Za Ka Ci Gaba Da Yin Nagarta Kuwa?
“Har in mutu ba ni rabuwa da [nagartata].”—AYU. 27:5.
1, 2. Wane aikin gini muke bukatar mu yi, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?
A CE kana kallon zanen wani gida da za a gina. Ka yi sha’awar kyaun zanen. Cike da farin ciki, kana tunanin yadda gidan zai amfane ka da iyalinka. Amma za ka yarda cewa, wannan zanen da duk wani tunanin da za ka yi a kansa ba zai amfane ka ba idan ba ka gina gidan ba kuma ka ƙaura ka shiga kuma ka ci gaba da adana shi.
2 Hakazalika, muna iya yin tunanin nagarta a matsayin hali mai muhimmanci da zai amfane mu da waɗanda muke ƙauna sosai. Amma yin tunani game da nagarta ba zai amfane mu ba idan ba mu koye ta ba kuma mu yi ƙoƙari mu kasance da nagarta ta Kirista. A duniya ta yau, sau da yawa kayan gini na zahiri suna da tsada. (Luk 14:28, 29) Hakazalika, koyon nagarta yana ɗaukan lokaci kuma yana bukatar yin ƙoƙari, duk da haka kwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu. Saboda haka, bari mu tattauna tambayoyi uku: Ta yaya za mu zama mutane masu nagarta? Ta yaya za mu ci gaba da yin nagarta ta Kirista? Menene za a yi idan a wani lokaci wani ya daina yin nagarta?
Ta Yaya Za Mu Zama Mutane Masu Nagarta?
3, 4. (a) Ta waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake taimaka mana mu koyi yin nagarta? (b) Ta yaya za mu koyi nagarta, kamar yadda Yesu ya yi?
3 A talifin da ya gabata mun lura cewa Jehobah ya ba mu gatan zaɓan ko za mu zama mutane masu yin nagarta. Amma, abin farin ciki shi ne, bai ƙyale mu mu yi abin da muka ga dama a wannan batun ba. Ya koya mana yadda za mu kasance da wannan hali mai tamani, kuma yana ba mu ruhunsa mai tsarki a yalwace, wanda ke taimaka mana mu yi amfani da koyarwarsa. (Luk 11:13) Ƙari ga haka, yana ba da kāriya ta ruhaniya ga waɗanda suka yi ƙoƙari su yi tafiya cikin adalci.—Mis. 2:7.
4 Ta yaya Jehobah ya koya mana mu zama masu yin nagarta? Fiye da kome, ta wajen aika Ɗansa, Yesu, zuwa duniya. Yesu ya bi tafarki na cikakkiyar biyayya. Ya yi “biyayya har da mutuwa.” (Filib. 2:8) Yesu ya yi biyayya ga Ubansa na samaniya a dukan abubuwan da ya yi, har ma lokacin da yin hakan yake da wuya sosai. Ya gaya wa Jehobah: “Ba nawa nufi ba, naka za a yi.” (Luk 22:42) Ya kamata kowannenmu ya tambayi kansa, ‘Ina da irin wannan halin na yin biyayya?’ Ta wajen bin tafarki na yin biyayya da ra’ayin da ya dace, za mu zama masu nagarta. Ka yi la’akari da wasu wurare na rayuwa da yin biyayya yake da muhimmanci sosai.
5, 6. (a) Ta yaya Dauda ya nanata muhimmancin kasancewa da nagarta har sa’ad da babu wanda ke kallonmu? (b) Waɗanne kaluɓale ne Kiristoci a yau suke fuskanta game da nagartarsu sa’ad da suke su kaɗai?
5 Muna bukatar mu yi biyayya ga Jehobah har a lokacin da muke mu kaɗai. Mai zabura Dauda ya ambata muhimmancin yin nagarta a lokacin da yake shi kaɗai. (Karanta Zabura 101:2.) Tun da yake Dauda sarki ne, a koyaushe yana tare da mutane. Babu shakka, akwai lokatai da ɗarurruwan mutane, har dubbai suke kallon abubuwan da yake yi. (Gwada Zabura 26:12.) Yin nagarta a irin waɗannan lokacin suna da muhimmanci, don sarkin yana bukatar ya kafa wa mutanensa misali mai kyau. (K. Sha 17:18, 19) Amma, Dauda ya koyi cewa a lokacin da yake shi kaɗai, wato, ‘cikin gidansa’ yana bukatar ya yi nagarta. Mu kuma fa?
