Me Ya Sa Za Ka Yi Nagarta?
“Ya Ubangiji, ka yi mani shari’a . . . gwalgwadon nagarta da ke gareni.”—Zab. 7:8.
1, 2. Waɗanne yanayi ne suke kawo ƙalubale ga nagartar Kirista?
KA YI tunanin waɗannan yanayin guda uku: Abokan makaranta wani yaro suna yi masa ba’a. Suna ƙoƙarin su sa shi ya yi fushi, wataƙila don ya yi zagi ko kuma faɗa. Zai rama ne, ko kuwa zai kame kansa kuma ya yi tafiyarsa? Wani miji yana gida shi kaɗai kuma yana yin wasu bincike a cikin Intane. Wani dandali ya fito a kan kwamfutarsa da ya gabatar da Duniyar gizo da ake lalata. Zai faɗa wa jarrabar kuma ya buɗe dandalin, ko kuma zai guje masa? Wata ’yar’uwa Kirista tana taɗi da wasu ’yan’uwa mata, sai taɗin ya koma muguwar gulma game da wata ’yar’uwa a cikin ikilisiya. Za ta sa baki a gulmar ce ko kuma za ta yi ƙoƙari ta canja batun?
2 Ko da yake waɗannan yanayi sun bambanta, suna da abu iri ɗaya. Dukansu sun ƙunshi famar yin nagarta a matsayin Kirista. Kana tunanin nagartarka sa’ad da kake fuskantar damuwarka, bukatunka, da makasudinka a rayuwa? A kowace rana, mutane suna tunanin siffarsu, lafiyar jikinsu, ƙalubalen biyan bukatun rayuwa, lokacin farin ciki da baƙin ciki na abokantaka, wataƙila har da dangantaka ta soyayya. Muna iya mai da wa irin waɗannan damuwar hankalinmu. Amma, menene ya fi muhimmanci ga Jehobah sa’ad da yake bincika zuciyarmu? (Zab. 139:23, 24) Yin nagarta ne.
3. Wane gata ne Jehobah ya ba mu, menene za mu tattauna a wannan talifin?
3 Jehobah mai ba da “kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta,” ya ba kowannenmu kyauta dabam dabam. (Yaƙ. 1:17) Godiya ta tabbata gare shi da yake ya ba mu kyautar jiki, zuciya, lafiyar jiki da baiwa dabam dabam. (1 Kor. 4:7) Duk da haka, Jehobah ba ya tilasta mana mu yi nagarta. Ya bar mu mu zaɓi ko za mu kasance da wannan halin. (K. Sha 30:19) Saboda haka, muna bukatar mu bincika ko mecece nagarta. Za mu kuma bincika dalilai uku da suka nuna abin da ya sa wannan halin yake da muhimmanci sosai.
Mecece Nagarta?
4. Menene nagarta ta ƙunsa, kuma menene za mu iya koya daga dokar Jehobah game da hadayun dabbobi?
4 Mutane da yawa ba su da cikakken fahimi game da abin da nagarta take nufi. Alal misali, sa’ad da ’yan siyasa suke fahariya cewa sun yi nagarta, sau da yawa suna nufin gaskiya. Hakan yana da muhimmanci, amma sashe ne kawai na nagarta. Kamar yadda aka yi amfani da shi cikin Littafi Mai Tsarki, nagarta ta ƙunshi cikakkiyar ɗabi’a mai kyau. An samo kalmomin Ibrananci da suke da nasaba da “nagarta” daga kalmar da ke nufin lafiyayye, cikakke, ko kuma marar aibi. An yi amfani da ɗaya cikin waɗannan kalmomin game da hadayu da za a miƙa wa Jehobah. Yana amincewa da dabbar da aka yi hadaya da ita idan lafiyayya ce, ko kuma cikakkiya. (Karanta Leviticus 22:19, 20.) Jehobah ya ƙi karɓan hadayar waɗanda suka ƙi yin biyayya da umurninsa ta wajen miƙa dabbobi naƙasassu, marasa lafiya, ko kuma makafi.—Mal. 1:6-8.
5, 6. (a) Waɗanne misalai ne suka nuna cewa sau da yawa muna son cikakken abu? (b) Idan ya zo ga batun ’yan adam ajizai, nagarta tana nufin kamilta ne? Ka yi bayani.
5 Ra’ayin biɗa da kuma daraja cikakken abu, ba sabo ba ne. Alal misali, ka yi tunanin mutum mai adana littattafai wanda ya samu wani littafi mai tamani da yake nema da daɗewa, amma sai ya ga cewa babu shafuffuka da yawa masu muhimmanci a cikin littafin. Domin hakan ya ɓata masa rai, yana iya mai da littafin cikin kanta. Ko kuma ka yi tunanin matar da ta je sayen ƙwai a kasuwa. Wannene za ta zaɓa? Waɗanda ba su fashe ba, wato, cikakku. Hakazalika, Allah yana son mutanen da suke bauta masa da dukan zuciyarsu.—2 Laba. 16:9.
6 Amma, kana iya yin mamaki ko muna bukatar mu zama kamiltattu idan za mu kasance masu nagarta. Domin zunubinmu da ajizancinmu, muna iya ganin cewa mu ba cikakku ba ne kamar littafin da wasu shafuffuka suka ɓace ko kuma kamar ƙwan da ya fashe. Kana jin hakan a wani lokaci? Ka tabbata cewa Jehobah ba ya bukatar mu zama kamiltattu. Ba ya bukatar mu yi abin da ba za mu iya ba.a (Zab. 103:14; Yaƙ. 3:2) Duk da haka, yana son mu ci gaba da yin nagarta. Saboda haka, da akwai bambanci ne tsakanin kamilta da nagarta? E. Alal misali: Wani saurayi yana ƙaunar wata budurwa da yake son ya aura. Ba zai sa rai cewa za ta zama kamiltacciya ba. Duk da haka, zai sa rai cewa za ta so shi da dukan zuciyarta, wato, ta so shi shi kaɗai. Hakanan ma, Jehobah “Allah mai-kishi ne.” (Fit. 20:5) Yana son mu ƙaunace shi da dukan zuciyarmu kuma mu bauta masa shi kaɗai, ba wai mu zama kamiltattu ba.
7, 8. (a) Wane misali ne Yesu ya kafa game da nagarta? (b) Menene ainihi nagarta take nufi bisa ga Nassi?
7 Yana da kyau mu tuna amsar da Yesu ya ba da sa’ad da aka tambaye shi dokar da ta fi muhimmanci a cikin dukan dokoki. (Karanta Markus 12:28-30.) Yesu ya yi rayuwar da ta jitu da amsar da ya bayar. Ya kafa misali mafi kyau wajen ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsa, ransa, da kuma ƙarfinsa. Ya nuna cewa ana yin nagarta ne ta ayyuka da aka yi da muradi mai kyau. Muna bukatar mu bi sawun Yesu idan muna son mu ci gaba da yin nagarta.—1 Bit. 2:21.
8 Ga ma’anar yin nagarta bisa ga Nassi: bauta wa Jehobah Allah na samaniya da dukan zuciyarmu, da kuma nufinsa da ya furta. Yin nagarta yana nufin cewa a rayuwarmu ta yau da kullum, za mu nemi mu faranta wa Jehobah Allah rai fiye da kome. Abubuwa da suka fi muhimmanci a gare shi, za su zama mafi muhimmanci a gare mu. Bari mu tattauna dalilai uku da ya sa hakan yake da muhimmanci sosai.
1. Amincinmu da Batun Ikon Mallaka
9. Ta yaya nagartarmu take da nasaba da batun ikon mallakar sararin samaniya?
9 Ikon mallakar Jehobah bai dangana da nagartarmu ba. Ikonsa ba ya son kai, na har abada ne, kuma a dukan duniya. Hakan zai ci gaba da kasancewa ko da menene kowane halitta ya ce ko kuma ya yi. Amma, an tsegunta ikon mallakar Allah sosai a sama da kuma duniya. Saboda haka, ya kamata a ƙunita sarautarsa, kuma a tabbatar wa dukan halittu masu basira cewa sarautarsa ce mafi dacewa, mafi adalci, kuma mai ƙauna. A matsayinmu na Shaidun Jehobah, muna son mu tattauna batun ikon mallakar Allah na sararin samaniya da duk mutumin da yake son ya saurara. Amma, ta yaya za mu yi zaɓi kuma mu yi abubuwan da suka jitu da ikonsa? Ta yaya za mu nuna cewa mun zaɓi Jehobah a matsayin Mai mallakarmu? Ta wajen yin nagarta.
10. Wace da’awa ce Shaiɗan ya yi game da amincin ’yan adam, kuma menene za ka so ka yi?
10 Ka yi la’akari da yadda hakan ya shafi nagartarka. Shaiɗan ya yi da’awar cewa babu ɗan adam da zai goyi bayan ikon mallakar Allah, cewa babu wanda zai bauta wa Jehobah ba tare da son kai ba. A gaban taro mai girma na halittun ruhu, Iblis ya gaya wa Jehobah: “Fata a bakin fata, hakika dukan abin da mutum ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa.” (Ayu. 2:4) Ka lura cewa Shaiɗan ba ya maganar Ayuba kawai amma dukan ’yan adam. Ya yi daidai da Littafi Mai Tsarki ya kira Shaiɗan “mai-saran ’yan’uwanmu.” (R. Yoh. 12:10) Ya gaya wa Jehobah cewa Kiristoci, har da kai, ba za su kasance da aminci ba. Shaiɗan ya yi da’awa cewa za ka ci amanar Jehobah don ka ceci ranka. Yaya kake ji game da wannan tuhuma da aka yi maka? Ba za ka nemi zarafin ƙaryata Shaiɗan ba? Ta wajen kasancewa da aminci, za ka iya yin hakan.
11, 12. (a) Waɗanne misalai ne suka nuna yadda shawarwarin da muke yi a rayuwarmu ta yau da kullum suka shafi batun yin nagarta? (b) Me ya sa gata ne yin nagarta?
11 Saboda haka, batun amincinka ya sa halinka da zaɓinka na yau da kullum su kasance da muhimmanci. Ka yi la’akari kuma da yanayi uku da aka ambata ɗazu. Ta yaya za su nuna nagarta? Yaron da abokan makarantarsa suke zagi ya ji kamar ya rama, amma sai ya tuna wannan gargaɗin: “Kada ku ɗauka ma kanku fansa, ƙaunatattu, amma ku kauce ma fushi: gama an rubuta, ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji.” (Rom. 12:19) Sai ya yi tafiyarsa. Mijin da yake amfani da Intane yana iya kallon abin da zai ta da sha’awar jima’i, amma sai ya tuna mizanin da ke cikin kalmomin Ayuba: “Na yi wa’adi da idanuna; yaya fa zan yi sha’awar budurwa?” (Ayu. 31:1) Hakazalika, mutumin ya ƙi ya kalli hotunan batsa, ya guji hotunan kamar yadda zai guje wa guba. Matar da take taɗi tare da ’yan’uwa mata inda za ta iya jin muguwar gulma ta ƙi ta sa baki da ta tuna umurnin nan: “Bari kowannenmu shi gami ɗan’uwansa wajen abin da ke nagari, zuwa ginawa.” (Rom. 15:2) Gulmar da za ta maimaita ba mai ginawa ba ce. Zai ɓata sunan ’yar’uwarta Kirista, kuma ba zai faranta wa Ubanta na samaniya rai ba. Saboda haka, ta ƙi sa baki kuma ta canja batun.
12 A kowane cikin waɗannan yanayi, Kiristocin sun yi zaɓin da ya nuna kamar suna cewa: ‘Jehobah ne Sarkina. Zan yi ƙoƙari na yi abin da yake so a wannan batun.’ Sa’ad da kake yin zaɓi da yanke shawarwari, kana ƙoƙarin faranta wa Jehobah rai kuwa? Idan haka ne, kana yin biyayya ga kalmomi masu daɗaɗa rai da ke rubuce a Misalai 27:11 “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.” Muna da gata mai girma na faranta wa Allah rai! Kwalliya za ta biya kuɗin sabulu idan muka yi nagarta. Ko ba haka ba?
2. Tushen Hukunci na Allah
13. Ta yaya ne kalaman Ayuba da na Dauda suka nuna cewa nagarta ce tushen hukuncin da Jehobah yake yi mana?
13 Mun ga cewa nagarta tana sa mu goyi bayan ikon mallaka na Jehobah. Ita ce tushen hukuncin da Allah zai iya yi mana. Ayuba ya fahimci wannan gaskiyar sosai. (Ayuba 31:6, Littafi Mai Tsarki.) Ayuba ya san cewa Allah yana auna dukan mutane cikin “ma’aunin da ke daidai,” ta wajen yin amfani da cikakken mizaninsa na adalci ya auna nagartarmu. Dauda ma ya faɗi hakan: “Ubangiji yana hukumta ma dangogi shari’a: Ya Ubangiji, ka yi mani shari’a gwalgwadon adilcina, gwalgwadon nagarta da ke gareni kuma. . . . Gama Allah mai-adilci yana auna zuciya da ciki.” (Zab. 7:8, 9) Mun san cewa Allah yana iya bincika mutuminmu na ciki, wato, ‘zuciyarmu da cikinmu’ na alama. Muna bukatar mu tuna ainihin abin da yake bincikawa. Kamar yadda Dauda ya ce, Jehobah yana yi mana hukunci ne bisa ga nagartarmu.
14. Me ya sa bai kamata mu taɓa tsammanin cewa yanayinmu na ajizai masu zunubi zai iya hana mu yin nagarta?
14 A ce Jehobah Allah yana bincika zukatan biliyoyin mutane a yau. (1 Laba. 28:9) Sau nawa yake samun mutumin da yake yin nagarta ta Kirista? Hakan yana da wuya! Amma, kada mu yi tsammanin cewa ajizancinmu zai hana mu yin nagarta. Akasin haka, kamar Dauda da Ayuba, muna da dalili mai kyau na kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai same mu muna yin nagarta, duk da cewa mu ajizai ne. Ka tuna cewa, kamilta ba ta nufin cewa za mu yi nagarta. Kamiltattun mutane uku ne kawai suka taɓa rayuwa a wannan duniyar, biyu daga cikinsu, Adamu da Hauwa’u, sun ƙi kasancewa da aminci. Duk da haka, miliyoyin mutane ajizai sun yi nasara. Kai ma za ka iya.
3. Tana da Muhimmanci ga Begenmu
15. Ta yaya ne Dauda ya nuna cewa yin nagarta yana da muhimmanci domin begenmu na nan gaba?
15 Domin nagarta ce tushen hukuncin da Jehobah yake yi mana, tana da muhimmanci ga begenmu na nan gaba. Dauda ya san cewa hakan gaskiya ne. (Karanta Zabura 41:12.) Yana sha’awar begen samun kulawar Allah har abada. Kamar Kiristoci na gaskiya a yau, Dauda yana da begen yin rayuwa har abada, kuma ya ci gaba da kusantar Jehobah Allah sa’ad da yake bauta masa. Dauda ya fahimci cewa yana bukatar ya yi nagarta idan yana son ya ga cikar wannan begen. Hakazalika, Jehobah yana taimaka mana, yana koyar da mu, yana yi mana ja-gora, kuma yana yi mana albarka yayin da muke yin nagarta.
16, 17. (a) Me ya sa ka kudurta cewa za ka riƙa yin nagarta a kowane lokaci? (b) Waɗanne tambayoyi ne talifi na gaba zai tattauna?
16 Muna bukatar mu kasance da bege idan muna son mu yi farin ciki. Bege na iya ba mu farin cikin da muke bukata don mu jimre wahala. Bege yana iya kāre tunaninmu. Ka tuna, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta bege da kwalkwali. (1 Tas. 5:8) Kamar yadda kwalkwali yake kāre kan sojan da ke bakin daga, bege yana kāre mu daga yin tunani marar kyau da Shaiɗan yake ɗaukakawa a wannan duniyar da za ta shuɗe. Rayuwa ba ta da ma’ana idan ba mu da bege. Muna bukatar mu bincika kanmu da gaske, mu bincika yanayin nagartarmu da kuma begenmu. Kada ka mance cewa idan kana yin nagarta, kana ɗaukaka ikon mallakar Jehobah kuma kana kāre begenka mai kyau na nan gaba. Bari ka riƙa yin nagarta a kowane lokaci!
17 Tun da yake yin nagarta yana da muhimmanci sosai, muna bukatar mu ƙara bincika wasu tambayoyi. Ta yaya za mu iya zama masu nagarta? Ta yaya za mu iya ci gaba da nuna ta? Kuma menene za a yi idan mutum ya daina yin nagarta? Talifi na gaba zai tatattauna waɗannan tambayoyin.
[Hasiya]
a Yesu ya ce: “Ku fa za ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama cikakke ne.” (Mat. 5:48) Babu shakka, ya fahimci cewa ’yan adam ajizai za su iya zama cikakku, ko kamiltattu amma ba gabaki ɗaya ba. Za mu iya bin dokar da ta ce mu ƙaunaci mutane sosai, ta hakan mu faranta wa Allah rai. Amma, Jehobah, kamili ne a dukan abu. Idan aka yi amfani da kalmar nan “nagarta” game da shi hakan ya ƙunshi kamiltawa.—Zab. 18:30; LMT.
Yaya Za Ka Amsa?
• Mecece nagarta?
• Ta yaya ne nagarta ta shafi batun ikon mallaka na sararin samaniya?
• Ta yaya ne nagarta ta zama tushen begenmu?
[Hotuna a shafi na 5]
Rayuwa ta yau da kullum tana sa mu fuskanci ƙalubale masu yawa da za su iya shafan nagartarmu