Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • jt pp. 15-18
  • Bisharar da Suke So Ka Ji

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bisharar da Suke So Ka Ji
  • Shaidun Jehovah Su Wanene ne Su
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ALBARKA TA DUNIYA A ƘARƘASHIN MULKIN
  • Sashe na 9—Yadda Muka Sani Muna Cikin “Kwanaki Na Ƙarshe”
    Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
  • Mulkin “da ba Za a Rushe Shi ba Daɗai”
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Menene Dukan Waɗannan Abubuwa Ke Nufi?
    Ka Zauna A Faɗake!
  • Menene Mulkin Allah?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Dubi Ƙari
Shaidun Jehovah Su Wanene ne Su
jt pp. 15-18

Bisharar da Suke So Ka Ji

LOKACIN da Yesu yake duniya, almajiransa suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya: “Me ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?” Ya amsa da cewa za a yi yaƙe-yaƙe da zai ƙunshi al’ummai da yawa, za a yi yunwa, annoba, girgizar ƙasa, yawaita na mugunta, malaman ƙarya na addinai da suke yaudarar mutane da yawa, ƙiyayya da tsananta wa mabiyansa na gaskiya, kuma ƙaunar adalci na mutane da yawa za ta yi sanyi. Lokacin da waɗannan abubuwa za su soma faruwa, za su nuna cewa bayyanuwar Kristi mara ganuwa da kuma cewa Mulki na samaniya ya kusa. Wannan zai zama labari—labari mai daɗi! Sai Yesu ya daɗa waɗannan kalmomi da ke ƙari ne na alamun: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.”—Matta 24:3-14.

Abubuwa da suke faruwa a duniya a baya bayan nan ba su da kyau, amma abin da suke nunawa yana da kyau, watau, bayyanuwar Kristi. An soma ganin abubuwa da aka ambata a saman nan daga shekara ta 1914 da aka sanar a ko’ina! Ya nuna ƙarshen Lokatan Al’ummai da somawar lokacin barin sarautar mutane zuwan Sarautar Kristi (na Alif) na Shekara Dubu.

Zabura sura 110, aya ta 1 da ta 2 da kuma Ru’ya ta Yohanna 12:7-12 ne suka nuna cewa za a samu lokacin canji. A wurin an nuna cewa Kristi zai zauna a hannun dama na Allah a sama har sai lokacin da zai zama Sarki. Yaƙi a sama ya sa aka jefo Shaiɗan zuwa ƙasa, ya kawo wahala ga duniya, kuma Kristi zai yi sarauta a tsakanin magabtansa. Ƙarshen mugunta gaba ɗaya zai zo ta “ƙunci mai-girma,” da zai kammala a yaƙin Har–​magedon kuma Sarautar Kristi ta Shekara Dubu ta salama za ta biyo bayansa.—Matta 24:21, 33, 34; Ru’ya ta Yohanna 16:14-16.

Littafi Mai Tsarki ya ce, “Amma sai ka san wannan, cikin kwanaki na ƙarshe miyagun zamanu za su zo. Gama mutane za su zama masu-son kansu, masu-son kuɗi, masu-ruba, masu-girman kai, masu-zagi, marasa-bin iyaye, marasa-godiya, marasa-tsarki, marasa-ƙauna irin na tabi’a, masu-baƙar zuciya, masu-tsegumi, marasa-kamewa, masu-zafin hali, marasa-son nagarta, masu-cin amana, masu-taurin kai, masu-kumbura, ma-fiya son annashuwa da Allah; suna riƙe da surar ibada, amma sun musunci ikonta: daga wajen waɗannan kuma sai ka bijire.”—2 Timothawus 3:1-5.

Wasu za su iya musu cewa waɗannan abubuwa sun faru dā a tarihin ’yan Adam, amma gaskiyar ita ce ba kamar haka ba. Kamar yadda ’yan tarihi da ’yan sharhi suka faɗa, ba a taɓa samun lokaci kamar daga 1914 har yanzu a duniya ba. (Duba shafi na 7.) Wahalolin sun yi yawa sosai fiye da dā. Ƙari ga haka, game da wasu fannoni na alamar da Kristi ya bayar na kwanakin ƙarshe, ya kamata a yi la’akari da waɗannan lazun: An yi shelar bayyanuwar Kristi da Mulkinsa da ba a taɓa yi ba cikin tarihi a duka duniya. Tsanantawa don aikin wa’azi da ake yi bai kai zalunci da aka yi wa Shaidun Jehovah ba. An kashe ɗarurruwa da yawa a sansanin fursuna na Nazi. Har ila yau an hana aikin Shaidun Jehovah a wasu wurare, a wasu wurare kuma ana kama su, ana sa su a fursuna, an gana musu azaba, kuma ana kashe su. Duka waɗannan alama da Yesu ya bayar ne.

Kamar yadda aka annabta a Ru’ya ta Yohanna 11:18, ‘al’ummai sun yi fushi’ a kan Shaidun Jehovah masu aminci, wannan ya nuna cewa ‘fushin’ Jehovah zai zo kan waɗannan al’ummai. Wannan ayar kuma ta ce Allah zai “halaka waɗanda ke halaka duniya.” Ba lokaci a tarihin ’yan Adam da iyawar duniya na kiyaye rayuwa ta razana. Amma yanzu dabam ne! Masana kimiyya sun yi kashedi cewa idan mutane sun ci gaba da gurɓata duniya, ba za a iya zama a cikinta ba. Amma Jehovah ya “kamanta ta domin wurin zama,” zai halaka waɗanda suke gurɓata duniya kafin su gama lalata ta.—Ishaya 45:18.

ALBARKA TA DUNIYA A ƘARƘASHIN MULKIN

Tunani cewa mutane za su zauna a duniya a ƙarƙashin Mulkin Allah mai yiwuwa zai yi wa mutane da yawa wuya, waɗanda suka gaskata da Littafi Mai Tsarki da suke tunani cewa waɗanda suka tsira suna sama. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutane kalilan ne za su je sama, taro mai girma da suke da yawa ne za su zauna har abada a duniya. (Zabura 37:11, 29; Ru’ya ta Yohanna 7:9; 14:1-5) Wani annabci a littafin Daniel na Littafi Mai Tsarki ne ya nuna cewa Mulkin Allah a ƙarƙashin Kristi zai cika duniya kuma ya yi sarauta bisanta.

A wurin an nuna Mulkin Kristi cewa dutse ne da ya fito daga ikon mallakar Jehovah mai kama da babban dutse. Ya buga kuma halaka wata siffa da take wakiltar al’umman duniya masu iko, kuma “dutsen kuwa wanda ya buga siffan ya zama babban dutse; ya cika dukan duniya.” Annabcin ya ci gaba: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna kuwa, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautarsa kuwa ba za a bar ma wata al’umma ba; amma za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.”—Daniel 2:34, 35, 44.

Wannan Mulki da begen rai na har abada a cikin tsabtacaccen duniya mai kyau da ke da goyon baya na Nassi ne Shaidun Jehovah suke so su gaya maka. Miliyoyi da suke rayuwa yanzu da miliyoyi da yawa da suke cikin kabarinsu za su sami zarafi su zauna a wurin har abada. Sa’annan a ƙarƙashin Sarautar Kristi Yesu na Shekara Dubu, za a cim ma nufin Jehovah na asali, na halittar duniya da sa mutane biyu na farko a cikinta. Wannan Aljanna ta duniya ba za ta zama abin gumawa ba. Kamar yadda aka ba Adamu aiki a cikin gonar Adnin, haka ma za a ba mutane ayyuka masu wuya na kula da duniya da tsiro da dabbobi cikinta. “Za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu.”—Ishaya 65:22; Farawa 2:15.

Akwai nassosi da yawa da ke nuna yanayi da zai kasance lokacin da aka amsa addu’a da Yesu ya koya mana: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Matta 6:10) A yanzu ɗaya ya isa: “Na ji babbar murya kuwa daga cikin kursiyin, ta ce, Duba, mazaunin Allah yana wurin mutane, za ya zauna tare da su kuma, za su zama al’ummai nasa, Allah kuma da kansa za ya zauna tare da su, ya zama Allahnsu: Za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙinzuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe. Shi kuma wanda ke zaune bisa kursiyin ya ce, Duba, sabonta dukan abu ni ke yi. Ya ce kuma, Ka rubuta: gama waɗannan zantattuka masu-aminci ne masu-gaskiya.”—Ru’ya ta Yohanna 21:3-5.

[Bayanin da ke shafi na 15]

“Miyagun zamanu,”

AMMA “sa’annan matuƙa za ta zo”

[Hoto a shafi na 18]

Netherlands

[Hoto a shafi na 18]

Nijeriya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba