Sashe na 6—Abinda Yasa Allah Ya Kyale Shan Wahala
1, 2. Ina yadda iyayenmu na farko suka ɓata somawa mai-kyau da Allah ya basu?
MINENE ya faru? Minene ya faru da ya ɓace somawa mai-kyau da Allah ya ba iyayenmu na fari cikin Aljanna na Adnin? Me yasa, maimakon salama da jituwa na Aljanna, mugunta da wahala sun ɗawwama cikin duban shekaru yanzu?
2 Dalilin haka shine wai Adamu da Hawa’u sun ɓace amfanin son zuciya nasu. Sun kasa tuna da gaskiyar cewa ba a halicce su su ni’imta waje da Allah da dokokinsa ba. Sun zaɓa su yance kansu daga Allah, da zaton cewa hakan zai gyarta rayuwarsu. Da haka fa suka ketare iyaka na son zuciya da Allah ya bayas.—Farawa, sura 3.
Muhawwarar Ikon Sarauta na Dukan Sarari
3-5. Me yasa Allah baya hallakas da Adamu da Hawa’u nan da nan don kuma ya sāke yin wasu ba?
3 Me yasa Allah baya dai hallakas da Adamu da Hawa’u kuma ya sāke halittar wasu yan-Adam biyu ba? Haka wannan yake domin an zarge, ikon sarautarsa na dukan sarari, watau, damar sarautarsa wanda babu wani da zai kwashe.
4 Tambayar ita ce: Wanene yake da ikon yin sarauta, da kuma sarautar wanene ya dace? Domin shi maɗaukakki ne da kuma Mahaliccin dukan halittu fa ya ba Allah ikon sarauta bisansu. Tun da shike mai-mafifficin hikima ne, sarautarsa shi ya fi kyau ga dukan halittu. Amma ga shi an zarge sarautar Allah ko. To, ashe da wani abinda ya ƙusƙura da halittarsa—mutum ne? Nan gaba fa zamu gwada yadda haka ya shafe kāmalar yan-Adam.
5 Yancewar mutum daga Allah, ya tadda wata tambaya: Anya yan-Adam zasu fi aikawa da kyau idan ba su ƙalƙashin sarautar Allah? Babu shakka fa Mahalicci ya san amsar, amma hanya na tabbataswa sarai ita ce na ba yan-Adam yanci mara-iyaka da suke so. Su suka zaɓi tafarkin son zuciyarsu, saboda haka Allah ya kyale shi.
6, 7. Don me Allah ya ba yan-Adam yanci mara-iyaka da daɗewa haka?
6 Ta wurin ba yan-Adam isasshen lokaci don su gwada yanci mara-iyaka fa, Allah zai iya warware sarai al’amarin ko yan-Adam zasu fi yin aikawa da kyau a ƙalƙashin sarautar Allah ko kuwa nasu. Kuma lokaci da za a bayas fa tilas ya kasance da tsawo sosai don yan-Adam su kai matsayi da zasu ce da shi mai-girma duka a fasalin siyasa, sana’a, kimiya, da jinya.
7 Saboda haka, Allah ya ba mutum cikakken yanci har zuwa kwananmu don ya nuna sarai ko sarautar yan-Adam waje da shi zai yi nasara. Da haka kuwa mutum ya iya zaɓa ko tsakanin tawali’u da zalunci, tsakanin ƙauna da ƙiyayya, tsakanin adilci da mugunta. Amma ya fuskance sakamakon zaɓansa ko shi kansa: nagarta da salama ko kuwa mugunta da shan wahala.
Tawayen Halittun Ruhu
8, 9. (a) Ta yaya ne tawaye ta soma cikin lardi na ruhu? (b) Waɗannene kuma ban da Adamu da Hawa’u ne Shaitan yasa su tawaye?
8 Akwai kuma wani batu na yin la’akari. Ba iyayenmu na farko ne kaɗai suka yi tawaye da sarautar Allah ba. Amma wanene kuma ke da rai a lokacin? Halittun ruhu. Kafin Allah ya halicce yan-Adam, ya halicce wasu irin rai mai-girma, jimillar mala’iku mai-girma, don su rayu cikin lardi na samaniya. Su ma an halicce su da son zuciya kuma suna bukata su yi biyayya ga sarautar Allah.—Ayuba 38:7; Zabura 104:4; Ru’ya ta Yohanna 5:11.
9 Littafi Mai-tsarki ya nuna cewa tawaye na farko ta soma cikin lardi na ruhu ne. Wani halitta na ruhu ya bukace yanci mara-iyaka. Yana ma son yan-Adam su bauta masa. (Matta 4:8, 9) Ruhun mai-tawayen nan ya zama tasirin tawayen Adamu da Hawa’u, wanda ke da’awar ƙarya cewa Allah yana riƙe wani abu maikyau daga garesu. (Farawa 3:1-5) Saboda haka an ƙira shi Ibelis (Mai-ɓatanci) da kuma Shaitan (Ɗan hammaya). Nan gaba fa, ya ruɗas da wasu halittun ruhu ga yin tawaye su ma. Waɗanda suka zama aljannu.—Kubawar Shari’a 32:17; Ru’ya ta Yohanna 12:9; 16:14.
10. Minene sakamakon tawayen yan-Adam da halittun ruhu?
10 Ta wurin yin tawaye da Allah fa, yan-Adam sun bada kansu ga tasirin Shaitan da aljannunsa. Shi yasa Littafi Mai-tsarki ya kira Shaitan “allah na wannan zamani,” wanda “ya maƙantar da idanun marasa bangaskiya.” Saboda haka ne, Kalmar Allah ta ce “duniya duka tana kwanciya cikin ikon mugun nan.” Yesu kansa ya kira Shaitan “mai-sarautar wannan duniya.”—2 Korinthiyawa 4:4; 1 Yohanna 5:19; Yohanna 12:31.
Muhawwarai Biyu
11. Game da wane muhawwara ne kuma Shaitan ya zarge Allah?
11 Shaitan ya tadda wani muhawwara kuma ya zarge Allah. A taƙaice dai, ya ce wai Allah ya yi ƙusƙuri a hanyar da Ya halicce yan-Adam kuma cewa babu wani da zai so ya yi abinda ya dace yayinda yake cikin tsanani. Hakika fa, ya yi da’awar cewa a cikin jaraba fa zasu zarge Allah. (Ayuba 2:1-5) Hakanan fa Shaitan ya tuhume kāmalar halittan yan-Adam.
12-14. Ina yadda lokaci zai bayana gaskiyar muhawwarai da Shaitan ya tadda su?
12 Saboda haka, Allah ya bada isasshen lokaci ko ga dukan halittu masu basira don a ga yadda za a warware muhawwarar nan da kuma na ikon sarautar Allah. (Gwada da Fitowa 9:16.) Abinda zai faru nan gaba ga yan-Adam zai bayana gaskiya game da waɗannan muhawwarai.
13 Da farko fa, minene lokaci zai bayana game da muhawwarar ikon sarauta na dukan sarari, dacewar sarautar Allah? Ashe yan-Adam zasu iya sarautar kansu fiye da Allah? Ashe da akwai wata irin sarautar yan-Adam waje da Allah da zai shigar da duniya yantacce daga yaƙi, aika laifi, da kuma rashin shari’a? Anya da akwai wani da zai kawas da talauci kuma ya tanadar da ni’imtawa ga mutane duka? Anya da akwai wani da zai ci nasara da ciwo, tsofewa, da kuma mutuwa? An shirya sarautar Allah don ya yi dukan waɗannan.—Farawa 1:26-31.
14 Game da muhawwara na biyu fa, minene lokaci zai bayana game da girman halittan yan-Adam? Ashe ƙusƙuri ne don Allah ya halicce yan-Adam yadda ya yi? Ashe akwai wani daga cikinsu wanda zai yi abinda ya dace ƙalƙashin jarabawa? Ashe akwai wasu mutane waɗanda zasu nuna cewa suna son sarautar Allah fiye da sarautar yan-Adam na yancin kai?
[Hoto a shafi na 13]
Allah ya ba yan-Adam isasshen lokaci ko don su kai girman matsayin aikinsu
[Inda Aka Ɗauko]
Jiragen sama: Daga foton NASA