Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 11/15 pp. 24-28
  • Jehobah Ubangijinmu Ne Maɗaukaki!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ubangijinmu Ne Maɗaukaki!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Fannonin Wasan Kwaikwayon
  • Yadda Wasan ya Soma
  • Sakamakon Tabbatacce Ne
  • Za Mu Iya Kasancewa da Aminci
  • Ka Goyi Bayan Sarautar Jehobah!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Al’amari da Dukanmu Dole Mu Fuskanta
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Ka Mai da Hankali ga Batun da Ya Fi Muhimmanci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Me Ya Sa Za Ka Yi Nagarta?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 11/15 pp. 24-28

Jehobah Ubangijinmu Ne Maɗaukaki!

“Ubangiji Maɗaukaki . . . babban sarki ne bisa dukan duniya.”—ZAB. 47:2.

1. Bisa kalamansa da ke rubuce a 1 Korintiyawa 7:31, Bulus yana nuni ne ga mene ne?

“GAMA ƙa’idar duniyan nan tana shuɗewa.” Hakan manzo Bulus ya ce. (1 Kor. 7:31) Kamar dai yana kwatanta duniya da fagen wasa, inda ’yan wasa da suke fagen wasa suke fitowa su yi nasu wasa a matsayin masu halin kirki ko kuma mugun hali har sai an sake fitowar wasan.

2, 3. (a) Da me za a iya kwatanta ƙalubale ga ikon mallaka na Jehobah? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?

2 A yau, yanayin da za a iya kwatanta da wasan kwaikwayo mafi muhimmanci yana faruwa, kuma ta shafe ku! Kuma musamman ta ƙunshi kunita ikon mallaka na Jehobah Allah. Za a iya kwatanta wannan wasan kwaikwayon da yanayi da zai iya kasancewa a wata ƙasa. A wata sassa kuma, akwai wata sarauta da aka amince da ita da take riƙe ƙa’ida. Kuma, akwai wata ƙungiya mai aikata laifi da wanda ke sarautarta munafuki ne da mai son yin faɗa da kuma mai kisa. Ƙungiya da take ƙetare doka ƙalubale ne ga sarautar ikon mallaka kuma gwaji ne ga amincin duk ’yan ƙasan wannan gwamnatin.

3 Irin wannan yanayin ya kasance a sararin samaniya. Gwamnati da aka amince da ita na “Ubangiji Yahweh” tana wanzuwa. (Zab. 71:5) Amma yanzu ’yan Adam suna ƙarƙashin ƙungiyar da shugabansu “Shaitan” ne. (1 Yoh. 5:19) Wannan ta ƙalubalanci gwamnatin Allah da aka amince da ita kuma ta gwada amincin dukan mutane ga ikon mallaka na sarautarsa. Mene ne ya jawo wannan yanayin? Me ya sa Jehobah ya ƙyale hakan? Mene ne ɗaɗɗayan mu za mu iya yi?

Fannonin Wasan Kwaikwayon

4. Wasa na sararin samaniya da ake yi ya ƙunshi waɗanne batutuwa biyu da suke da nasaba da juna?

4 Wannan wasa na sararin samaniya da ake yi ya ƙunshi batutuwa biyu da suke da nasaba da juna: Wato ikon mallakar Jehobah da aminci na ’yan Adam. A cikin Nassosi, an kira Jehobah “Ubangiji Maɗaukaki.” Alal misali, marubucin wannan zabura ya rera: “Ubangiji Maɗaukaki. . . . Babban Sarki ne bisa dukan duniya.” (Zab. 47:2) “Maɗaukaki” shi ne mafificin iko ko kuma sarauta. Mamallaki yana nuna iko mafifici. Da akwai dalilai masu kyau na ɗaukan Jehobah Allah a matsayin Mai Iko Mafifici.—Dan. 7:22.

5. Me zai sa mu mu ɗaukaka ikon mallakar Jehobah?

5 A matsayin Mahalicci, Jehobah ne Mamallakin duniya da dukan sararin samaniya. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 4:11.) Jehobah kuma Mai Mulkinmu ne, Mai Shari’armu da kuma Sarki. (Isha. 33:22) Tun da yake Allah ne ya sa muke wanzuwa kuma mun dogara gare shi, ya kamata mu ɗauke shi a matsayin Ubangijinmu Mai-Ikon Mallaka. Idan a koyaushe muna tuna cewa “Ubangiji ya kafa kursiyinsa a cikin sammai; Mulkinsa kuwa yana bisa kowa” hakan zai sa mu mu ɗaukaka matsayinsa mai girma.—Zab. 103:19; A. M. 4:24.

6. Mene ne aminci?

6 Don mu tallafa wa ikon mallakar Jehobah, dole ne mu kasance da amincinmu a gare shi. “Aminci” ɗabi’a ce mai kyau ko cikakkiya. Mai aminci kamili ne mai adalci. Ayuba uban iyali, irin wannan mutumi ne.—Ayu. 1:1.

Yadda Wasan ya Soma

7, 8. Ta yaya Shaiɗan ya ƙalubalanci ikon mallakar Jehobah?

7 Fiye da shekaru 6,000 da suka shige, wani halittar ruhu ya ƙalubalanci ikon mallakar Jehobah. Sha’awar son kai, na son a bauta masa ne ya motsa wannan ɗan tawaye ya furta kalaman da ya yi da ayyukansa. Ya rinjaye mutane na farko, Adamu da Hauwa’u su yi rashin aminci ga ikon mallakar Allah kuma ya yi ƙoƙari ya ɓata sunan Jehobah ta wajen yin da’awa cewa Jehobah ya yi ƙarya. (Karanta Farawa 3:1-5.) Ɗan tawayen ya zama babban Magabci, Shaiɗan (Mai yin tsayayya), Iblis (Mai tsegumi), maciji (mai yaudara), da kuma babban maciji (mai halakarwa).—R. Yoh. 12:9.

8 Shaiɗan ya sa kansa ya zama masarauci abokin hamayya. Mene ne Ubangiji Jehobah Mai Ikon Mallaka zai yi don wannan ƙalubale? Zai halaka waɗannan ’yan tawaye gudu uku, Shaiɗan, Adamu da Hauwa’u nan da nan ne? Babu shakka, yana da ikon yin hakan, kuma da a ce ya ɗauki irin wannan matakin da ya magance tuhuma na wanda ya fi iko. Da ya nuna cewa Jehobah ne ya faɗi gaskiya game da horon karya dokarsa. Me ya sa Allah bai ɗauka irin wannan matakin ba?

9. Mene ne Shaiɗan ya tuhumi?

9 Ta wajen yin ƙarya da kuma sa Adamu da Hauwa’u su juya wa Allah baya, Shaiɗan ya tuhumi ikon Jehobah na bukatar ’yan Adamu su yi masa biyayya. Bugu da ƙari, ta wajen rinjayar mutane biyu na farko su yi rashin biyayya ga Allah, Shaiɗan ya tuhumi amincin dukan halittu masu basira. Kamar yadda batun Ayuba wanda ya kasance da aminci ga ikon mallakar Jehobah ya nuna, Shaiɗan ya yi da’awa cewa zai iya juya dukan ’yan Adam daga wurin Allah.—Ayu. 2:1-5.

10. Da yake bai halaka ɗan tawayen nan da nan ba don ya nuna ikon mallakarsa, mene ne Allah ya ƙyale?

10 Da yake bai halaka ɗan tawayen nan da nan ba don ya nuna ikon mallakarsa, Jehobah ya ba Shaiɗan lokaci ya tabbatar da da’awarsa. Allah kuma ya ba ’yan Adam zarafin nuna amincinsu ga ikon mallakarsa. Mene ne ya faru da shigewar ƙarnuka? Shaiɗan ya kafa muguwar ƙungiya ta masu aikata laifi. Daga baya Jehobah zai halaka ƙungiyar da kuma Iblis, hakan zai ba da tabbaci sosai na ikon mallakar Allah. Jehobah Allah ya kasance da tabbaci sosai cewa sakamakon zai zama mai kyau har ya annabta hakan a lokacin da tawayen ya faru a cikin Adnin.—Far. 3:15.

