Sashe na 7—Minene Ya Zama Sakamakon Tawaye?
1-3. Ina yadda lokaci ya tabbatas da Jehovah mai gaskiya?
GAME da muhawwara na ikon Allah na sarauta fa, minene ya zama sakamakonsa ko cikin dukan ƙarnuka na sarautar yan-Adam a yance daga Allah? Ashe yan-Adam sun zama masu sarauta mafi-kyau da Allah? Hakika a’a, idan muka gwada da labarin zaluncin mutum da ɗan’uwansa.
2 Lokacinda iyayenmu na farko suka ƙi da sarautar Allah fa, bala’i ta auku. Sun kawo shan wahala bisa kansu da dukan iyalin yan-Adam da suka zo ta wurinsu. Kuma basu da wani da zasu kama shi da laifi sai dai kansu. Kalmar Allah ta ce: “Sun yi masa aikin ƙazamta, aibinsu ke nan, su ba ’ya’yansa ba ne.”—Kubawar Shari’a 32:5.
3 Tarihi ta nuna gaskiyar fadakadwar Allah ga Adamu da Hawa’u cewa idan suka fita daga tanadodin Allah fa, zasu lalace kuma su mutu daga bisani. (Farawa 2:17; 3:19) Sun fita kuwa daga sarautar Allah, kuma sun lalace har kuma mutu.
4. Me yasa an haife dukanmu marasa cikawa ne, masu ciwo da kuma mutuwa?
4 Abinda ya faru nan gaba ga dukan zuriyarsu shine Romawa 5:12 ya bayyana: “Domin wannan fa, kamar yadda zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya [Adamu, kan iyalin mutane], mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane.” Lokacinda iyayenmu na farko suka yi tawaye da shugabancin Allah fa, sun zama masu zunubi masu aibi. Cikin jituwa da dokokin ƙwayoyin haifuwa fa, rashin cikawa ne kawai suka haye ga zuriyarsu. Shi yasa an haife dukanmu da aibi, masu kamuwa da ciwo da kuma mutuwa.
5, 6. Minene tarihi ya nuna ko game da ƙoƙarceƙoƙarcen mutum na kawo salama da ni’imtawa?
5 Ƙarnuka dayawa sun shige ko. Dauloli sun bayanu sun kuma shuɗe. An gwada kowane irin gwamnati ko da zaka iya tunaninsa. Duk da haka, loto loto, abubuwa masu ban razana sun auku ko ga iyalin yan-Adam. Bayan shekaru dubu shidda fa, wani zai iya zata cewa da yan-Adam sun gushe ko zuwa matsayin kafa salama, shari’a, da ni’imtawa a dukan duniya kuma cewa yanzu haka sun gwaninta ko game da amfanin tawali’u, nasiha, da kuma na haɗa kai.
6 Amma dai, ƙishiyar haka, shine gaskiyar zaton nan. Babu wata gwamnatin yan-Adam da aka taɓa shirya da ta kawo salama da ni’imtawa na gaskiya ga kowa. A cikin wannan ƙarni na 20 kaɗai, mun ga shiryayyen kisan miliyoyin mutane ko a manyan Gobara da kisan mutane sama da miliyan 100 cikin yaƙoƙi. A lokuttanmu fa an riga an zalunta, kashe, da kuma jefa mutane dayawa a kurkuku domin rashin jurewa da kuma rashin jituwa na siyasa.
Yanayin Ayau
7. Ina yadda za a iya kwatanta yanayin iyalin yan-Adam ayau?
7 Ƙari ga haka, ka yi la’akari da dukan yanayin iyalin yan-Adam ayau. Aika laifi da nuna ƙarfi suna ko’ina. Shan mugan ƙwayoyi ya zama annoba. Cututtuka da ake hayewa ta wurin jima’i sun gama gari. Cutan nan AIDS da ake tsoronsa sosai yana harɓa miliyoyin mutane. Mutane miliyoyi barkatai suna mutuwa domin yunwa ko kuwa cuta kowace shekara, yayinda ƙalila kuma suna wadatawa ƙwarai. Yan-Adam sun gurɓantad da kuma lalace duniya. Zaman iyali da halin kirki sun sukukuce ko a ko’ina. Gaskiya fa, rayuwa yau yana nuna munin sarautar ‘allah na wannan duniya,’ Shaitan ne. Duniya da shine ubangijinta marasa tausayi ne, marasa hankali, kuma ɓatace sarai.—2 Korinthiyawa 4:4.
8. Me yasa ba zamu ce da abinda mutane suke cimma gushewa na gaskiya ne ba?
8 Allah ya bada isasshen lokaci ko ga yan-Adam su kai ga girman gushewarsu na kimiya da kuma na dukiya. Amma ashe gushewar kirki ne yayinda baka da kibiya an sāke su da inji halbi, tankunan yaƙi, jirajen yaƙi, da kuma konan nukiliya? Ashe gushewa ne yayinda mutane suna iya tafiya cikin sararin sama amma basu zaman salama tare bisa duniya? Ashe gushewa ne yayinda mutane suna jin tsoron yin tafiya bisa tituna da dare, ko kuwa da rana a wasu wurare ma?
Abinda Shigewar Lokaci ya Nuna
9, 10. (a) Minene ƙarnukan lokutta da suka shige sun nuna sarai? (b) Me yasa Allah ba zaya kawas da son zuciya ba?
9 Abinda gwadawa na ƙarnukan lokaci ya nuna shine cewa ba shi yiwuwa ga yan-Adam su shirya tafiyassu sosai waje da sarautar Allah. Ba shi yiwuwa garesu su yi haka daidai kamar yadda ba shi yiwuwa su rayu babu ci, sha, da yin lumfashi. Shaidar sarai yake: An shirya mu mu dangana bisa jagabancin Mahaliccinmu daidai kamar an halicce mu mu rayu ta wurin abinci, ruwa, da iska kuma.
10 Ta wurin kyale mugunta fa, Allah ya nuna sarai mumunan sakamakon ɓata amfanin son zuciya. Son zuciya kuwa kyauta ne maigirma shi yasa maimakon raba yan-Adam da shi fa, Allah ya yarda masu su ga abinda ɓata amfaninsa ke nufa. Kalmar Allah ya faɗi gaskiya yayinda ya ce: “Mutum ba shi da iko shi shirya tafiyassa.” Gaskiya ne ma yayinda ya ce: “Mutum ya sami iko bisa mutum don cutarsa.”—Irmiya 10:23; Mai-wa’azi 8:9.
11. Anya akwai wata sarautar yan-Adam da ta kawas da shan wahala ko?
11 Kyalewar sarautan yan-Adam na shekaru dubu shidda yanzu da Allah ya yi ya nuna ko sarai cewa mutum ba zai iya kawas da shan wahala ba. Mutum ba zai taɓa yin haka ba. Alal misali, a kwanansa Sarki Solomon na Israila, da dukan hikima, arziki, da ikonsa, baya iya kawas da wahaloli da suke fitowa daga sarautar yan-Adam ba. (Mai-wa’azi 4:1-3) A makamancin hali, a kwananmu fa, shugabannen duniya, har da wayewar kai na zamani, basu iya kawas da shan wahala ba. Mafi muni ma, tarihi ta nuna ko cewa yan-Adam a yance daga sarautar Allah sun ƙara girman shan wahala maimakon kawas da shi.
Yin La’akarin Allah Mai-nisa
12-14. Wane albarkatai masu-daɗewa ne zasu zo ta wurin kyalewar shan wahala da Allah ya yi?
12 Kyale shan wahala da Allah ya yi ya kasance ko da ɗaci garemu. Amma shi ya yi la’akari mai-nisa ko, yana sanin sakamako mai-kyau da zai zo daga bisani. Ra’ayin Allah zai amfane halittu, ba kawai na ƙalilan shekaru ko kuwa na yan dubban shekaru ba, amma na miliyoyin shekaru, hakika, har matuƙa.
13 Idan fa wani yanayi ya sāke aukuwa kuma nan gaba da wani ya ɓata amfanin son zuciya don tuhume hanyar Allah na yin abubuwa, ba za a ba shi wani lokaci kuma don ya gwada ra’ayoyinsa ba. Da shike ya ba yan tawaye dubban shekaru ko, Allah ya kafa tushen tsai da shawara ko wanda za a iya aika shi duk matuƙa ko’ina cikin sararin halitta.
14 Domin Jehovah ya kyale mugunta ko da shan wahala a lokacin nan fa, an tabbatas da shi ke nan sarai cewa babu wani abu da ke waje da shi da zai yi nasara. Za a tabbatas da shi ke nan sarai cewa babu wata tsari na mutane ko kuwa na halittun ruhu mai yancin kansa ne zai kawo madawwamiyar albarka. Da haka fa, Allah zai kasance babu laifi a kawas da wani mai-tawaye babu ɓata lokaci. “Zaya hallaka dukan miyagu.”—Zabura 145:20; Romawa 3:4.
[Hoto a shafi na 15]
Bayan da iyayenmu na farko sun zaɓa yancin kai daga wurin Allah, da sannu sannu suka tsofe kuma mutu
[Hotuna a shafi na 16]
Sarautar yan-Adam waje da Allah ya kasance bala’i
[Inda Aka Ɗauko]
Foton U.S. Coast Guard