Tawaye a Cikin Lardi na Ruhu
Dukan ruhu masu-rai da Jehovah ya halitta nagargaru ne. Sai wani mala’ika ya zama mugu. Shine Shaitan Ibelis. Shaitan yana son mutane a duniya su yi masa sujada maimakon Jehovah. Ga abinda ya faru:
A cikin gonar Adnin fa, da akwai itattuwa dayawa da suke bada ya’ya masu-daɗi. Jehovah ya gaya ma Adamu da matarsa, Hawa’u, cewa su a iya ci daga kowanne a cikinsu. Amma akwai itace ɗaya da Allah ya ce kada su ci daga ciki. Ya ce idan suka ci daga cikinsa fa, zasu mutu lallai.—Farawa 2:9, 16, 17.
Wata rana fa yayinda Hawa’u ce kaɗai da kanta sai wani maciji ya yi mata magana. Hakika, ba macijin ne da gaske ya yi magana ba; Shaitan Ibelis ne yasa ya zama kamar macijin ne ke magana. Shaitan ya gaya ma Hawa’u cewa idan ta ci daga itacen nan, zata waye kamar Allah. Ya kuma ce wai baza ta mutu ba. Dukan waɗannan furcin ƙarya ne. Duk da haka dai, Hawa’u ta amince da Shaitan kuma ta ci ya’yan itacen. Nan gaba, sai ta bada shi ga Adamu, kuma shi ma ya ci.—Farawa 3:1-6.
Daga wannan labarin gaskiya fa, mun sani cewa Shaitan ɗan-tawaye ne da kuma maƙaryaci. Ya gaya ma Hawa’u cewa idan ta yi rashin biyyaya ga Allah, baza ta mutu ba. Hakan ƙarya ne. Ta kuwa mutu hakanan ma Adamu. Shaitan kuwa baya mutu a lokacin ba, amma zaya mutu kuwa lallai domin ya yi zunubi. Amma, yanzu haka, yana nan da rai kuma yana ci gaba da ruɗin mutane. Har ila shi maƙaryaci ne, kuma yana ƙoƙarin sa mutane su taka dokokin Allah.—Yohanna 8:44.
Wasu Mala’iku Sun Yi Tawaye
Nan gaba, wasu mala’iku suka zama miyagu. Waɗannan mala’ikun sun hange mata kyawawa a duniya kuma sun so su yi ma’amala da su. Da haka fa suka sauƙo duniya kuma suka yafa jikunan yan-Adam mazaje. Sai suka ɗauko ma kansu matan. Wannan gāba yake da nufin Allah.—Farawa 6:1, 2; Yahuda 6.
Hakan ya kawo damuwa na ƙwarai ga mutane ma. Matan waɗannan mala’iku sun haifi ya’ya, amma ya’yansu ba kamar yadda aka san yara ba ne. Da girmansu suka zama kattai masu nuna ƙarfi da kuma masu-cin zali. Da sannu sannu fa duniya ta ciku da mugunta da Jehovah ya shawarta ya hallakas da miyagun mutane da tufana mai-girma. Yan-Adam da suka tsira daga Tufanan fa sune adilai Nuhu da iyalinsa.—Farawa 6:4, 11; 7:23.
Amma dai, miyagun mala’iku nan, sun komo zuwa lardi na ruhu; su kuwa basu mutu ba. Amma an horace su. Ba a yarda masu su shiga cikin iyalin Allah na amintattu mala’iku ba. Bugu kan kari, Jehovah baya yarda masu su iya yafa jikunan yan-Adam kuma ba. Kuma nan gaba fa zasu mutu cikin hukunci mai-girma.—2 Bitrus 2:4; Yahuda 6.
An Jefas da Shaitan Daga Sama
A somawar ƙarninmu, an gwabza wata yaƙi a sama. Littafin Ruya ta Yohanna na Littafi Mai-tsarki ya kwantata abinda ya faru: “Aka yi yaƙi cikin sama, Mika’ilu [Yesu Kristi wanda aka tashe shi daga matattu] da nasa [nagargarun] mala’iku suna fita su yi gāba da [Shaitan] dragon; dragon kuma ya yi gāba tare da nasa [miyagun] mala’iku, basu rinjaya ba, ba a kuwa ƙara tarasda masayinsu cikin sama ba. Aka jefasda babban dragon, tsofon maciji, shi wanda ana ce da shi Ibelis da Shaitan, mai-ruɗin dukan duniya; aka jefas da shi a duniya, aka jefasda [miyagun] mala’ikunsa kuma tare da shi.”
Minene sakamakon haka? Labarin ya ci gaba da cewa: “Domin wannan fa, ku yi farinciki, ya sammai, da ku mazauna a ciki.” Nagargarun mala’ikun su a yi farinciki domin Shaitan da miyagun mala’iku, ko kuwa ruhohin, basu cikin sama kuma. Amma game da mutane a duniya fa? Littafi Mai-tsarki ya ce: “Kaiton duniya da teku: domin Shaitan ya sauko wajenku, hasala mai-girma kuwa gareshi, domin ya sani sauran zarafinsa kaɗan ne.”—Ru’ya ta Yohanna 12:7-9, 12.
I fa, Shaitan da miyagun abokansa suna ruɗi da kuma kawo bala’i masu girma ga mutane a duniya. Ana kira waɗannan miyagun mala’iku ajannu. Magabtan Allah ne su. Dukan su miyagu ne.
[Hoto a shafi na 8]
Lokacinda Shaitan ya yi amfani da maciji don ya yi magana da Hawa’u, ta haɗa da shi cikin yin tawaye da Allah
[Hoto a shafi na 9]
Miyagun mala’iku sun zo duniya kuma sun yi ma’amala da mata
[Hoto a shafi na 10]
An jefasda Shaitan da miyagun mala’ikunsa daga sama