Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • dg kashi 10 pp. 22-28
  • Sashe na 10—Sabuwar Duniya Mai-Ban Al’Ajibi Yin Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sashe na 10—Sabuwar Duniya Mai-Ban Al’Ajibi Yin Allah
  • Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Adilci ya Ɗauki Matsayin Mugunta
  • An Mayas da Kamiltacciyar Lafiya
  • Matattu Sun Komo
  • Duniya ta Salama na Gaskiya
  • Duniya da Aka Juya Zuwa Aljanna
  • Kawas da Abin Ɗā
  • Rayuwa Cikin Sabuwar Duniya ta Salama
    Rayuwa Cikin Sabuwar Duniya ta Salama
  • Abin Da Mulkin Allah Zai Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Annabcin Rayuwarmu Ta Nan Gaba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
dg kashi 10 pp. 22-28

Sashe na 10—Sabuwar Duniya Mai-Ban Al’Ajibi Yin Allah

1, 2. Minene zai faru bayan yaƙin Armageddon mai-tsabtatawa?

BAYAN yaƙin Allah mai-tsabtatawar nan Armageddon, minene zai faru kuma? Sai sabuwar tsara mai-girma zata soma. Waɗanda suka tsira ma Armageddon ɗin, za a shigar da su cikin sabuwar duniya, da shike sun tabbatas da imaninsu ko ga sarautar Allah. Duba sabuwar tsara na kwashe hankali a tarihi da zai zama fa yayinda albarkatai masu-ban al’ajibi suka gudana daga wurin Allah zuwa ga iyalin yan-Adam!

2 Ƙalƙashin jagabancin Mulkin Allah fa, waɗanda suka tsirar zasu soma gina wata aljanna. Ƙarfinsu zasu bada shi duka ga aiki da zai amfane kowa da ke da rai a lokacin. Za a soma sabonta duniyar cikin gidan mutane mai-kyau, mai-salama, mai-ƙoshed wa kuma.

Adilci ya Ɗauki Matsayin Mugunta

3. Wane sauƙaƙawa na nan da nan ne za a shaida bada daɗewa ba bayan Armageddon?

3 Dukan wannan yana yiwuwa ta wurin hallakas da duniyar Shaitan. Ba za a ƙara ganin addinan ƙarya, shirye-shiryen zaman jama’a, ko kuwa gwamnatoci da suke raɓuwa kuma ba. Babu shela irin ta shaitan da zai ruɗas da mutane kuma; dukan waɗanda suke haifad da su zasu hallaku sarai tare da shirin Shaitan. Ka dai ga: an kawas da dukan gurɓaɓɓiyar yanayin duniyar Shaitan ko sarai! Ga fa hutawa da haka zai zama!

4. Ka kwatanta canjin koyo da zai auku.

4 Sa’annan za a sāke ra’ayoyin sarautar yan-Adam mai hallakaswa da koyaswa mai-ginawa da ke zuwa daga wurin Allah. “Dukan ’ya’yanki kuma zasu zama masukoyi na Jehovah.” (Ishaya 54:13) Da koyaswa mai-tsarkin nan shekara shekara fa, “duniya zata cika da sanin Jehovah, kamar yadda ruwaye suke rufe teku.” (Ishaya 11:⁠9) Gama mutane ba zasu ƙara koya mugunta kuma ba, amma “mazaunan duniya sukan koyi adilci.” (Ishaya 26:⁠9) Tunani da ayuka masu ginawa sune zasu zama halayen mutane duka.​—⁠Ayukan Manzanni 17:31; Filibbiyawa 4:⁠8.

5. Minene zai faru ga dukan mugunta da miyagun mutane?

5 Saboda haka, ba za a ƙara yin kisan kai, nuna ƙarfi, fyaɗe, kwace, ko kuwa wani irin aika laifi kuma. Babu wani da zai sāke shan wahala domin mugun ayukan wasu. Misalai 10:30 ya ce: “Ba za a kawas da masu-adilci ba daɗai; amma miyagu ba zasu zama cikin ƙasan ba.”

An Mayas da Kamiltacciyar Lafiya

6, 7. (a) Wane hasali ne sarautar Mulkin zai kawas da shi? (b) Ina yadda Yesu ya nuna wannan yayinda yake bisa duniya?

6 A cikin sabuwar duniyar, za a kawas da dukan abubuwa da tawaye na farkon ya kawo. Alal misali, sarautar Mulkin zai kawas da ciwo da tsofewa. Ayau fa, ko idan kana moran misalin lafiyar jiki mai-kyau, al’amarin gaskiya shine cewa yayinda ka ke tsofewa, idanunka sukan ɗankare, haƙoranka sukan ruɓe, jin gari naka takan rage, fatan jikinka yakan tamoje, ƙwayoyin jikinka na ciki suka kakarye, har kuma ka mutu.

7 Amma dai, bada jimawa ba waɗannan abubuwa masu wahalaswa da muka gāda daga wurin iyayenmu na fari su a zama abin dā. Ka tuna kuwa da abinda Yesu ya nuna game da lafiyar jiki yayinda yake duniya? Littafi Mai-tsarki ya bayana haka: “Sai taro masu-yawa suka zo wurinsa, suna tare da guragu, da makafi, da bebaye, da masu-dungu, da waɗansu kuma dayawa, suka zuba su wajen ƙafafunsa; ya kuwa warkadda su; har taro suka yi mamaki, da suka ga bebaye suna magana, masu dungu suka yi sarai, guragu suna tafiya, makafi suna gani.”​—⁠Matta 15:30, 31.

8, 9. Ka kwatanta farinciki da zai zo cikin sabuwar duniya yayinda aka mayas da kamiltacciyar lafiyar.

8 Dubi farinciki mai-girma fa da zai zo cikin sabuwar duniyar yayinda an kawas da dukan ciwonmu! Wahala daga rashin lafiya ba zai sāke wulakantar da mu kuma ba. “Wanda yake zaune a ciki ba zaya ce, Ina ciwo ba.” “Sa’annan za a buɗe idanun makafi, kunnuwan kurame kuma za a buɗe. Sa’annan gurgu zaya yi ta tsalle kamar barewa, harshen bebe kuma zaya raira waƙa.”​—⁠Ishaya 33:24; 35:⁠5, 6.

9 Ashe ba zai zama abin murna ba ne ka tashi kowace safiya kuma ga cewa kana moran lafiyayyen rai? Ashe ba zai zama dalilin farinciki ba ne ga tsofaffi su ga cewa an komo da su ko zuwa ƙarfin ƙuruciya kuma zasu samu kamiltawa da Adamu da Hawa’u a farko suka mora? Alkawalin Littafi Mai-tsarki ke nan: “Namansa zaya komo ya fi na yaro sabontaka; ya komo kwanakin ƙuruciyassa ke nan.” (Ayuba 33:25) Dubi yadda zai zama abin farinciki ne fa ka jefas da waɗannan madubin idanu, abubuwa jin gari, sandunan tafiya, kekunan guragu, da kuma magungunan nan! Ba za a sāke bukatar asibitoci, likitoci, har kuma da likitocin haƙora kuma.

10. Minene zai faru ga mutuwa?

10 Mutane da suke moran irin cikakken lafiyar jikin nan ba zasu so su mutu ba. Kuma ba zasu yi hakan ba, gama mutane ba zasu sāke kasance cikin riƙon rashin cikawa da mutuwa da aka gāda ba. Kristi “dole zaya yi mulki, har [Allah] ya sa dukan maƙiyansa ƙalƙashin sawayensa. Maƙiyi na ƙarshe da za a kawas, mutuwa ne.” “Kyautar Allah rai na har abada ce.”​—⁠1 Korinthiyawa 15:​25, 26; Romawa 6:23; duba kuma Ishaya 25:⁠8.

11. Ina yadda Ru’ya ta Yohanna ya taƙaita albarkatai na sabuwar duniyan?

11 A yin hasalin albarkatai da zasu zubo daga Allah mai-kulawa ga iyalin yan-Adam cikin Aljanna fa, littafin ƙarshe na Littafi Mai-tsarki ya ce: “[Allah] zaya share dukan hawaye kuma daga idanunsu; mutuwa kuwa ba zata ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙinzuciya, ko kuka, ko azaba. Al’amura na fari sun shuɗe.”​—⁠Ru’ya ta Yohanna 21:​3, 4.

Matattu Sun Komo

12. Ina yadda Yesu ya nuna ikon da Allah ya bayas na tadda matattu?

12 Yesu ya aika fiye da warkas da masu ciwo da kuma guragu. Ya komo da mutane ma daga kabari. Da haka fa ya gwada iko mai-girma na tadda matattu da Allah ya ba shi. Ka tuna da wani lokaci da Yesu ya zo gidan wani mutum wanda ɗiyarsa ta mutu? Yesu ya ce ma matacciyar yarinyar: “Yarinya, ina ce maki, ki Tashi.” Da wane sakamako? “Nan da nan yarinya ta tashi, ta soma tafiya.” Sa’anda mutanen, da ke wurin suka ga abin nan suka “yi mamaki mai-girma.” Hakika basu iya riƙe farincikinsu ba!​—⁠Markus 5:41, 42; duba kuma Luka 7:​11-16; Yohanna 11:​1-⁠45.

13. Wane irin mutane ne za a tashe su daga matattu?

13 A cikin sabuwar duniyar “za a yi tashin matattu, na masu-adilci da na marasa-adilci.” (Ayukan Manzanni 24:15) A lokacin fa Yesu zaya yi amfani da ikonsa da Allah ya ba shi don ya tadda matattu, gama ya ce, “Nine tashin matattu, nine rai. Wanda ya bada gaskiya gareni, ko ya mutu, za shi rayu.” (Yohanna 11:25) Kuma ya ce: “Dukan waɗanda suna cikin karbarun tuni [cikin azancin Allah] zasu ji muryatasa [Yesu] su fito kuma.”​—⁠Yohanna 5:​28, 29.

14. Domin mutuwa ba zai kasance kuma ba, waɗanne abubuwa ne za a kawas da su?

14 Murna mai-girma zai kasance a dukan duniya yayinda rukunonin matattu suna komowa zuwa rai su haɗa da ƙaunatattunsu! Ba za a ƙara ganin talifin sanarwan mutuwa a jaridu da zai kawo baƙinciki ga waɗanda suka tsira ba. Maimakon haka, aƙasarin haka za a shaida: sanarwan sabbobi da aka tashe su wanda zai kawo murna ga masu ƙaunarsu. Saboda haka babu jana’iza kuma, tarin itacen kone gawaye, wuraren kone gawaye, ko kuwa makabarai!

Duniya ta Salama na Gaskiya

15. Ina yadda za a cika annabcin Mikah a cikakkiyar azanci?

15 Za a samu salama ta gaskiya a dukan fasalolin rayuwa. Yaƙoƙi, waɗanda suke gabatad da yaƙoƙi, da keran makamai zasu zama abubuwa da suka shuɗe ko. Don me? Domin rarrabuwar al’ummai, kabilai, da fata zasu ɓace sarai. A cikakken azanci, kuma, “al’umma ba zata zare ma al’umma takobi ba, ba kuwa zasu ƙara koya yaƙi ba.”​—⁠Mikah 4:⁠3.

16. Ina yadda Allah zaya tabbatas da cewa babu yaƙi kuma?

16 Wannan zai iya zama abin mamaki domin tarihin yaƙin mai-barna mara sauyewa. Amma hakan ya zama domin kasancewar mutane ƙalƙashin sarautar yan-Adam da aljannu ne. A cikin sabuwar duniyar, ƙalƙashin sarautar Mulkin, ga abinda zai faru: “Ku zo, ku duba ayukan Jehovah . . . Ya sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya; ya karya baka, ya daddatse māshi; ya ƙoƙone karusai [na yaƙi] cikin wuta.”​—⁠Zabura 46:​8, 9.

17, 18. Wane irin dangantaka ne zai wanzu tsakanin dabbobi da mutane, cikin sabuwar duniyan?

17 Mutum da dabba ma zasu kasance cikin salama, kamar yadda suke cikin Adnin. (Farawa 1:28; 2:19) Allah ya ce: “A ranan nan zan yi masu alkawali da namomin jeji, da tsuntsayen sama, da masu-rarrafe . . . in kwanshe su lafiya kuma.”​—⁠Hosea 2:⁠18.

18 Ina iyakar faɗin salamar nan? “Kerkeci zaya zauna tare da ɗan rago, damisa kuma zata kwanta tare da ɗan akuya; da ɗan maraƙi da ɗan zaki da kiyayayyen ɗan sā zasu zauna wuri ɗaya; ɗan yaro kuwa zaya bishe su.” Dabbobi ba zasu ƙara zama abin razana ga mutum ko ga junansu ba. “Zaki kuwa zaya ci ciyawa kamar sā”!​—⁠Ishaya 11:​6-⁠9; 65:⁠25.

Duniya da Aka Juya Zuwa Aljanna

19. Za a juya duniyar zuwa minene?

19 Za a juya dukan duniya zuwa gida na aljanna ga mutane. Shi yasa Yesu ya iya yin alkawali ga wani mutum da ya gaskata shi haka: “Zaka kasance da ni cikin Aljanna.” Littafi Mai-tsarki ya ce: “Jeji da ƙeƙasashiyar ƙasa zasu yi farinciki; hamada kuma zata yi murna, ta yi fure kamar wardi . . . Gama cikin jeji ruwaye zasu ɓullo, rafufuka kuma a cikin hamada.”​—⁠Luka 23:⁠43; Ishaya 35:⁠1, 6.

20. Me yasa yunwa ba zai ƙara wulakantar da mutane kuma ba?

20 A ƙalƙashin Mulkin Allah fa, yunwa ba zai sāke wulakantar da miliyoyin mutane kuma ba. “Za a yi albarkar hatsi a ƙasa a bisa ƙwanƙolin duwatsu; zangarku zasu riƙa lilo.” “Itatuwan gonaki zasu bada ’ya’ya, ƙasa zata bada amfaninta, zasu zauna lafiya a ƙasarsu.”​—⁠Zabura 72:16; Ezekiel 34:⁠27.

21. Minene zai faru ga rashin gidaje, wurin kwanciya, da mumunan anguwa?

21 Babu talauci, babu mutane masu rashin gida, wurin kwanciya, ko kuwa anguwa da ke cike da aika laifi. “Zasu gina gidaje, kuma zasu zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu.” “Amma kowa zaya zauna a ƙalƙashin kuringar anab nasa da itacen ɓaurensa; ba kuwa wani mai-tsoratadda su.”​—⁠Ishaya 65:21, 22; Mikah 4:⁠4.

22. Ina yadda Littafi Mai-tsarki ya kwatanta albarkatan sarautar Allah?

22 Yan-Adam zasu more dukan waɗannan abubuwa, da ƙarin wasu kuma, cikin Aljanna. Zabura 145:16 ya ce: “[Allah] kana buɗe hannunka, kana biya ma kowane mai-rai muradinsa.” Babu mamaki ke nan da annabcin Littafi Mai-tsarki ya furta cewa: “Amma masu-tawali’u zasu gāji ƙasan; zasu faranta zuciyassu kuma cikin yalwar salama. . . . Masu-adilci zasu gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”​—⁠Zabura 37:​11, 29.

Kawas da Abin Ɗā

23. Ina yadda Mulkin Allah zai kawas da dukan wahala da muka taɓa sha?

23 Mulkin Allah zai kawas da dukan barna da an yi ma iyalin yan-Adam ko tun shekaru dubu shidda da suka shige. Murna na lokacin fa zai zarce kowane irin wahala da mutane sun taɓa sha. Babu tunin wani mumunan yanayi na dā da zai ɓata rayuwa kuma. Tunani da ayuka masu ginawa da zasu zama halayen mutane duka fa da sannu sannu zasu kawas da tuni masu ɓacin rai nan.

24, 25. (a) Minene Ishaya ya annabta cewa zai faru? (b) Me yasa zamu gaskata cewa tunanin wahala da muka sha a dā zasu koɗe?

24 Allah mai kulawan ya furta haka: “Gama ga shi, sabbobin sammai [sabuwar gwamnati ta sama bisa mutane] da sabuwar duniya [jam’iyyar yan-Adam masu adilci] nike halitta; ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa zasu shiga zuciya ba. Amma sai ku yi murna ku yi farinciki har abada da abinda ni ke halittawa.” “Dukan duniya tana zaune a huce, da rai a kwance, fashe da rairawa suke yi.”​—⁠Ishaya 14:⁠7; 65:​17, 18.

25 Ta wurin Mulkinsa fa, Allah zai sāke sarai mumunan yanayi da ya wanzu da daɗewa nan. A dukan matuƙa fa zaya nuna kulawarsa mai-girma garemu ta wurin zuba albarkatai nasa fiye da wani ɓacin rai da muka taɓa sha a cikin rayuwa a dā. Wahaloli da muka taɓa sha zasu ɓace sarai a lokacin, idan ma mun tuna da su ke nan fa.

26. Me yasa Allah zaya biya ladar wahala da muka sha a dā?

26 Haka ne fa Allah zai biya ma shan wahala da mun iya jimre masu cikin duniyar nan. Ya sani cewa ba laifin mu ba ne da aka haife mu marasa cikawa, gama mun gāda rashin cikawa daga wurin iyayenmu na farko ne. Ba laifin mu ba ne da aka haife mu cikin duniyar shaitan, gama da Adamu da Hawa’u sun kasance da aminci da an haife mu cikin aljanna maimakon haka. Saboda haka da tausayi mai-girma fa Allah zaya yi abinda ya ninke mumunan abubuwa da aka ɗanka mana.

27. Waɗanne annabce-annabce ne zasu samu cikawarsu masu ban al’ajibi cikin sabuwar duniyan?

27 A cikin sabuwar duniyar, mutane zasu more yanci da aka annabta a Romawa 8:​21, 22: “Ana bege talikai da kansu kuma zasu tsira daga bautar ɓacewa zuwa cikin yanci na darajar ’ya’yan Allah. Gama mun sani dukan talikai suna nishi suna naƙuda tare da mu har yanzu.” Sa’annan fa mutane zasu ga cikawar addu’ar nan sarai: “Mulkinka shi zo. Abinda ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.” (Matta 6:10) Yanayoyi masu ban al’ajibi da suke Aljanna na duniya fa zasu kamanta waɗanda ke cikin sama.

[Hotuna a shafi na 23]

A cikin sabuwar duniyar, tsofaffi zasu komo zuwa ƙarfin ƙuruciyassu

[Hoto a shafi na 24]

Za a kawas da dukan ciwo da rashin cikawar jiki cikin sabuwar duniyan

[Hoto a shafi na 25]

A cikin sabuwar duniyan, matattu ma zasu tashi zuwa rai

[Hoto a shafi na 26]

‘Ba zasu ƙara koyan yaƙi kuma ba’

[Hotuna a shafi na 27]

Yan-Adam da dabbobi zasu zama cikin cikakkiyar salama cikin Aljanna

[Hotuna a shafi na 27]

‘Allah zaya buɗe hannunsa kuma ya biya muradin kowane abu mai-rai’

[Hoto a shafi na 28]

Mulkin Allah zai aika fiye da kawas da wahala da muka jimre da su kawai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba