Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 11/15 pp. 28-32
  • Za Mu Yi Tafiya Cikin Gaskiyarmu!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Mu Yi Tafiya Cikin Gaskiyarmu!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tarbiyya Tana da Muhimmanci
  • Kada Ka Kuskura Ka Yi Cuku-Cuku
  • Ka Kafa Misali Mai Kyau Wajen Yin Sha’ani da Mutane
  • Ka Zama Mai Karimci, ba Mai Ƙyashi Ba
  • Ka Manne wa Bauta ta Gaskiya
  • Kada Ka Zama Mai Ramako ko Munafuki
  • Mai Aminci Ya Fuskanci Gwaji
  • Za Ka Iya Kasancewa da Aminci
  • Ka Rike Amincinka!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Ba Zan Daina Tsare Mutuncina Ba!”
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Darussa Daga Littafin Ayuba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 11/15 pp. 28-32

Za Mu Yi Tafiya Cikin Gaskiyarmu!

“A cikin gaskiyata zan yi zamana.”—ZAB. 26:11.

1, 2. Mene ne Ayuba ya faɗa game da gaskiyarsa, kuma mene ne aka nuna game da shi a cikin Ayuba sura ta 31?

A ZAMANIN dā, ana gwada abubuwa ne a kan sikelin da ake ɗora kwanoni biyu a gefensa biyu. Shi wannan sikelin yana da sashe biyu. Ana ɗora abin da za a gwada ne a ɓangare guda, sai kuma a ɗaura abin da an riga a san nauyinsa a ɗayan bangaren. An bukaci mutanen Allah su yi amfani da sikeli da ma’auni masu kyau.—Mis. 11:1.

2 Sa’ad da Ayuba mutum mai tsoron Allah yake shan wahalar farmaki da Shaiɗan ya kawo masa, ya ce: “[Jehobah zai] auna ni a cikin mizanin gaskiya, domin Allah shi san sahihancina!” (Ayu. 31:6) Game da wannan, Ayuba ya ambata yanayi da yawa da za su iya sa a gwada mai aminci. Amma Ayuba ya yi nasara bisa gwajin, kamar yadda kalamansa da ke rubuce a cikin Ayuba sura 31 suka nuna. Misalinsa mai kyau zai iya motsa mu mu aikata hakan nan kuma mu furta da tabbaci yadda Dauda marubucin wannan zabura ya yi: “Amma ni, a cikin gaskiyata zan yi zamana.”—Zab. 26:11.

3. Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da aminci ga Allah a manyan batutuwa da kuma ƙanana?

3 Ko da yake an gwada Ayuba sosai, ya kasance da aminci ga Allah. Ayuba fitaccen misali ne na wanda ya kasance da aminci sa’ad da aka gwada shi sosai. Ba ma shan wahala kamar yadda Ayuba ya sha. Don mu nuna muna tafiya cikin gaskiya kuma muna goyon bayan ikon mallakar Jehobah, dole ne mu kasance da aminci a manyan batutuwa da kuma ƙanana.—Karanta Luka 16:10.

Tarbiyya Tana da Muhimmanci

4, 5. A matsayin mai aminci, wane hali ne Ayuba ya guji?

4 Don mu riƙe amincinmu ga Jehobah, dole ne mu manne wa mizanansa na ɗabi’a, kamar yadda Ayuba ya yi. Ya ce: “Na yi wa’adi da idanuna; yaya fa zan yi sha’awar budurwa? Idan zuciyata ta ruɗe da sha’awar mace, har na yi kwanto a ƙofar maƙwabcina: sai a bar matata ta yi ma wani niƙa, waɗansu kuma su yi māta da ita.”—Ayu. 31:1, 9, 10.

5 Don ya ƙuduri aniya kasancewa da aminci ga Allah, Ayuba ya guji ya kalli mace da sha’awar yin lalata da ita. A matsayin mai aure, bai yi kwarkwasa da mace da ba ta yi aure ba ko kuma soma soyayya da matar wani. A cikin Huɗuba na kan Dutse, Yesu ya yi magana mai kyau game da tarbiyya na jima’i, hakan darasi ne da masu aminci suke bukata su riƙa tunawa.—Karanta Matta 5:27, 28.

Kada Ka Kuskura Ka Yi Cuku-Cuku

6, 7. (a) Kamar yadda yake a batun Ayuba, Allah yana amfani da mene ne don ya auna amincinmu? (b) Me ya sa ba za mu yi cuku-cuku ba ko ruɗu?

6 Ba za mu yi cuku-cuku ba idan muna son a lissafa mu a cikin masu gaskiya. (Karanta Misalai 3:31-33.) Ayuba ya ce: “Idan na yi hali na ƙarya a banza, idan ƙafata ta yi garaje garin yin ha’inci; [Jehobah ya] auna ni a cikin mizanin gaskiya, domin Allah shi san sahihancina!” (Ayu. 31:5, 6) Jehobah yana auna dukan ’yan Adam a cikin “mizanin gaskiya.” Kamar yadda yake a batun Ayuba, Allah yana amfani da cikakken mizani na shari’a don ya auna amincinmu a matsayin bayinsa da suka keɓe kansu.

7 Idan muka zama masu cuku-cuku ko kuma masu ruɗu, ba za mu kasance da aminci ga Allah ba. Masu aminci sun “kakkaɓe ɓoyayyun al’amura na kunya” kuma ba sa “tafiya cikin kirsa ba.” (2 Kor. 4:1, 2) Amma idan muna cuku-cuku a kalamai ko kuma ayyukanmu, kuma don hakan muka sa ɗan’uwa mai bi ya yi roƙo ga Allah ya taimaka masa kuma fa? Hakan zai kawo mugun sakamako a gare mu! Marubucin wannan zabura ya rera: “A cikin ƙuncina na yi kuka ga Ubangiji, ya kuwa amsa mani. Ya Ubangiji, ka ceci raina daga leɓuna masu-yin ƙarya, daga harshe mai-mugunta kuma.” (Zab. 120:1, 2) Yana da kyau mu tuna cewa Allah zai iya bincika abin da muke a ciki, “yana auna zuciya da ciki” don ya san ko mu masu aminci ne na gaske.—Zab. 7:8, 9.

Ka Kafa Misali Mai Kyau Wajen Yin Sha’ani da Mutane

8. Yaya Ayuba ya bi da mutane?

8 Don mu kasance da aminci, muna bukatan mu zama kamar Ayuba, wanda ba ya son kai, mai tawali’u, da kuma mai yin la’akari da mutane. “Idan na rena ƙarar bawana, ko baiwata, Sa’anda suka yi jayayya da ni; Mi zan yi fa sa’anda Allah ya tashi tsaye? Kadan ya ziyarce ni, mi zan amsa masa? Shi wanda ya sifanta ni cikin ciki, ba shi ya yi wancan kuma? Ba shi ɗaya ne ya sifanta duka biyunmu cikin ciki ba?”—Ayu. 31:13-15.

9. Waɗanne halaye ne Ayuba ya nuna wajen yin sha’ani da bayinsa, kuma yaya ya kamata mu aikata game da wannan?

9 Hakika, babu mizani mai wuya da ake amfani da shi don gudanar da shari’a a zamanin Ayuba. Ana yin shari’a bisa ƙa’ida, kuma har bayi ma suna iya kai ƙara kotu. Ayuba ya bi da bayinsa cikin adalci da jin ƙai. Idan za mu yi tafiya cikin gaskiya, dole ne mu nuna irin waɗannan halaye, musamman idan muna hidima a matsayin dattawa a cikin ikilisiyar Kirista.

Ka Zama Mai Karimci, ba Mai Ƙyashi Ba

10, 11. (a) Yaya muka san cewa Ayuba mai karimci ne da kuma mai taimako? (b) Wane kashedin Nassi ne littafin Ayuba 31:16-25 zai iya tunasar mana?

10 Ayuba mai karimci ne da mai ba da taimako, ba mai son kai ba ko kuma mai ƙyashi. Ya ce: “Idan . . . na sa idanun gwauruwa su yi durum; ko na ci yar lomata ni kaɗai, Maraya ba ya sami abin da za ya ci a ciki ba, . . . Idan na ga kowa ya mutu sabili da rashin tufafi . . . Idan na tada hannu garin in cuci marayu, domin na ga taimakona a ƙofa: Sai a bar kafaɗata ta gulle daga allon baya, hannuna shi karye daga cikin ƙashi.” Kuma da Ayuba bai riƙe amincinsa ba idan ya gaya wa zinariya: “Ke ce abin dogara gareni.”—Ayu. 31:16-25.

11 Irin waɗannan furcin waƙa yana iya tuna mana waɗannan kalaman almajiri Yaƙub: “Addini mai-tsarki marar-ɓāci a gaban Allah Ubanmu ke nan, mutum ya ziyarci marayu da gwauraye cikin ƙuncinsu, shi tsare kansa marar-aibi daga duniya.” (Yaƙ. 1:27) Za mu iya tuna da kashedin Yesu: “Ku yi lura, ku tsare kanku daga dukan ƙyashi: gama ba da yalwar dukiya da mutum ya ke da ita ransa ke tsayawa ba.” Sai Yesu ya ba da kwatanci game da wani mutum mawadaci mai ƙyashi da ya mutu a matsayin wani da “ba mawadaci ba ne ga Allah.” (Luk 12:15-21) Don mu kasance masu riƙe aminci, kada mu faɗa wa ƙyashi na zunubi ko kuma haɗama. Ƙyashi bautar gunki ne domin abin da mai haɗama yake sha’awarsa yana janye hankalinsa daga Jehobah kuma da hakan abin ya zama gunki a gare shi. (Kol. 3:5) Ba za mu zama masu aminci kuma mu kasance masu haɗama ba.

Ka Manne wa Bauta ta Gaskiya

12, 13. Wane misali ne Ayuba ya kafa na guje wa bautar gunki?

12 Masu aminci ba sa bijirewa daga bauta mai tsarki. Ayuba bai yi haka ba, gama ya ce: “Idan na dubi rana sa’anda tana walƙiya, ko farin wata cikin tafiyassa yana sheƙi; har zuciyata ta shiga ruɗaminsu a ɓoye, bakina kuma ya yi wa hannuna sumba: Wannan kuma laifi ne da ya isa alƙalawa su hukunta: Gama da yin wannan na musunci Allah da ke bisa.”—Ayu. 31:26-28.

13 Ayuba bai bauta wa abubuwa marasa rai ba. Idan a zuciyarsa ya yi sha’awar halittu na sama, kamar su wata, kuma in bakinsa ‘ya yi wa hannunsa sumba’ wataƙila ta wurin nuna alama da hannunsa kamar yana bautar gunki, zai zama mai bautar gunki wanda ya ƙi Allah. (K. Sha 4:15, 19) Don mu kasance da aminci ga Allah, dole mu guje wa bautar gunki.—Karanta 1 Yohanna 5:21.

Kada Ka Zama Mai Ramako ko Munafuki

14. Me ya sa za mu iya faɗa cewa Ayuba ba maƙetaci ba ne?

14 Ayuba ba maƙetaci ba ne ko kuwa mai zalunci. Ya fahimci cewa irin wannan halin zai iya nuna rashin aminci, gama ya ce: “Idan na yi murna da ganin hallakar wanda ya ƙi ni; ko kuwa na ɗaukaka kaina sa’anda masifa ta same shi . . . , ban yarda bakina shi yi zunubi ba, ta wurin biɗan ransa da la’ana.”—Ayu. 31:29, 30.

15. Me ya sa bai dace ba mu yi farin ciki sa’ad da bala’i ya sami wanda ya tsane mu?

15 Ayuba adali bai taɓa yin murna sa’ad da bala’i ya faɗa wa wani da ya tsane shi ba. Wani karin magana ya ba da kashedi: “Kada ka yi farinciki lokacin da maƙiyinka ya fāɗi, kada zuciyarka kuma ta yi murna sa’anda ya kaɓantu: Domin kada Ubangiji ya gani, ya ji fushi kuma, ya juya ga barin hasalarsa a kansa.” (Mis. 24:17, 18) Tun da yake Jehobah zai iya sanin zuciya, ya san ko idan muna farin ciki da gaske game da bala’in da ya sami wani kuma ba ya amincewa da irin wannan halin. (Mis. 17:5) Allah yana iya shari’anta mu yadda ya dace, gama ya ce: “Ramawa gareni ta ke, da sakamako kuma.”—K. Sha 32:35.

16. Ta yaya za mu riƙa karɓan baƙi, ko da yake mu ba mawadata ba ne?

16 Ayuba mai karɓan baƙi ne. (Ayu. 31:31, 32) Za mu iya ‘riƙa yi wa baƙi alheri,’ ko da mu ba mawadata ba ne. (Rom. 12:13) Za mu iya raba abin da muke da shi da wasu ko da ba shi da yawa, muna tunawa cewa “gwamma a ci abinci na bakulai wurin da ƙauna ta ke, da a ci san kiwo tare da ƙiyayya.” (Mis. 15:17) Cin abinci da ɗan’uwa mai aminci a cikin ƙauna zai sa abincin ya kasance mai daɗi kuma ya amfane mu a ruhaniya.

17. Me ya sa bai kamata mu yi ƙoƙari mu ɓoye zunubi mai tsanani ba?

17 Babu shakka abin ban ƙarfafa a ruhaniya ne mutane a lokacin su more karimcin Ayuba, domin shi ba munafuki ba ne. Ba ya kamar mutane masu fajirci da suka shigo cikin ikilisiya na ƙarni na farko waɗanda suka “yi wa mutane bambaɗanci don samun wata fa’ida.” (Yahu. 3, 4, 16, Littafi Mai Tsarki) Ayuba bai kuwa ɓoye laifinsa ba ko kuma ‘ya rufe muguntarsa a ƙirjinsa,’ yana jin tsoron za a rena shi idan mutane suka sani. Yana a shirye Allah ya bincika shi, wanda zai yi wa duk wani ikirari da ake bukata. (Ayu. 31:33-37) Idan muka yi zunubi mai tsanani, kada mu yi ƙoƙari mu ɓoye irin wannan laifin don mu guji ɓata sunanmu. Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙoƙari mu kasance da aminci? Ta wajen amincewa da kuskurenmu, mu kuma tuba, mu nemi taimako na ruhaniya, da kuma yin dukan iyakar ƙoƙarinmu mu yi gyara.—Mis. 28:13; Yaƙ. 5:13-15.

Mai Aminci Ya Fuskanci Gwaji

18, 19. (a) Me ya sa za a ce Ayuba bai taɓa cuci kowa ba? (b) Mene ne Ayuba yake shirye ya yi idan aka kama shi da laifi?

18 Ayuba mai yin gaskiya ne kuma ba ya son kai. Saboda haka, ya ce: “Idan gonakina sun yi kuka game da ni, rumanyansu sun taru suna kuka; Idan na ci anfaninsu amma ban biya ba, ko kuwa na sa maabutansu suka mutu: Bari ƙayayuwa su yi girma maimakon alkama, ciyayi kuma maimakon shair.” (Ayu. 31:38-40) Ayuba bai taɓa ƙwace filin mutane ba, kuma bai cuci ma’aikata ba. Kamar Ayuba, muna bukatan mu kasance da aminci a ƙanana da kuma manya batutuwa.

19 A gaban abokansa guda uku da kuma matashi Elihu, Ayuba ya faɗa yadda ya yi rayuwarsa. Bisa ga labarin rayuwarsa wanda ke ɗauke da “saka hannunsa,” Ayuba ya gayyaci ’yan adawa su shigar da ƙara. Idan an kama Ayuba da laifi, yana shirye ya karɓi hukuncin. Shi ya sa ya miƙa ƙararsa kuma ya jira hukuncin kotun Allah. Da hakan, “maganar Ayuba ta ƙare.”—Ayu. 31:35, 40.

Za Ka Iya Kasancewa da Aminci

20, 21. (a) Me ya sa Ayuba ya iya kasancewa da aminci? (b) Ta yaya za mu iya koyon ƙaunar Allah?

20 Ayuba ya iya kasancewa da aminci domin yana ƙaunar Allah, kuma Jehobah yana ƙaunarsa kuma ya taimake shi. Ayuba ya ce: “Ka ba ni rai da alheri [ƙauna ta aminci], luran da [Jehobah ya] yi mani ya kiyayar da raina.” (Ayu. 10:12) Bugu da ƙari, Ayuba ya nuna ƙauna ga wasu, ya fahimci cewa duk wanda ya ƙi nuna ƙauna ta aminci ga ’yan’uwansa ’yan Adam zai daina tsoron Maɗaukaki Duka. (Ayu. 6:14) Masu aminci suna ƙaunar Allah da maƙwabta.—Mat. 22:37-40.

21 Muna iya koyon ƙaunar Allah ta wajen karanta Kalmarsa kullum da kuma yin bimbini a kan abin da ta bayyana game da shi. Sa’ad da muke addu’a da dukan zuciyarmu, muna iya yabon Jehobah kuma mu gode masa don nagartansa a gare mu. (Filib. 4:6, 7) Muna iya rera waƙa ga Jehobah kuma mu amfana ta wurin yin cuɗanya a kai a kai da mutanensa. (Ibran. 10:23-25) Sa’an nan ƙauna ga Allah za ta ƙaru yayin da muke sa hannu a hidimar kuma muke yin shelar “bisharar cetonsa.” (Zab. 96:1-3) A irin waɗannan hanyoyi, za mu iya kasance da aminci, kamar wannan marubucin zabura wanda ya rera: “Ya yi mani kyau in kusanci Allah: Na maida Ubangiji Yahweh mafakata.”—Zab. 73:28.

22, 23. A matsayin masu ɗaukaka ikon mallakar Jehobah, yaya ayyukanmu suka yi kama da na masu aminci na zamanin dā?

22 Cikin shekaru da yawa, Jehobah ya ba masu aminci ayyuka dabam dabam. Nuhu ya gina jirgi kuma shi “mai-shelan adalci” ne. (2 Bit. 2:5) Joshua ya ja-goranci Isra’ilawa zuwa Ƙasar Alkawari, amma ya yi nasara domin ya karanta “littafin shari’a . . . dare da rana,” kuma ya aikata daidai da abin da ke cikinsa. (Josh. 1:7, 8) Kiristoci na ƙarni na farko sun yi almajirai kuma sun taru a kai a kai don su yi nazarin Nassosi.—Mat. 28:19, 20.

23 Muna ɗaukaka ikon mallakar Jehobah kuma mu kasance da aminci ta wurin yin wa’azin adalci da samun almajirai, da bin gargaɗin Nassi, da kuma taruwa da ’yan’uwa masu bi a taron ikilisiya da manyan taro, da kuma taron gunduma. Irin waɗannan ayyuka suna taimaka mana mu kasance da gaba gaɗi, mu yi ƙarfi a ruhaniya, kuma mu yi nasara wajen yin nufin Allah. Waɗannan ayyuka ba su da wuya a gare mu domin muna da goyon bayan Ubanmu na samaniya da kuma Ɗansa. (K. Sha 30:11-14; 1 Sar. 8:57) Bugu da ƙari muna da goyon bayan “’yan’uwanci” waɗanda suke tafiya cikin gaskiya kuma suna ɗaukaka Jehobah a matsayin Ubangijinsu Mai-Ikon Mallaka.—1 Bit. 2:17.

Yaya Za Ka Amsa?

• Yaya ya kamata mu ɗauki mizanan ɗabi’a na Jehobah?

• Waɗanne halayen Ayuba ne ka fi so?

• Kamar yadda aka nuna a Ayuba 31:29-37, wane irin hali ne Ayuba yake da shi?

• Me ya sa zai yiwu mu kasance da aminci ga Allah?

[Hoton da ke shafi na 29]

Ayuba ya kasance da aminci ga Jehobah. Mu ma za mu iya yin hakan!

[Hoton da ke shafi na 32]

Za mu iya kasancewa da aminci!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba