An Tsabtacce Mutane Don Ayyuka Masu Kyau
“Bari mu tsarkake kanmu daga dukan ƙazantar jiki da ta ruhu, muna kāmala tsarki cikin tsoron Allah.”—2 KORINTHIYAWA 7:1.
1. Menene Jehovah yake bukata daga waɗanda suke bauta masa?
“WANENE za ya hau zuwa tudun Ubangiji? Wanene za ya tsaya a cikin wurinsa mai-tsarki?” Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya yi wannan tambayar mai sa tunani game da bauta da Jehovah ya amince da ita. Sai ya ba da amsa: “Shi wanda ya ke da hannuwa masu-tsabta, da zuciya mai-tsarki; wanda ba ya ɗauki ransa ya sa ga abin banza ba, ba ya kuwa rantse da algus ba.” (Zabura 24:3, 4) Don Jehovah ya amince da mutum, wanda shi mai tsarki ne, dole mutum ya kasance da tsabta da tsarki. Da farko, Jehovah ya tuna wa ikilisiyar Isra’ila: “Ku tsarkake kanku fa, ku za ma masu-tsarki; gama ni mai-tsarki ne.”—Leviticus 11:44, 45; 19:2.
2. Ta yaya Bulus da Yaƙub suka nanata muhimmancin tsabta a bauta ta gaskiya?
2 Ƙarnuka bayan haka, manzo Bulus ya rubuta wa ’yan’uwa Kiristoci a malalacin birni na Koranti: “Da shi ke fa, ƙaunatattu, muna da waɗannan alkawarai, bari mu tsarkake kanmu daga dukan ƙazantar jiki da ta ruhu, muna kāmala tsarki cikin tsoron Allah.” (2 Korinthiyawa 7:1) Wannan kuma ya nuna cewa don mutum ya kasance da dangantaka da Allah kuma ya samu albarka da ya yi alkawarinta, dole mutum ya kasance da tsabta ya ’yantu daga ƙazanta da lalata na zahiri da na ruhaniya. Hakanan ma, a rubutu game da bauta da Allah ya amince da ita, almajiri Yaƙub ya ce: “Addini mai-tsarki mara-ɓāci a gaban Allah Ubanmu ke nan, mutum shi ziyarci marayu da gwauraye cikin ƙuncinsu, shi tsare kansa mara-aibi daga duniya.”—Yaƙub 1:27.
3. Don Allah ya amince da bautarmu, da me za mu damu ƙwarai?
3 Tun da yake kasancewa da tsabta, tsarki da marasa aibi muhimman abubuwa ne a bauta ta gaskiya, wanda yake so ya samu amincewar Allah ya kamata ya mai da hankali sosai ga cika waɗannan farillai. Domin mutane a yau suna da mizanai da ra’ayoyi dabam dabam game da tsabta, muna bukatar mu fahimci kuma mu yi biyayya da abin da Jehovah yake ɗauka da tsabta kuma ya amince da shi. Muna bukatar mu bincika abin da Allah ke bukata masu bauta masa su yi game da wannan da abin da ya yi ya taimaka musu su zama kuma su kasance da tsabta kuma ya amince da shi.—Zabura 119:9; Daniel 12:10.
Tsabta don Bauta ta Gaskiya
4. Ka yi bayanin ra’ayin Littafi Mai Tsarki na tsabta.
4 Ga yawancin mutane, kasancewa da tsabta yana nufin kada mutum ya yi datti ko kuma ya gurɓata. Amma, a cikin Littafi Mai Tsarki, an ba da ma’anar ra’ayin kasancewa da tsabta da kalmomin Ibrananci da Helenanci da sun kwatanta tsabta ba kawai cikin azanci na zahiri ba amma sau da yawa ya fi cikin azanci na ɗabi’a da na ruhaniya. Da haka, wani kundin sani na Littafi Mai Tsarki ya ce: “ ‘Tsabta’ da ‘rashin tsabta’ kalmomi ne da ƙyar a yi amfani da su wajen lafiyar jiki, amma game da ra’ayoyi na addini ne. Saboda haka ƙa’idar ‘tsabta’ ta shafi kusan kowane fasalin rayuwa.”
5. Har yaya Dokar Musa ta yi ja-gorar tsabta a rayuwar Baisra’ile?
5 Hakika, Dokar Musa ta ƙunshi dokoki da farillai a kan kowane fannin rayuwa na Isra’ilawa, ya faɗi abin da ke da tsabta da aka amince da shi da abin da ba shi da tsabta. Alal misali, a Leviticus surori 11 zuwa 15, mun samu bayani dalla-dalla game da tsabta da rashin tsabta. Wasu dabbobi ba su da tsabta, kuma Isra’ilawa ba za su ci su ba. Haihuwa za ta sa mace ta kasance ba ta da tsabta na ɗan lokaci. Wasu cututtuka na fatar jiki, musamman kuturta, da abin da ke fitowa daga al’aurar namiji da tamace za su sa mutum ya kasance ba shi da tsabta. Doka ma ta faɗa abin da za a yi a yanayi da ya shafi rashin tsabta. Alal misali, a Litafin Lissafi 5:2, mun karanta: “Ka umurci ’ya’yan Isra’ila, su fitarda kowane kuturu daga cikin sansani, da kowane mai-mājina, da dukan wanda ya ƙazantu ta wurin gawa.”
6. Domin menene aka ba da dokoki a kan tsabta?
6 Babu shakka, waɗannan da wasu dokoki daga Jehovah na ɗauke da hanyar magani da yadda jiki ke aiki tun da wuri kafin likitoci su san game da su, kuma mutane sun amfana sa’ad da suka bi su. Duk da haka, wannan dokoki ba a bayar ba kawai don ja-gorar lafiya ko ja-gora a hanyar magaji. Ɓangare ne na bauta ta gaskiya. Gaskiya cewa dokokin sun shafi rayuwar mutane na yau da kullum—cin abinci, haihuwa, nasabar aure, da sauransu—ya nanata cewa Allahnsu, Jehovah yana da iko ya tsai da musu abin da ya dace da abin da bai dace ba a dukan fasalolin rayuwarsu, wadda an bayar gabaki ɗaya ga Jehovah.—Kubawar Shari’a 7:6; Zabura 135:4.
7. Ta bin Dokar, wace albarka al’ummar Isra’ila za ta samu?
7 Dokar alkawari kuma ta tsare Isra’ilawa daga ayyukan ƙazanta na al’ummai gewaye da su. Ta bin Dokar cikin aminci, haɗe da dukan farillai na kasance da tsabta a gaban Jehovah, Isra’ilawa za su dace su bauta wa Allahnsu kuma su samu albarkarsa. Game da wannan Jehovah ya gaya wa al’ummar: “Idan lallai za ku yi biyayya da maganata, ku kiyaye wa’adina kuma, sa’annan za ku zama keɓaɓiyar taska a gareni daga cikin dukan al’umman duniya; gama dukan duniya tawa ce. Za ku zama mulki na [firistoci] a gareni, al’umma mai-tsarki.”—Fitowa 19:5, 6; Kubawar Shari’a 26:19.
8. Me ya sa ya kamata Kiristoci a yau su saurari abin da aka faɗa cikin Doka game da tsabta.
8 Tun da Jehovah ya haɗa irin wannan umurnai cikin Doka ya koyar da Isra’ilawa yadda za su kasance da tsabta, tsarki, da amincewarsa, bai dace Kiristoci a yau su bincika a hankali yadda za su cika wannan farillan ba? Ko da Kiristoci ba sa ƙarƙashin Dokar, dole su tuna, yadda Bulus ya yi bayani cewa, duka abin da aka rubuta cikin Dokar “inuwar al’amuran da ke zuwa ne; amma aini na Kristi ne.” (Kolossiyawa 2:17; Ibraniyawa 10:1) Idan Jehovah Allah, wanda ya ce “ban canja ba,” ya ɗauki tsabta da rashin ƙazanta muhimmin abubuwa ne a bauta ta gaskiya a lokacin, dole ne mu a yau mu ɗauki batun kasancewa da tsabta a zahiri, a ɗabi’a da ruhaniya da muhimmanci idan muna so mu samu amincewarsa da albarkarsa.—Malachi 3:6; Romawa 15:4; 1 Korinthiyawa 10:11, 31.
Tsabta ta Zahiri na Gabatar da Mu
9, 10. (a) Me ya sa tsabta ta zahiri take da muhimmanci ga Kiristoci? (b) Wane furci sau da yawa aka yi game da manyan taro na Shaidun Jehovah?
9 Tsabta ta zahiri har ila muhimmin ɓangare ne a bauta ta gaskiya? Yayin da tsabta ta zahiri kaɗai ba ta mai da mutum mai bauta wa Allah da gaskiya, ya dace mai bauta ta gaskiya ya kasance da tsabta a zahiri yadda yanayinsa ya ƙyale. Musamman ma yau, da mutane da yawa ba sa mai da hankali ga tsara kansu, adonsu, ko mahallinsu da tsabta, waɗanda suke yi sau da yawa mutane gewaye da su suna lura. Wannan zai iya kai ga sakamako mai kyau, yadda Bulus ya gaya wa Kiristocin Koranti: “Kada mu bada dalilin tuntuɓe cikin kome, domin kada a yi zargin hidimarmu; amma cikin kowacce matsala mu koɗa kanmu masu-hidimar Allah.”—2 Korinthiyawa 6:3, 4.
10 A kai a kai, manyan ma’aikata sun yaba wa Shaidun Jehovah don tsabtarsu, tsari, da halaye masu kyau, da ake gani musamman a manyan taronsu. Alal misali, game da taro da aka yi a yankin Savona, a Italiya, jaridar La Stampa ta ce: “Abin da ake gani da farko yayin da mutum yake zagaya wurin shi ne tsabta da tsari na mutanen da suke amfani da su.” Bayan wani taro na Shaidun a filin wasa a São Paulo, Brazil, wani ma’aikaci na filin wasa ya gaya wa shugaban ’yan shara: “Daga yanzu muna son a share filin wasan yadda Shaidun Jehovah suka yi.” Wani ma’aikaci a wannan filin wasan ya ce: “Sa’ad da Shaidun Jehovah suke son su yi hayar wurin wasan, damuwarmu kwanan da za su yi amfani da wurin ne kawai. Ba abin da ya dame mu.”
11, 12. (a) Wace ƙa’ida ta Littafi Mai Tsarki ya kamata mu tuna da ita yayin da ya zo ga tsabta? (b) Waɗanne tambayoyi za a iya yi game da halinmu da hanyar rayuwa?
11 Idan tsabta da tsari a wurin da muke bauta za ta iya kawo wa Allah da muke bauta wa yabo, babu shakka nuna wannan halaye a rayuwarmu na da muhimmanci. Amma, a cikin gidanmu, za mu ji muna da ikon mu ƙyale kuma mu aikata yadda muke so. Game da sa tufafi da yin ado, hakika muna da ’yancin zaɓan abin da muke so kuma abin da ya fi mana kyau! Duk da haka, duka wannan ’yanci na da iyaka. Ka tuna cewa a tattauna zaɓen mutum ya ci wani irin abinci, Bulus ya yi wa ’yan’uwa Kiristoci gargaɗi: “Amma ku yi hankali kada wannan iko naku ya zama abin tuntuɓe ga raunana.” Sai ya faɗi ƙa’ida mai kyau: “Abu duka halal ne; amma ba dukan abu ya dace ba. Abu duka halal ne; amma ba dukan abu ne ya ke gini ba.” (1 Korinthiyawa 8:9; 10:23) Ta yaya gargaɗin Bulus ya shafe mu a batun tsabta?
12 Daidai ne mutane su zaci cewa mai hidimar Allah ya kamata ya kasance da tsabta a hanyar rayuwarsa. Saboda haka, ya kamata mu tabbata cewa yadda gidanmu yake da mahalli ba su janye hankalin abin da muke da’awa ba, wato, masu hidimar Kalmar Allah. Wane irin wa’azi, gidanmu yake yi game da mu da imaninmu? Yana nuna muna son mu rayu cikin sabuwar duniya ta adalci mai tsabta da aka tsara sosai, wadda muke gaya wa wasu game da ita? (2 Bitrus 3:13) Hakanan ma, kamaninmu na zahiri—ko lokacin hutu ko a hidima—zai iya ƙara ko rage son saƙo da muke wa’azinsa. Alal misali, ka lura da wannan kalamin manema labarai a Mexico: “Hakika matasa suna da yawa tsakanin Shaidun Jehovah, abin da ya fita sarai askinsu, tsabta, da adonsu da kyau.” Abin farin ciki ne mu kasance da irin wannan matasa a tsakaninmu!
13. Menene za mu yi don mu tabbata cewa duka fannin rayuwarmu ta yau da kullum na da tsabta kuma da tsari?
13 Hakika, tabbata cewa jikinmu, kayanmu, da gidanmu koyaushe suna da tsabta kuma an tsara sosai ba shi da sauƙi. Abin da ake bukata, ba yawan kaya masu tsada ba, amma shiri mai kyau da ƙoƙari. Dole a keɓe lokaci don wanka, wanki, tsabtace gida, wanke mota, da sauransu. Shagala cikin hidima, halartar taro, nazari na kanmu—ƙari ga kula da wasu hakki na rayuwar yau da kullum—ba dalilin hana mu tsabta kuma kasance da amincewa a gaban Allah da mutane ba. Ƙa’ida da aka sani na cewa “ga kowane abu akwai nasa kwanaki” ta shafi wannan fannin rayuwarmu.—Mai-Wa’azi 3:1.
Zuciya Marasa Aibi
14. Me ya sa za a ce tsabta ta ɗabi’a da ta ruhaniya sun fi tsabta ta zahiri muhimmanci?
14 Yadda yake da muhimmanci a mai da hankali ga tsabta ta zahiri, ya fi ma muhimmanci a damu da tsabta ta ɗabi’a da ta ruhaniya. Mun zo ga wannan ta tuna cewa Jehovah ya ƙi al’umma ta Isra’ila, ba domin ba sa tsabta a zahiri ba, amma domin sun kasance da ƙazanta a ɗabi’a da ruhaniya. Ta wurin annabi Ishaya, Jehovah ya gaya musu cewa domin su “al’umma mai-zunubi, dangi labtace da kayan laifi,” hadayunsu, kiyaye sabuwar wata da assabaci, hakika, addu’o’insu ya zama abin nauyaya a gare shi. Menene ya kamata su yi su sake samun tagomashin Allah? Jehovah ya ce: “Ku yi wanka, ku tsabtata; ku kawarda muguntar ayyukanku daga gaban idanuna: ku bar yin mugunta.”—Ishaya 1:4, 11-16.
15, 16. Menene Yesu ya ce yake ƙazantar da mutum, kuma ta yaya za mu amfana daga kalmomin Yesu?
15 Don mu ƙara fahimtar muhimmancin tsabta ta ɗabi’a da na ruhaniya, yi la’akari da abin da Yesu ya faɗa sa’ad da Farisawa da marubuta suka yi da’awa cewa almajiransa ba su da tsabta domin ba su wanke hannunsu ba kafin su ci abinci. Yesu ya yi musu gyara ta wajen cewa: “Abin da ya shiga ta baki, ba shi ne ya kan ƙazantadda mutum ba; amma abin da ke fitowa daga baki, shi ke ƙazantadda mutum.” Yesu ya yi bayani: “Abubuwan da ke fita daga baki, daga zuciya su ke fitowa; su ne masu ƙazantadda mutum. Gama daga cikin zuciya miyagun tunani ke fitowa, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar zur, alfasha: su ne masu ƙazantadda mutum: amma ci da hannuwa marasa-wanki ba shi ƙazantadda mutum ba.”—Matta 15:18-20.
16 Menene za mu koya daga kalmomin Yesu? Yesu yana nuna cewa mugunta, lalata, da ayyuka marasa tsabta suna fitowa daga saƙar zuciya mai mugunta, lalata da rashin tsabta. Almajiri Yaƙubu ya ce, “kowanne mutum ya jarabtu, sa’anda sha’awatasa ta janye shi, ta yi masa tarko.” (Yaƙub 1:14, 15) Da haka, idan ba ma son mu faɗa cikin zunubi mai tsanani da Yesu ya kwatanta, dole mu cire gabaki ɗaya kuma kada mu ƙyale zuciyarmu ta kasance da irin waɗannan abubuwa. Wannan yana nufin mu mai da hankali game da abin da muke karantawa, muke kallo, kuma wanda muke sauraro. A yau, cikin larurar fasaha, kamfanonin nishaɗi da na talla suna fitowa da kaɗe-kaɗe da yawa da siffofi da suke biyan bukatar sha’awa ta jiki. Ya kamata mu ƙuduri aniyar kada mu ƙyale irin wannan ra’ayoyi su kasance cikin zukatanmu. Abu na musamman don mu faranta wa Allah rai kuma ya amince da mu, dole ne mu ci gaba da kasancewa a farke don mu riƙe zukata masu tsabta marasa aibi.—Misalai 4:23.
An Tsabtacce Mu don Ayyuka Masu Kyau
17. Me ya sa Jehovah ya kawo mutanensa cikin yanayi mai tsabta?
17 Gata ce mai tamani kuma kāriya ce da taimakon Jehovah, za mu more matsayi mai tsabta a gabansa. (2 Korinthiyawa 6:14-18) Duk da haka, mun fahimta cewa Jehovah ya kawo mutanensa cikin yanayi mai tsabta don takamaiman nufi. Bulus ya gaya wa Titus cewa Kristi Yesu “Ya bada kansa dominmu, domin shi fanshe mu daga dukan zunubi, shi tsarkake wa kansa jama’a su zama abin mulkinsa, masu-himman nagargarun ayyuka.” (Titus 2:14) Mutane da aka tsabtacce, a waɗanne ayyuka ya kamata mu kasance da himma?
18. Ta yaya za mu nuna cewa muna himma don ayyuka masu kyau?
18 Abu na farko duka shi ne, ya kamata mu mazakuta kanmu a shelar bishara na Mulkin Allah. (Matta 24:14) Ta yin haka, muna ba mutane ko’ina begen rayuwa har abada a duniya da za ta kasance da ’yancin ƙazanta kowacce iri. (2 Bitrus 3:13) Ayyukanmu masu kyau ya ƙunshi nuna ɗiyan ruhun Allah a rayuwarmu na yau da kullum, da haka muna ɗaukaka Ubanmu na samaniya. (Galatiyawa 5:22, 23; 1 Bitrus 2:12) Kuma ba ma manta da waɗanda ba sa cikin gaskiya da za su sha wahalar tsarar bala’i ko kuma masifu na mutane. Muna tuna da gargaɗin Bulus: “Yayinda mu ke da dama fa, bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda su ke cikin iyalin imani.” (Galatiyawa 6:10) Irin wannan ayyuka, da ake yi daga zuciya mai tsabta da tsarkakken nufi, na faranta wa Allah rai.—1 Timothawus 1:5.
19. Wace albarka ke jiranmu idan mun ci gaba da riƙe ɗabi’a mai girma na tsabta—a zahiri, a ɗabi’a, da kuma a ruhaniya?
19 Da yake mu bayin Maɗaukaki ne, muna biyayya da kalmomin Bulus: “Ina roƙonku fa, ’yan’uwa, bisa ga jiyejiyenƙai na Allah, ku miƙa jikunanku hadaya mai-rai mai-tsarki, abin karɓa ga Allah, bautarku mai-ruhaniya ke nan.” (Romawa 12:1) Bari mu ci gaba da riƙe gatar zama tsabtattu na Jehovah da tamani kuma mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu riƙe mizani mai girma na tsabta a zahiri, a ɗabi’a da ruhaniya. Yin haka zai kawo mana daraja da gamsuwa ba yanzu kaɗai ba amma zaton ganin “al’amura na [dā]”—mugun zamani da ya ƙazanta—ya shuɗe yayin da Allah ‘na sabonta dukan abubuwa.’—Ru’ya ta Yohanna 21:4, 5.
Ka Tuna?
• Me ya sa aka ba Isra’ilawa dokoki da yawa a kan tsabta?
• Ta yaya tsabta ta zahiri take inganta saƙon da muke wa’azinsa?
• Me ya sa tsabta na ɗabi’a da na ruhaniya suka fi ta zahiri muhimmanci?
• Ta yaya za mu nuna cewa mu mutane ne “masu-himman nagargarun ayyuka”?
[Hotuna a shafi na 29]
Tsabta na zahiri na sa a ƙara son saƙon da muke wa’azinsa
[Hoto a shafi na 30]
Yesu ya yi gargaɗi cewa mugun tunani na kai wa ga miyagun ayyuka
[Hotuna a shafi na 31]
Tun da mutane ne masu tsabta, Shaidun Jehovah suna da himma don ayyuka masu kyau