Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • rq darasi na 9 pp. 18-19
  • Tilas Bayin Allah su Kasance da Tsabta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tilas Bayin Allah su Kasance da Tsabta
  • Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Makamantan Littattafai
  • Allah Yana Kaunar Mutane Masu Tsabta
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Jehobah Yana So Bayinsa Su Kasance da Tsabta
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Ta Yaya Za Mu Zama Masu Tsabta a Gaban Allah?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • An Tsabtacce Mutane Don Ayyuka Masu Kyau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
rq darasi na 9 pp. 18-19

Darasi na 9

Tilas Bayin Allah su Kasance da Tsabta

Don me tilas ne mu kasance da tsabta a kowace hanya? (1)

Me ake nufi da zama da tsabta na ruhaniya? (2)

tsabtar ɗabi’a? (3) tsabtar azanci? (4) tsabtar jiki? (5)

Waɗanne maganganun banza ne zamu guje masu? (6)

1. Jehovah Allah yana da tsabta kuma mai-tsarki ne. Yana son masu bauta masa su kasance da tsabta​—a ruhaniya, ɗabi’a, azanci, da kuma a jiki. (1 Bitrus 1:16) Ana bukatar ƙoƙari na sarai domin a kasance da tsabta a gaban Allah. Muna zama a cikin duniya mara-tsabta. Muna faman kame halayenmu na son yin laifi. Amma kada mu fidda rai.

2. Tsabtar Ruhaniya: Idan muna so mu bauta ma Jehovah, ba zamu ci gaba da bin koyaswa ko al’adun addinin ƙarya ba. Dole mu fito daga cikin addinin ƙarya kuma ƙi goyon bayan ta a kowace hanya. (2 Korinthiyawa 6:​14-18; Ru’ya ta Yohanna 18:4) Da zarar mun koyi gaskiya game da Allah, tilas ne mu maida hankali kada mutane su yaudare mu da koyaswan ƙarya.​—2 Yohanna 10, 11.

3. Tsabtar Ɗabi’a: Jehovah yana son dukan masu bauta masa su nuna halin Kirista na gaskiya a kowane lokaci. (1 Bitrus 2:12) Yana ganin dukan abinda muke yi, ko a asirce ma. (Ibraniyawa 4:13) Sai mu guje wa halin lalata da wasu ayukan ƙazanta na duniyar nan.​—1 Korinthiyawa 6:​9-11.

4. Tsabtar Azanci: Idan muka cika azantanmu da tunani masu tsabta, ƙyau, halayenmu ma zasu kasance da tsabta. (Filibbiyawa 4:8) Amma idan muka zama da tunani bisa rashin tsabta, zai kai ga mugunta. (Matta 15:​18-20) Sai mu guje ma fasalolin nishaɗi da zasu ɓata azantanmu. Zamu iya cika azantanmu da tunani masu-tsabta ta wurin nazarin Kalmar Allah.

5. Tsabtar Jiki: Domin suna wakilce Allah fa, ya kamata Kiristoci su kasance da tsabtar jiki da kuma tufafin su. Ya kamata mu wanke hannayenmu idan mun gama bayan gida, mu kuma wanke su ma kafin cin abinci ko kuma taɓa wani abinci. Idan ba ka da wurin bayan gida mai-kyau, sai mu binne bayan gida sosai. (Kubawar Shari’a 23:​12, 13) Zama da tsabta na jiki na ƙara lafiyar jiki. Gidan Kirista ya kamata ya kasance da tsabta sosai a ciki da wajen. Ya kamata ya zama gurbi a gaban jama’a.

6. Tsabtaccen Magana: Mutanen Allah tilas ne su faɗi gaskiya kullum. Masu ƙarya ba zasu shiga Mulkin Allah ba. (Afisawa 4:25; Ru’ya ta Yohanna 21:8) Kiristoci basu maganar ashar. Ba sua faɗi ko kuwa saurare ƙazamin wasa ko taɗi mara-tsarki. Suna kasance dabam a wurin aiki ko makaranta da kuma cikin furcinsu a unguwansu, saboda furcinsu mai-kyau.​—Afisawa 4:​29, 31; 5:3.

[Hotuna a shafi na 18 da 19]

Tilas ne bayin Allah su kasance da tsabta a kowace hanya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba