, lokacin da ka ke yin Addu’ar Ubangiji, ko kuwa na Ubanmu, kana roƙo, Mulkin Allah ya zo, kana addu’a domin gwamnatinsa ta sama ta kawar da mugunta daga duniya kuma ta yi mulki bisa wannan sabuwar duniya. (Matta 6:9, 10) Za mu kasance da gaba gaɗi cewa Allah zai amsa wannan addu’a, tun da ya ke Kalmarsa ta yi alkawari cewa: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zabura 37:29.
Rayuwa a Cikin Sabuwar Duniya ta Allah
Mulkin Allah zai kawo albarka da suka wuce a kimanta wa duniya, zai cika kowane abubuwa masu kyau da Allah ya ƙudura mutanensa za su more a duniya tun farko. Ƙiyayya da ƙabilanci ba za su kasance ba, daga baya kuma kowa a duniya zai zama aboki na gaskiya. A cikin Littafi Mai-Tsarki, Allah ya yi alkawari cewa zai ‘sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya.’ “Al’umma ba za ta zāre ma al’umma takobi ba, ba kuwa za a ƙara koya yaƙi nan gaba ba.”—Zabura 46:9; Ishaya 2:4.
Daga baya za a mai da dukan duniya zuwa lambu na aljanna. Littafi Mai-Tsarki ya ce: “Jeji da ƙeƙasashiyar ƙasa za su yi farin ciki, hamada kuma za ta yi murna, ta yi fure kamar rose. . . . Gama a cikin jeji ruwaye za su ɓullo, rafufuka kuma a cikin hamada. Jigawa mai-ƙuna za ya zama tabki, ƙasa mai-ƙishi kuma za ta zama maɓulɓulan ruwaye.”—Ishaya 35:1, 6, 7.
Da dalilin murna a cikin Aljanna a duniya. Mutane ba za su ji yunwa domin rashin abinci kuma ba. “Ƙasa tā bada amfaninta,” in ji Littafi Mai-Tsarki. (Zabura 67:6; 72:16) Dukan mutane za su more amfanin aikinsu, yadda Mahaliccinmu ya yi alkawari: “Za su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu . . . ba za su dasa, wani ya ci ba.”—Ishaya 65:21, 22.
Cikin sabuwar duniya ta Allah, ba za a ƙara sa mutane su cunkushe cikin manyan gidaje ko kuwa ƙasƙantattun sassa na matalauta ba, domin Allah ya kuɗura cewa: “Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki . . . Ba za su yi gini, wani ya zauna ba.” Littafi Mai-Tsarki ya yi alkawari kuma cewa: “Ba za su yi aiki a banza ba.” (Ishaya 65:21-23) Da haka, mutane za su sami aiki mai amfani, mai gamsarwa. Ba za a gaji da rayuwa ba.
Da sannu sannu, Mulkin Allah zai sake mai da dangantaka ta salama da ta kasance cikin lambun Adnin tsakanin dabbobi, da kuma tsakanin dabbobi da mutane. Littafi Mai-Tsarki ya ce: “Kerkeci za ya zauna tare da ɗan rago, damisa kuma za ta kwanta tare da ɗan akuya; da ɗan maraƙi da ɗan zaki da kiyayyen ɗan sā za su zauna wuri ɗaya, ɗan yaro kuwa za ya bishe su.”—Ishaya 11:6-9; Hosea 2:18.
Ka yi tunani, cikin Aljanna ta duniya za a warkar da dukan cututtuka da kumammanci na zahiri! Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa: “Wanda yake zaune a ciki ba za ya ce, ina ciwo ba.” (Ishaya 33:24) “[Allah] za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu, mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙinzuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”—Ru’ya ta Yohanna 21:4.
Yadda Zai Kasance a Gareka
Lallai dole zuciyarka ta motsa game da alkawuran Allah na rayuwa cikin sabuwar duniyarsa ta adalci. Kuma yayin da waɗansu mutane sun ɗauka cikar waɗannan albarka cewa kyaunsu ya wuci ya zama gaskiya, kyaunsu bai wuci su zo daga hannun ƙaunataccen Mahaliccinmu ba.—Zabura 145:16; Mikah 4:4.
Babu shakka, akwai bukatu da za a biya idan za mu rayu har abada cikin Aljanna mai zuwa bisa duniya. Yesu ya nuna na musamman a cikinsu, ya faɗi a cikin addu’a ga Allah: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.”—Yohanna 17:3.
Saboda haka idan da gaske muna son mu rayu cikin sabuwar duniya ta Allah, dole ne da farko mu koyi nufin Allah sa’annan kuma mu yi shi. Gama gaskiya ne: Wannan “duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada,” ya more albarka da Mahaliccinmu mai ƙauna zai zuɓo har abada.—1 Yohanna 2:17.
Sai dai ko an nuna alama, dukan ayoyin da aka yi amfani da su daga Litafi Mai-Tsarki ne kuma an yi amfani da harufan zamani.