Babi Na Shida
Al’amari da Dukanmu Dole Mu Fuskanta
1, 2. (a) Wane al’amari ne Shaiɗan ya tayar a Adnin? (b) Menene nufin wannan al’amarin a abin da ya faɗa?
WANI muhimmin al’amari da bil Adam suke fuskanta ya shafe ka. Matsayinka game da shi zai nuna inda za ka dawwama. Wannan al’amarin ya taso ne lokacin da aka yi tawaye a Adnin. A lokacin, Shaiɗan ya tambayi Hauwa’u: “Ko Allah ya ce, ba za ku ci daga dukan itatuwa na gona ba?” Ta amsa cewa, Allah ya ce game da wani itace: ‘Ba za mu ci ba, . . . domin kada mu mutu.’ Sai Shaiɗan ya tuhumi Jehovah da yin ƙarya, yana cewa rayuwar Hauwa’u da ta Adamu ba ta dangana ga yin biyayya ga Allah ba. Shaiɗan ya yi da’awar cewa Allah ya hana halittunsa wani abu ne mai kyau—iya tsara nasu mizanin rayuwa. Sai Shaiɗan ya ce: “Allah ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su buɗe, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.”—Farawa 3:1-5.
2 A taƙaice, Shaiɗan cewa yake wai bil Adam za su fi morewa idan suna yanke nasu shawara maimakon yin biyayya ga dokokin Allah. Saboda haka ya ƙalubalanci hanyar sarauta ta Allah. Wannan ne ya ta da al’amari mafi muhimmanci na ikon mallakar dukan sararin samaniya na Allah, watau, ikonsa ya yi sarauta. Ga tambayar da ta taso: Wacce ta fi wa bil Adam kyau, hanyar sarauta ta Jehovah ko ’yancin kai daga wajensa? To, da Jehovah ya halaka Adamu da Hauwa’u nan da nan, amma hakan ba zai warware al’amari na ikon mallakar a hanyar da za ta gamsar ba. Ta barin jam’iyyar bil Adam ta bunƙasa na ɗan lokaci, Allah ya nuna daidai abin da ’yanci daga gare sa da kuma daga dokokinsa zai jawo.
3. Wane al’amari ne na biyu Shaiɗan ya tayar?
3 Farmakin Shaiɗan a kan ikon sarauta ta Jehovah bai tsaya a abin da ya faru a Adnin ba. Ya kuma tuhumi amincin wasu ga Jehovah. Wannan ya zama al’amari na biyu da yake da dangantaka da shi. Wannan ƙalubalan ya haɗa da ’ya’yan Adamu da Hauwa’u da kuma dukan ’ya’yan ruhu na Allah, har ma da Ɗan farin Jehovah da yake ƙauna sosai. Alal misali, a zamanin Ayuba, Shaiɗan ya yi tuhuma, cewa waɗanda suke bauta wa Jehovah suna yin haka ne, ba domin suna ƙaunarsa da hanyarsa ta sarauta ba ne, amma domin son kai ne. Ya nace cewa idan aka wahalar da su, za su bi son zuciyarsu.—Ayuba 2:1-6; Ru’ya ta Yohanna 12:10.
Abin da Tarihi Ya Tabbatar
4, 5. Menene tarihi ya tabbatar game da mutum da ja-gorar mutum ga kansa?
4 Abu mai muhimmanci a al’amarin nan na sarauta shi ne: Allah bai halicci mutane su sami ’yancin kai daga sarautarsa kuma su yi nasara ba. Domin amfaninsu ya yi su su dogara ga dokokinsa na adalci. Annabi Irmiya ya ce: “Ya Ubangiji, na tabbata hanyar mutum ba cikin nasa hannu ta ke ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa. Ya Ubangiji, kā tsauta ni.” (Irmiya 10:23, 24) Domin haka, Kalmar Allah ta aririta: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi.” (Misalai 3:5) Kamar yadda Allah ya yi mutane su kasance ƙarƙashin dokokinsa na zahiri domin su rayu, haka ma ya yi dokoki na ɗabi’a da idan mun bi zai kawo haɗin kai na jam’iyya.