6 A Zabura 101:3, Dauda ya ce: “Ba zan sa wani mummunan al’amari a gaban idanuna ba.” Da akwai zarafi da yawa a yau da za mu iya ganin mummunan abubuwa, musamman sa’ad da muke mu kaɗai. Intane yana sa mutane da yawa su fuskanci wannan ƙalubalen. Yana da sauƙi mu faɗa jarrabar kallon hotunan batsa da ba su dace ba. Amma wanda yake yin hakan, yana yin biyayya ne ga Allahn da ya hure Dauda ya rubuta waɗannan kalmomin? Hotunan batsa suna da lahani, don suna ta da mummunan sha’awoyi da haɗama, suna ɓata lamiri, suna rushe aure, kuma suna zubar da mutuncin duk wanda ya yi hakan.—Mis. 4:23; 2 Kor. 7:1; 1 Tas. 4:3-5.
7. Wane mizani ne zai iya taimaka mana mu yi nagarta sa’ad da muke mu kaɗai!
7 Hakika, babu bawan Jehobah da yake shi kaɗai da gaske. Ubanmu yana kallonmu cikin ƙauna. (Karanta Zabura 11:4.) Jehobah yana farin ciki sa’ad da ya gan ka kana yin tsayayya da gwaji! Ta yin haka, kana yin biyayya da kalaman Yesu da ke Matta 5:28. Ko ta yaya, kada ka kalli hotuna da za su jarrabe ka ka yi abin da ba shi da kyau. Kada ka yi musanyar amincinka mai tamani da kallon ko kuma karanta littafin batsa!
8, 9. (a) Daniel da abokansa sun fuskanci wane ƙalubale game da amincinsu? (b) Ta yaya Kiristoci matasa a yau suke sa Jehobah da ’yan’uwansu Kiristoci farin ciki?
8 Muna iya zama masu adalci ta wajen yin biyayya da Jehobah sa’ad da muke tsakanin marasa bi. Ka yi tunanin Daniel da abokansa uku. An kwashe su zuwa bauta a Babila sa’ad da suke matasa. A wajen, marasa bi da ba su san kome ba game da Jehobah sun kewaye su, kuma an matsa wa Ibraniyawan huɗu su ci abinci da Dokar Allah ta hana. Waɗannan matasa suna iya tabbatar wa kansu cewa wannan ba laifi ba ne. Ballantana ma, iyayensu, dattawa, da kuma firistoci ba za su ga abin da su huɗun suke yi ba. Wanene zai sani? Jehobah zai sani. Saboda haka, sun yi tsayin daka kuma suka yi masa biyayya duk da matsi da kuma haɗarin da ke tattare da yin hakan.—Dan. 1:3-9.
9 A dukan duniya, matasa Shaidun Jehobah suna bin irin wannan tafarkin, sun manne wa mizanan Allah ga Kiristoci kuma sun ƙi su faɗa wa matsi na tsara. Sa’ad da ku matasa kuka ƙi shan ƙwaya, yin mugunta, zagi, lalata da sauran mugun ayyuka, kuna yi wa Jehobah biyayya ke nan. Sa’ad da kuke hakan, kuna yin nagarta. Kuna amfana, kuma kuna sa Jehobah da ’yan’uwanku Kiristoci farin ciki!—Zab. 110:3.
10. (a) Waɗanne ra’ayoyi marar kyau game da fasikanci ne ya sa wasu matasa suka daina yin nagarta? (b) Ta yaya nagarta take sa mu aikata game da haɗarin fasikanci?
