Miliyoyin Halittu na Ruhu
Littafi Mai-tsarki ya gaya mana cewa akwai masu rai na ruhu dayawa. Je hovah da kansa ma ruhu ne.—Yohanna 4:24; 2 Korinthiyawa 3:17, 18.
Akwai lokacinda Jehovah shine kaɗai cikin dukan sarari. Daga nan ya soma halittar halittun ruhu da ake kiran su mala’iku. Sun fi girma kuma sun fi basira da yan-Adam. Jehovah ya halicce mala’iku dayawa; a cikin ru’ya fa, bawan Allah Daniel ya ga mala’iku miliyan ɗari.—Daniel 7:10; Ibraniyawa 1:7.
Waɗannan mala’iku Allah ne ya halicce su kafin ya yi duniya. (Ayuba 38:4-7) Babu ko ɗaya cikinsu da mutum ne da ya taɓa rayuwa kuma mutu a duniya.
[Hoto a shafi na 7]
Ruhu mai-girma, Jehovah, ya halicce miliyoyin ruhohi masu-rai