5 A bayyane yake, Allah ya sani cewa iyalin bil Adam ba za ta taɓa yin nasara ba daga nata ja-gora ba tare da nasa sarauta ba. A ƙoƙarin wofi na neman samun nasarar ’yancin kai daga sarautar Allah, mutane sun kafa tsarin siyasa, na tattalin arziki, da kuma na addini. Waɗannan bambanci kullayaumi ya jawo jayayya da juna, da ke jawo nuna ƙarfi, yaƙi, da kuma mutuwa. “Mutum ya sami iko bisa wani, ikon kuwa ya ciwuce shi.” (Mai-Wa’azi 8:9) Abin da ya faru ke nan a dukan tarihin mutane. Kamar yadda aka annabta cikin Kalmar Allah, miyagu da ’yan hila suna “daɗa mugunta gaba gaba.” (2 Timothawus 3:13) A cikin ƙarni na 20, da mutane sun bunƙasa ƙwarai a hanyar kimiyya da fasaha, amma sun ga bala’i da babu irinsa. Kalmomin Irmiya 10:23 sun tabbata ƙwarai—ba a halicci mutane su yi ja-gorar kansu ba.
6. Ta yaya ne ba da jimawa ba Allah zai warware ’yancin kai na ’yan Adam daga wajensa?
6 Mummunar sakamakon ’yancin kai daga Allah da ya daɗe ya nuna cewa sarautar mutane ba za ta yi nasara ba. Sarautar Allah ce kawai hanyar farin ciki, haɗin kai, lafiyar jiki, da kuma rai. Kuma Kalmar Allah ta nuna cewa ƙyale ’yancin kai na sarautar ’yan Adam da Jehovah ya yi yana zuwa ƙarshensa. (Matta 24:3-14; 2 Timothawus 3:1-5) Ba da jimawa ba, zai sa hannu cikin harkokin mutane don ya saka nasa sarauta bisa duniya. Annabcin Littafi Mai Tsarki ya ce: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna [sarautar ’yan Adam mai ci a yau] kuwa, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki [a sama], wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautarsa kuwa ba za a bar ma wata al’umma ba [mutane ba za su sake yin sarautar duniya ba]; amma za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki [na yanzu] ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.”—Daniel 2:44.
Tsira Zuwa Cikin Sabuwar Duniya ta Allah
7. Yayin da sarautar Allah ta kawo ƙarshen sarautar mutane, su wa za su tsira?
7 Yayin da sarautar Allah ta kawo ƙarshen sarautar mutane, su wa za su tsira? Littafi Mai Tsarki ya amsa: “Masu-adalci [waɗanda suke goyon bayan sarautar Allah] za su zauna cikin ƙasan, kamilai kuma za su wanzu a cikinta. Amma za a datse miyagu [waɗanda ba sa goyon bayan sarautar Allah] daga cikin ƙasan.” (Misalai 2:21, 22) Hakanan ma, mai Zabura ya ce: “In an jima kaɗan, sa’annan mai-mugunta ba shi . . . Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zabura 37:10, 29.
8. Ta yaya ne Allah zai yi cikakkiyar kunita ikonsa na mallaka?
8 Bayan an halaka zamanin Shaiɗan, Allah zai kawo sabuwar duniya, wadda za ta kawar da nuna ƙarfi, yaƙe-yaƙe, talauci, wahala, ciwo gabaki ɗaya, da kuma mutuwa, da ta mai da mutane bayinta na shekaru dubbai yanzu. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta albarka da ke jiran mutane masu biyayya da kyau: “[Allah] za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙinzuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” (Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Ta wurin Mulkinsa na samaniya ƙarƙashin Kristi, Allah zai kunita (ko kuma tabbatar da) Ikonsa na Mamallaki, watau, Masaraucinmu.—Romawa 16:20; 2 Bitrus 3:10-13; Ru’ya ta Yohanna 20:1-6.
Yadda Wasu Suka Nuna Matsayinsu a Al’amarin
9. (a) Ta yaya waɗanda suka kasance da aminci ga Jehovah suka ɗauki maganarsa? (b) Ta yaya Nuhu ya tabbatar da amincinsa, kuma ta yaya za mu amfana daga misalinsa?
9 Duk cikin tarihi, an samu mutane maza da mata da suka tabbatar da amincinsu na manne wa Jehovah cewa shi ne Mamallaki. Sun sani cewa rayuwarsu ta dangana ne bisa ga sauraronsa da kuma yi masa biyayya. Haka Nuhu yake. Sai, Allah ya ce wa Nuhu: “Matuƙar dukan abu mai-rai a garemu ta yi . . . Ka yi jirgi.” Nuhu kuwa ya bi ja-gorar Jehovah. Duk da gargaɗi da aka yi, sauran mutanen zamanin suka ci gaba da rayuwarsu ta yau da kullum kamar babu abin da zai faru. Amma Nuhu ya gina babban jirgi kuma ya shagala wajen yi wa wasu wa’azi game da hanyoyin adalci na Jehovah. Labarin ya ci gaba: “Hakanan kuwa Nuhu ya yi; bisa ga abin da Allah ya umurce shi duka, haka ya yi.”—Farawa 6:13-22; Ibraniyawa 11:7; 2 Bitrus 2:5.
10. (a) Ta yaya Ibrahim da Saratu suka goyi bayan ikon mallaka na Jehovah? (b) A wace hanya ce za mu amfana daga misalin Ibrahim da Saratu?
10 Ibrahim da Saratu kuma misalai ne masu kyau na goyon bayan ikon mallaka na Jehovah, sun yi dukan abin da ya umurce su. Suna da zama a Ur na Kaldiyawa, birni mai ni’ima. Amma sa’ad da Jehovah ya gaya wa Ibrahim ya je wata ƙasa da bai san ta ba, Ibrahim ya yi “kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.” Babu shakka cewa Saratu ta more rayuwa—da gida, abokai, da kuma dangi. Duk da haka, ta yi biyayya ga Jehovah da mijinta kuma ta tafi ƙasar Kan’ana, ko da yake ba ta san yadda rayuwa za ta juya mata ba.—Farawa 11:31–12:4; Ayukan Manzanni 7:2-4.
11. (a) Ƙarƙashin wane irin yanayi ne Musa ya goyi bayan ikon mallaka na Jehovah? (b) Ta yaya misalin Musa zai iya taimakonmu?
11 Musa ma wani ne da ya goyi bayan ikon mallaka na Jehovah. Kuma ya yi hakan cikin yanayi mai wuya ƙwarai—a gaban Fir’auna na Masar, gaba da gaba. Ba wai Musa ya dogara ga kansa ba ne. Akasin haka, ya yi shakkar iya maganarsa. Amma ya yi wa Jehovah biyayya. Da goyon bayan Jehovah da kuma taimakon ɗan’uwansa, Haruna, a kai a kai Musa ya idar da maganar Jehovah ga Fir’auna mai taurin zuciya. Har wasu cikin Isra’ilawa ma sun kushe wa Musa sosai. Duk da haka, cikin aminci Musa ya yi dukan abin da Jehovah ya umurce shi ya yi, kuma ta wurinsa, Isra’ilawa suka samu ceto daga ƙasar Masar.—Fitowa 7:6; 12:50, 51; Ibraniyawa 11:24-27.
12. (a) Menene ya nuna cewa aminci ga Jehovah ya ƙunshi fiye da yin abin da Allah ya ambata a rubuce kawai? (b) Ta yaya fahimtar irin amincin nan za ta taimake mu mu yi amfani da 1 Yohanna 2:15?
12 Waɗanda suke da aminci ga Jehovah ba su yi tunanin cewa abin da ake bukata shi ne su yi biyayya kawai ga abin da Allah ya ce da ke rubuce ba. Yayin da matar Potiphar ta yi ƙoƙarin ta yaudari Yusufu ya yi zina da ita, babu wani umurni da aka rubuta daga Allah da ya haramta zina. Amma, Yusufu ya sani bisa ga tsarin aure da Jehovah ya kafa a Adnin. Ya sani cewa yin jima’i da matar wani zai ɓata wa Allah rai. Yusufu bai yi ƙoƙarin ya gwada iyakacin yadda Allah zai ƙyale shi ya yi daidai da Masarawa ba. Ya goyi bayan hanyoyin Jehovah ta yin bimbini a kan sha’anin da Allah ya yi da mutane kuma ya yi amfani da abin da ya fahimci shi ne nufin Allah.—Farawa 39:7-12; Zabura 77:11, 12.
13. Ta yaya aka tabbatar da Iblis maƙaryaci ne game da (a) Ayuba? (b) Ibraniyawa uku?
13 Ko sa’ad da suke cikin gwaji mai tsanani, waɗanda sun san Jehovah da gaske ba sa juya masa baya. Shaiɗan ya ce idan Ayuba ya yi hasarar dukiyarsa ko ya yi rashin lafiya, shi ɗin ma—da Jehovah ya yarda da shi sosai—zai yasar da Allah. Amma Ayuba ya tabbatar da Iblis maƙaryaci ne, ko da yake Ayuba kansa bai san dalilin da ya sa masifa ta faɗo masa ba. (Ayuba 2:9, 10) Ƙarnuka daga baya, a ƙoƙarin ya tabbatar da abin da ya ce, Shaiɗan ya sa sarkin Babila da ya fusata ya razanar da matasa Ibraniyawa uku, da cewa za su mutu cikin tanderu idan ba su yi sujjada a gaban gunki da sarkin ya ƙera ba. An tilasta musu su zaɓi tsakanin yin biyayya ga dokar sarki da kuma yin biyayya ga dokar Jehovah game da bautar gumaka, suka tsaya tsayin daka suka nuna cewa suna bauta wa Jehovah ne kuma shi ne Mamallakinsu Mafifici. Aminci ga Allah ya fi rai da suke da shi daraja!—Daniel 3:14-18.
14. Yaya yake yiwuwa mu ajizai mu tabbatar da cewa muna da aminci na gaske ga Jehovah?
14 Daga waɗannan misalai za mu kammala ne cewa domin a kasance da aminci ga Jehovah, dole ne mutum ya kasance kamili ko kuma cewa duk wanda ya yi kuskure ya kasa ke nan? Ba haka ba ne! Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa a wasu lokatai Musa ya yi kuskure. Ko da yake Jehovah bai yi farin ciki ba, amma bai yasar da Musa ba. Manzannin Yesu Kristi ma suna da nasu kumamanci. Domin Jehovah yana tunawa da gadōnmu na ajizanci, yana farin ciki idan ba da gangan muka yi banza da nufinsa ba a kowane hali. Idan domin kumamanci ne muka faɗi cikin wani laifi, yana da muhimmanci mu tuba da gaske kuma kada mu ci gaba da yin laifin. A wannan hanyar ce za mu nuna cewa muna ƙaunar abin da Jehovah ya ce nagari ne da gaske kuma mu ƙi abin da ya nuna cewa mummuna ne. Ta wurin bangaskiyarmu cikin darajar hadayar Yesu, za mu more tsayawa mai tsabta a gaban Allah.—Amos 5:15; Ayukan Manzanni 3:19; Ibraniyawa 9:14.
15. (a) Wanene ne kaɗai cikin mutane ya riƙe cikakken aminci ga Allah, kuma menene wannan ya tabbatar? (b) Ta yaya muka samu taimako daga abin da Yesu ya yi?
15 Amma, yin cikakkiyar biyayya ga ikon mallaka na Jehovah ba zai taɓa yiwuwa ba ne ga mutane? Amsar wannan kama take da ‘asiri’ na shekaru 4,000. (1 Timothawus 3:16) Ko da yake an halicci Adamu kamiltacce, bai bar misali mai kyau ba na ibada. To, wanene zai yi hakan? Hakika babu wani cikin ’ya’yansa masu zunubi. Yesu Kristi ne kaɗai wanda ya yi wannan. (Ibraniyawa 4:15) Abin da Yesu ya yi, ya tabbatar da cewa Adamu da yake cikin yanayi mafi kyau, da zai riƙe amincinsa ƙwarai idan ya so. Ba laifin halittar da Allah ya yi ba ne. Saboda haka, misalin Yesu Kristi ne muke ƙoƙarin mu yi koyi da shi a nuna biyayya ga dokokin Allah da kuma ba da kai ga Jehovah, wanda shi ne Mamallakin Dukan Halitta.—Kubawar Shari’a 32:4, 5.
Mecece Amsarmu?
16. Me ya sa dole ne mu kasance kullum a farke game da halinmu saboda ikon mallaka na Jehovah?
16 Dole ne kowannenmu ya fuskanci al’amarin nan na ikon mallakar dukan sararin samaniya. Idan mun nuna a fili cewa muna gefen Jehovah, sai mu zama abin farmaki na Shaiɗan. Zai kawo matsala daga dukan ɓangarori kuma ya ci gaba da yin haka har ƙarshen zamaninsa. Dole ne mu ci gaba da tsare kanmu. (1 Bitrus 5:8) Halayenmu na nuna gefen da muke a al’amarin ikon mallaka na Jehovah da kuma al’amari na biyu na kasancewa da aminci ga Allah lokacin gwaji. Ba zai dace ba mu koyi munanan halaye, cewa ba su da damuwa domin ana yi a ko’ina cikin duniya. Riƙe aminci yana bukatar mu yi amfani da hanyoyin adalci na Jehovah a dukan rayuwarmu.
17. Me muka sani game da asalin ƙarya da sata da zai sa mu guje su?
17 Alal misali, ba za mu yi koyi da Shaiɗan wanda shi ne “uban ƙarya” ba. (Yohanna 8:44) Dole ne mu kasance da gaskiya a dukan sha’aninmu. Cikin duniyar Shaiɗan, sau da yawa matasa ba sa gaya wa iyayensu gaskiya. Amma matasa Kirista suna guje wa wannan, ta haka kuwa suna tabbata da ƙaryar tuhumar Shaiɗan cewa mutanen Allah za su yasar da amincinsu cikin gwaji. (Ayuba 1:9-11; Misalai 6:16-19) Akwai wasu kasuwanci da ke iya nuna mutum cewa na “uban ƙarya” ne maimakon na Allah mai gaskiya. Muna guje wa waɗannan. (Mikah 6:11, 12) Sata ba za a taɓa cewa daidai ba ce, ko idan mutum yana cikin bukata ne ko wanda aka yi masa sata yana da arziki. (Misalai 6:30, 31; 1 Bitrus 4:15) Ko idan yin haka hali ne inda muke da zama ko da abin da aka sace ƙarami ne, sata ta saɓa wa dokokin Allah.—Luka 16:10; Romawa 12:2; Afisawa 4:28.
18. (a) A ƙarshen Sarautar Shekaru Dubu na Kristi, wane gwaji za a yi wa dukan mutane? (b) Wane irin hali ya kamata mu koya a yanzu?
18 A lokacin Sarautar Shekara Dubu na Kristi, za a saka Shaiɗan da aljanunsa cikin rami, ba za su iya rinjayar mutane ba kuma. Wannan zai kawo sauƙi ƙwarai! Amma bayan shekara dubun, za a kwance su na ɗan lokaci. Shaiɗan da dukan waɗanda suka bi shi za su matsa wa mutane da aka maido su da suke riƙe amincinsu ga Allah. (Ru’ya ta Yohanna 20:7-10) To, idan mun samu gatar kasancewa da rai, yaya za mu yi a zancen al’amari game da ikon mallakar dukan sararin samaniya? Tun da yake dukan mutane za su zama kamiltattu, idan an yi rashin aminci zai zama da gangan ne kuma zai jawo halaka ta har abada. Yana da muhimmanci yanzu mu koyi yin biyayya da kowacce koyarwa da Jehovah yake yi mana, ko ta wurin Kalmarsa ko kuma ta ƙungiyarsa! A yin haka, muna nuna ibadarmu ta gaske gare shi wanda shi ne Mamallakin Dukan Halitta.
Maimaita Abin da Aka Tattauna
• Menene babban al’amari da dukanmu dole ne mu fuskanta? Ta yaya ya shafe mu?
• Menene abu na musamman game da hanyoyi da maza da matan zamanin dā suka tabbatar da amincinsu ga Jehovah?
• Me ya sa ya kamata mu daraja Jehovah ta halinmu kowacce rana?