10 Muna bukatar kuma mu yi biyayya sa’ad da muke sha’ani da wani jinsi. Mun san cewa Kalmar Allah ta hana fasikanci. Amma, yana da sauƙi mu ƙyale halinmu na yin biyayya ya zama na amincewa da abubuwa marar kyau. Alal misali, wasu matasa sun yi jima’i na baki ko ɗuwawu ko kuma yin wasa da al’aura, kuma sun kammala cewa waɗannan ayyukan ba laifi ba ne domin suna tunani cewa ba ainihin “zina suke yi ba.” Irin waɗannan matasan sun manta ko kuma sun yi watsi da cewa kalmar da Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da ita don fasikanci ta ƙunshi dukan waɗannan ayyuka, hakan mugun hali ne da ake iya yi wa mutum yankan zumunci don yinsu.a Amma, abin da ya fi muni shi ne cewa sun yi banza da bukatar yin nagarta. Tun da yake muna ƙoƙarin mu ci gaba da yin nagarta, ba za mu nemi hujja don yin halaye marasa kyau ba. Bai kamata mu yi abin da bai da kyau da gangan ba domin mun san cewa babu wanda zai yi mana horo. Ba za mu mai da hankali kawai ga horon da za a yi mana a ikilisiya ba idan muka yi abin da ba shi da kyau. Maimakon haka, ya kamata mu mai da hankali a kan yin abin da zai sa Jehobah farin ciki kuma mu guji yin abin da zai ɓata masa rai. Maimakon mu ga yadda za mu yi kusa ga yin zunubi, ya kamata mu yi nisa ga yin hakan kuma mu “guje ma fasikanci.” (1 Kor. 6:18) Ta haka, muna nuna cewa mu mutane ne masu yin nagarta.
Ta Yaya Za Mu Ci Gaba da Yin Nagarta?
11. Me ya sa kowanne aiki na yin biyayya yake da muhimmanci? Ka ba da bayani.
11 Muna koyan nagarta ta wajen yin biyayya, saboda haka, muna ci gaba da yin nagarta ta wajen jimrewa cikin tafarkin yin biyayya. Yin biyayya cikin ƙaramin abu sau ɗaya tak, zai iya zama kamar ba shi da muhimmanci. Amma irin waɗannan ayyuka na biyayya za su kafa tarihi na yin nagarta. Alal misali: Tubali ɗaya kamar ba shi da muhimmanci, amma idan muka ɗora masu yawa a kan juna, za mu iya gina gida mai kyau. Saboda haka, ta wajen ci gaba da yin ayyuka na biyayya, za mu ci gaba da yin nagarta.—Luk 16:10.
12. Ta yaya Dauda ya kafa misali wajen yin nagarta sa’ad da yake fuskantar wulakanci da rashin adalci?
12 Za mu nuna cewa mu masu yin nagarta ne sa’ad da muka jimre wahala, wulakanci ko kuma rashin adalci. Ka yi la’akari da misalin Dauda a cikin Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da yake matashi, ya jimre tsanantawa daga sarkin da ya kamata ya wakilci ikon Jehobah. Amma, sarki Saul ya riga ya yi rashin tagomashin Jehobah kuma yana mugun kishin Dauda wanda Allah ya zaɓa. Duk da haka, Saul ya kasance da matsayinsa na ɗan lokaci kuma ya yi amfani da sojojin Isra’ila wajen neman Dauda. Jehobah ya ƙyale wannan rashin adalcin ya ci gaba har wasu shekaru. Dauda ya yi fushi da Allah ne? Ya tsai da shawara cewa babu amfanin jimrewa ne? Bai yi hakan ba. Ya ci gaba da daraja matsayin Saul wanda shafaffe ne na Allah, ya ƙi ya rama sa’ad da ya samu zarafin kashe Saul.—1 Sam. 24:2-7.
13. Ta yaya za mu ci gaba da yin nagarta idan wasu sun yi mana laifi?
13 Dauda ya kafa mana misali mai kyau a yau! Muna cikin ikilisiya na dukan duniya da ke cike da mutane ajizai, kowanne cikinsu yana iya yi mana laifi har ma ya yi rashin aminci. Hakika, an albarkace mu da yake muna zama a lokacin da mutanen Jehobah gabaki ɗaya ba za su taɓa ɓacewa ba. (Isha. 54:17) Amma, yaya za mu aikata idan wani ya yi mana laifi ko kuma ya ɓata mana rai? Idan muka ƙyale fushi ya sa mu riƙe wani ɗan’uwa mai bi a zuciya, muna iya daina kasancewa da aminci ga Allah. Halin wasu ba dalili ba ne na yin fushi da Allah ko kuma mu ƙi bin tafarkin yin nagarta. (Zab. 119:165) Jimrewa sa’ad da muke fuskantar gwaji zai taimake mu mu ci gaba da yin nagarta.
14. Yaya masu yin nagarta suke aikatawa sa’ad da aka yi canje-canje ga tsarin ƙungiya da kuma koyarwa?
14 Za mu ci gaba da yin nagarta ta wajen guje wa neman laifi ko kuma kurakurai. Hakika, hakan yana nufin kasancewa da aminci ga Jehobah. Yana yi wa mutanensa albarka yanzu fiye da dā. Yanzu ne aka fi ɗaukaka bauta mai tsarki a duniya. (Isha. 2:2-4) Sa’ad da aka yi gyara ga yadda aka yi bayanin wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki ko kuma yadda ake yin abubuwa, ya kamata mu amince da hakan. Muna farin cikin ganin tabbacin cewa haske na ruhaniya har ila yana ƙaruwa. (Mis. 4:18) Idan ya yi mana wuya mu fahimci wani gyara da aka yi, ya kamata mu roƙi Jehobah ya taimake mu mu fahimci batun. Kafin lokacin, ya kamata mu jimre ta wajen yin biyayya, ta hakan za mu ci gaba da yin nagarta.
Idan Mutum Ya Daina Yin Nagarta Fa?
15. Wanene kawai zai iya sa ka daina yin nagarta?
15 Wannan tambaya ce mai sa tunani, ko ba haka ba? Kamar yadda muka koya a talifin da ya gabata, nagarta tana da muhimmanci sosai. Idan ba ma yin nagarta, ba mu da dangantaka da Jehobah kuma ba mu da bege. Ka sa wannan a zuciya: Mutum ɗaya ne kawai a dukan duniya zai iya sa ka daina yin nagarta. Kai ne mutumin. Ayuba ya fahimci wannan gaskiyar sosai. Ya ce: “Har in mutu ba ni rabuwa da gaskiyata.” (Ayu. 27:5) Idan kana da irin wannan ƙudurin kuma ka kusaci Jehobah, ba za ka taɓa rashin nagartarka ba.—Yaƙ. 4:8.
16, 17. (a) Idan mutum ya yi mugun zunubi, wane mugun tafarki ne bai kamata ya bi ba? (b) Wane tafarki mai kyau ne ya kamata ya bi?
16 Duk da haka, wasu sun daina yin nagarta. Kamar yadda ya faru a lokacin da manzanni suke da rai, wasu a yau suna aikata mugun zunubi. Idan hakan ya faru da kai, menene za ka yi? Bari mu fara tattauna abin da bai kamata a yi ba. Halin mutane shi ne su ƙi gaya wa iyayensu, ’yan’uwa Kiristoci, ko kuwa dattawa mugun zunubin da suka aikata. Littafi Mai Tsarki ya tuna mana: “Wanda ya rufe laifofinsa ba za ya yi albarka ba: Amma dukan wanda ya faɗa su ya kuwa rabu da su za ya sami jinƙai.” (Mis. 28:13) Waɗanda suka nemi su rufe zunuban da suka yi sun yi mugun kuskure, domin babu abin da za a iya ɓoye wa Allah. (Karanta Ibraniyawa 4:13.) Wasu sukan yi rayuwa iri biyu, sukan nuna suna bauta wa Jehobah yayin da suke aikata zunubi. Irin wannan rayuwar ba ta nagarta ba ce, mutumin ya yi rashin nagartarsa. Jehobah ba ya son bautar mutanen da suke rufe mugun zunubansu. Akasin haka, irin wannan munafuncin yana ba shi haushi.—Mis. 21:27; Isha. 1:11-16.
17 Sa’ad da Kirista ya yi mugun zunubi, Littafi Mai Tsarki ya faɗi matakin da zai ɗauka. Lokaci ya yi da zai nemi taimakon dattawa Kiristoci. Jehobah ya naɗa dattawa a matsayin waɗanda za su taimaka wa waɗanda suke mugun rashin lafiya na ruhaniya. (Karanta Yaƙub 5:14.) Kada ka bari tsoron horon da za a yi maka ko gyara ya hana ka biɗar lafiyarka ta ruhaniya. Mutum mai hikima zai bar zafin allura ko aikin tiyata ya hana shi kula da rashin lafiyar da za ta iya ɗauke ransa?—Ibran. 12:11.
18, 19. (a) Ta yaya misalin Dauda ya nuna cewa mutum zai sake yin nagarta? (b) Menene ka kuɗuri ka yi game da nagartarka?
18 Mutumin zai iya warkewa kuwa? Mutumin da ya daina yin nagarta zai iya soma yin ta kuwa? Ka sake yin la’akari da misalin Dauda. Dauda ya aikata mugun zunubi. Ya yi sha’awar matar wani, ya yi zina da ita, kuma ya sa aka kashe mijinta da bai san hawa ko sauka ba. Zai yi wuya a ce Dauda mutumi ne mai nagarta a lokacin, ko ba haka ba? Duk da haka, akwai abin da za a iya yi ne? An yi wa Dauda horo sosai. Amma don ya tuba da gaske, Jehobah ya gafarta masa. Dauda ya koya daga horon da aka yi masa kuma ya sake kasancewa da nagarta ta wajen yin biyayya ga Allah kuma ya ci gaba da yin hakan. Rayuwar Dauda ta nuna tabbacin abin da aka faɗa a Misalai 24:16: “Mai-adilci ya kan fāɗi so bakwai, ya sake tashi kuma.” Menene sakamakon hakan? Ka yi la’akari da abin da Jehobah ya gaya wa Sulemanu game da Dauda bayan ya mutu. (Karanta 1 Sarakuna 9:4.) Allah ya tuna da Dauda a matsayin mutum mai adalci. Hakika, Jehobah zai iya tsabtace masu zunubi da suka tuba daga taɓon mugun zunubi.—Isha. 1:18.
19 Hakika, za ka zama mutum mai nagarta ta wajen yin biyayya ga Allah don kana ƙaunarsa. Ka ci gaba da jimrewa da aminci, kuma idan ka yi zunubi mai tsanani ka tuba da gaske. Lalai nagarta hali ne mai tamani! Bari kowannenmu ya yi ƙuduri kamar Dauda: “Amma ni, a cikin [nagarta] zan yi zamana.”—Zab. 26:11.
[Hasiya]
a Ka duba Hasumiyar Tsaro na 1 ga Maris, 2004 shafi na 11, sakin layi na 15.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya za ka zama mutum mai yin nagarta?
• A waɗanne hanyoyi ne za ka ci gaba da yin nagarta?
• Ta yaya zai yiwu a sake soma yin nagarta?
[Akwati a shafi na 8]
‘Wannan Halin Kirki Ne’
Wata mata mai ciki wata biyar ce ta faɗi waɗannan kalaman game da alheri da nagarta na wata baƙuwa. Ta je shagon da ake sayar da shayi, sa’o’i da barin wurin ta fahimci cewa ta bar jakar kuɗinta a shagon. Jakar tana ɗauke da Dala 2,000, kuɗi mai yawa fiye da waɗanda take fita da su a dā. Ta gaya wa wata jarida cewa, “Na rikice ba kaɗan ba.” Amma, wata budurwa ta ga jakar kuma nan da nan ta nemi mai shi. Da ba ta yi nasara ba, sai ta kai wa ’yan sanda, kuma ’yan sanda suka nemi matar mai ciki. “Wannan halin kirki ne sosai,” in ji wannan mata mai nuna godiya. Me ya sa wannan budurwar ta mai da kuɗin? Jaridar ta faɗi cewa a matsayinta na Mashaidiyar Jehobah, ta “yi irin wannan nagarta domin addinin da ta yi girma a ciki.”
[Hoto a shafi na 9]
Matasa za su iya yin nagarta sa’ad da suka fuskanci gwaji
[Hoto a shafi na 10]
Dauda ya ɗan daina yin nagarta, amma ya farfaɗo