11. Mene ne ’yan Adam da yawa suka yi game da ikon mallakar Jehobah?

11 ’Yan Adam da yawa sun nuna bangaskiya kuma sun kasance da aminci ga ikon mallakar Jehobah da kuma tsarkaka sunansa. Wannan rukunin ya ƙunshi Habila da Anuhu da Nuhu da Ibrahim da Saratu da Musa da Ruth, da almajirai na farko na Kristi, da kuma masu aminci da yawa a yau. Irin waɗannan da suka ɗaukaka ikon mallaka na Allah sun sa hannu wajen nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne kuma sun kawar da zargi da Iblis ya ɗora wa sunan Jehobah ta wajen yin fahariya cewa zai iya sa dukan ’yan Adam su daina bauta wa Allah.—Mis. 27:11.

Sakamakon Tabbatacce Ne

12. Ta yaya za mu kasance da tabbaci cewa Allah ba zai ƙyale mugunta har abada ba?

12 Muna da tabbaci cewa ba da daɗewa ba Jehobah zai nuna ikon mallakarsa. Ba zai ƙyale mugunta har abada ba kuma mun san cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe. Jehobah ya kawar da miyagu a lokacin Rigyawa. Ya halaka Saduma da Gwamrata da Fir’auna da rundunarsa. Sisera da rundunarsa da Sennakerib da rundunarsa ’yan Assuriya ba su yi nasara a kan Maɗaukakin Sarki ba. (Far. 7:1, 23; 19:24, 25; Fit. 14:30, 31; Alƙa. 4:15, 16; 2 Sar. 19:35, 36) Saboda haka, muna da tabbaci cewa Jehobah Allah ba zai ci gaba da ƙyale rashin biyayya ga sunansa da kuma wulakanci da ake wa Shaidunsa ba. Bugu da ƙari, yanzu muna ganin tabbacin alamar bayanuwar Yesu da kuma cikawar wannan mugun zamani.—Mat. 24:3.

13. Ta yaya za mu tsira don kada a halaka mu tare da magabtan Jehobah?

13 Don kada a halaka mu tare da magabtan Allah, dole ne mu kasance da aminci ga ikon mallakar Jehobah. Ta yaya za mu iya yin hakan? Ta wurin ware kanmu daga mugun sarautar Shaiɗan da kuma ƙin mabiyansa su tsoratar da mu. (Isha. 52:11; Yoh. 17:16; A. M. 5:29) Sai a cikin irin wannan yanayi ne kaɗai za mu iya ɗaukaka ikon mallakar Ubanmu na samaniya kuma mu kasance da bege cewa za mu tsira sa’ad da Jehobah zai kawar da zargi da aka yi wa sunansa kuma ya nuna cewa shi ne Mamallakin Dukan Halitta.

14. Mene ne aka bayyana a surori dabam dabam na Littafi Mai Tsarki?

14 An ba da bayani dalla-dalla game da ’yan Adam da ikon mallakar Jehobah a cikin Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya. Surori uku na farko sun gaya mana game da halitta da kuma yadda ’yan Adam suka faɗa cikin zunubi, amma kuma surori uku na ƙarshe sun faɗa yadda ’yan Adam suka farfaɗo. Sauran surorin sun faɗa dalla-dalla matakan da Ubangiji Jehobah Mai-Ikon Mallaka ya ɗauka don ya cim ma nufinsa ga ’yan Adam da duniya da kuma sararin samaniya. Littafin Farawa ya nuna yadda Shaiɗan da mugunta suka shigo duniya, kuma sashen ƙarshe na Littafin Ru’ya ta Yohanna ya bayyana yadda za a kawar da mugunta da yadda za a halaka Iblis da kuma yadda za a yi nufin Allah a duniya kamar yadda ake yi a sama. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da ya kawo zunubi da mutuwa kuma ya nuna yadda za a kawar da su daga duniya kuma a sauya su da farin ciki marar iyaka da rai madawwami na masu aminci.

15. Don mu amfana sa’ad da wasan kwaikwayon da ya ƙunshi ikon mallaka ya zo ƙarshensa, mene ne ya wajaba mu yi?

15 Ba da daɗewa ba yanayin wannan duniyar zai canja gabaki ɗaya. Wasan kwaikwayon da ya ƙunshi ikon mallaka zai zo ƙarshensa. Za a cire Shaiɗan daga fagen a kuma halaka shi, kuma nufin Allah zai kasance. Amma don mu amfana daga wannan kuma mu more albarkatu masu yawa da aka annabta cikin Kalmar Allah, dole ne mu ɗaukaka ikon mallakar Jehobah yanzu. Dole ne mu zaɓi wanda za mu bi. Don mu iya faɗa cewa: “Ubangiji yana wajena,” dole ne mu goyi bayansa.—Zab. 118:6, 7.

Za Mu Iya Kasancewa da Aminci

16. Me ya sa za mu kasance da tabbaci cewa zai yiwu ’yan Adam su kasance da aminci ga Allah?

16 Za mu iya ɗaukaka ikon mallakar Jehobah kuma mu kasance da aminci, gama manzo Bulus ya rubuta: “Babu wata jaraba ta same ku sai irin da mutum ya iya jimrewa: amma Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi muku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi muku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.” (1 Kor. 10:13) Mene ne tushen jaraba da Bulus ya ambata, kuma yaya Allah ya yi mana hanyar tsira?

17-19. (a) Isra’ilawa sun faɗa wa wane gwaji a cikin jeji? (b) Me ya sa zai yiwu mu kasance da aminci ga Jehobah?

17 Kamar yadda aka kwatanta daga abubuwa da Isra’ila ta fuskanta a cikin jeji, muna fuskantar “jaraba” ta wurin yanayi da zai sa mu karya dokar Allah. (Karanta 1 Korintiyawa 10:6-10.) Da Isra’ilawa za su tsayayya wa jaraba, amma sun yi kwaɗayin “miyagun abu” sa’ad da Jehobah ta mu’ujiza ya yi musu tanadin makwarwa na wata guda. Ko da yake mutanen ba su ci nama ba na ɗan lokaci, amma Allah ya ba su isashen manna da suka ci. Duk da haka sun faɗa wa jarabar haɗama sa’ad da suke tara makwaren.—Lit. Lis. 11:19, 20, 31-35.

18 Da farko, sa’ad da Musa yake karɓan Dokar a kan Dutsen Sinai, Isra’ilawa sun zama masu bautar gunki, sun sa hannu a bautar maraƙi da jin daɗi na jiki. Da yake Musa shugabansu na zahiri ba ya nan sai suka faɗa wa gwajin. (Fit. 32:1, 6) Ba da daɗewa ba kafin su shiga Ƙasar Alkawari, matan Mowab suka rinjayi Isra’ilawa dubbai kuma suka yi lalata da su. A wannan lokacin, dubban Isra’ilawa sun mutu don zunubansu. (Lit. Lis. 25:1, 9) A wasu lokatai, sun faɗa wa gwajin yin gunaguni cikin tawaye, a wani lokaci kuma sun yi gunaguni game da Musa da kuma Allah! (Lit. Lis. 21:5) Mutanen Isra’ila sun ma yi gunaguni bayan an halakar da mugaye Kora da Datan da Abiram da abokansu, suna tunani cewa yadda aka kashe ’yan tawayen ba daidai ba ne. Saboda haka, Isra’ilawa 14,700 sun mutu don annoba da Allah ya aika.—Lit. Lis. 16:41, 49.

19 Babu gwaji da aka ambata ɗazu da Isra’ilawa ba za su iya tsayayya musu ba. Mutanen sun faɗa wa gwaji domin sun yi rashin bangaskiyarsu kuma sun manta da Jehobah, yadda ya kula da su, da kuma dacewar hanyoyinsa. Kamar yadda yake a batun Isra’ilawa, gwajin da muke fuskanta wanda ’yan Adam suka saba fuskanta ne. Idan muka yi ƙoƙari mu tsayayya musu kuma muka dogara ga Allah don ya kiyaye mu, za mu iya kasancewa da aminci. Za mu iya kasancewa da tabbaci game da wannan domin “Allah mai-aminci” ne kuma ba ya ƙyale a yi mana ‘jaraba wadda ta fi ƙarfinmu.’ Jehobah ba zai taɓa ƙyale mu har ya yarda mu faɗa cikin yanayi da zai sa ba zai yiwu ba mu yi nufinsa.—Zab. 94:14.

20, 21. Idan aka gwada mu, yaya Allah yake mana “hanyar tsira”?

20 Jehobah yana mana “hanyar tsira” ta wajen ƙarfafa mu mu tsayayya wa gwaji. Alal misali, ’yan hamayya suna iya zalunta mu a zahiri don su sa mu bar bangaskiyarmu. Irin wannan wulakanci yana iya sa mu yasar da bangaskiyarmu don kada a daɗa yi mana dūka da azaba ko kuma a kashe mu. Amma, bisa hurarren tabbacin da Bulus ya ba da da ke rubuce a 1 Korintiyawa 10:13, mun san cewa yanayi da ke kawo gwaji na ɗan lokaci ne kawai. Jehobah ba zai bar gwajin ya kai har da ba za mu iya kasancewa da aminci a gare shi kuma ba. Allah zai iya ƙarfafa bangaskiyarmu kuma ya ba mu ƙarfi na ruhaniya da muke bukata don mu kasance da aminci.

21 Jehobah yana kiyaye mu ta wajen ruhunsa mai tsarki. Wannan ruhun yana tuna mana koyarwa na Nassi da muke bukata don mu tsayayya wa gwaji. (Yoh. 14:26) Saboda haka, ba a yaudararmu mu bi mugun tafarki. Alal misali, mun fahimci batutuwa da suke da nasaba da ikon mallakar Jehobah da kuma muhimmancin riƙe amincinmu. Tun da yake suna da wannan sani, Allah ya kiyaye mutane da yawa su kasance da aminci har mutuwa. Amma ba mutuwa ba ce ta sa suka tsira daga gwajin, taimakon Jehobah ne ya sa ya yiwu su jimre har ƙarshe ba tare da faɗa wa gwaji ba. Zai iya yi mana hakan. Hakika ya kuma yi amfani da mala’ikunsa masu aminci a madadinmu a matsayin bayi masu hidima “aikakku domin su yi hidima sabili da waɗanda za su gaji ceto.” (Ibran. 1:14) Kamar yadda talifi na gaba ya nuna, masu aminci ne kaɗai za su iya kasancewa da begen samun gata na farin ciki don ɗaukaka ikon mallakar Allah har abada. Muna iya kasancewa cikinsu idan muka manne wa Jehobah a matsayin Ubangijinmu Mai Ikon Mallaka.

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa za mu amince da Jehobah a matsayin Ubangijinmu Mai Ikon Mallaka?

• Mene ne yake nufi mu kasance da aminci ga Allah?

• Yaya muka sani cewa ba da daɗewa ba Jehobah zai nuna ikon mallakarsa?

• Bisa ga 1 Korintiyawa 10:13, me ya sa zai yiwu mu kasance da aminci?

[Hoton da ke shafi na 24]

Shaiɗan ya yaudari Adamu da Hauwa’u su yi rashin aminci ga Jehobah

[Hoton da ke shafi na 26]

Ka ƙuduri aniya ka ɗaukaka ikon mallakar Jehobah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba