Babi Na Bakwai
Abin da Muka Koya Daga Ƙyale Mugunta da Allah Ya Yi
1, 2. (a) Da Jehovah ya halaka ’yan tawayen a Adnin nan da nan, yaya wannan zai shafe mu? (b) Wane tanadi mai kyau ne Jehovah ya yi mana?
“KWANAKIN shekaru na raina kaɗanna ne miyagu ne kuwa,” in ji uban iyali Yakubu. (Farawa 47:9) Haka ma, Ayuba ya ce mutum “kwanakinsa kaɗanna ne, cike da wahala kuma.” (Ayuba 14:1) Yawancinmu mun sha wahala, mun ga rashin adalci, har da masifa. Amma, haihuwarmu ba rashin adalci ba ce daga Allah. Hakika, ba mu da kamiltaccen azanci da jiki da kuma gida na Aljanna da Adamu da Hauwa’u suke da shi ba a farko. Amma da a ce nan da nan Jehovah ya halaka su bayan sun yi tawaye fa? Da ba za a samu ciwo, azaba, ko mutuwa ba, haka ma da ba za a samu zuriyar bil Adam ba. Da ba a haife mu ba. Cikin jinƙai kuwa, Allah ya bai wa Adamu da Hauwa’u lokaci don su haifi ’ya’ya, ko da waɗannan sun gāji ajizanci. Ta wurin Kristi kuma, Jehovah ya yi mana tanadi mu sami abin da Adamu ya ɓatar—rai na har abada a aljanna a duniya.—Yohanna 10:10; Romawa 5:12.
2 Abin ƙarfafa ne mu kasance da begen rayuwa har abada cikin sabuwar duniya a cikin Aljanna, inda ba za mu yi ciwo ba, baƙin ciki, azaba, da kuma mutuwa, har ma babu miyagu! (Misalai 2:21, 22; Ru’ya ta Yohanna 21:4, 5) Amma daga labarin Littafi Mai Tsarki, mun koyi cewa ko da cetonmu yana da muhimmanci a gare mu da kuma ga Jehovah, akwai abu mafi muhimmanci da wannan ya shafa.
Domin Sunansa Mai Girma
3. Menene cika nufin Jehovah ya ƙunsa game da duniya da kuma bil Adam?
3 Cika nufinsa game da duniya da kuma bil Adam ya shafi sunan Allah. Sunan nan, Jehovah, yana nufin “Yakan Sa Ya Kasance.” Domin haka, sunansa ya ƙunshi halinsa na Mamallakin Dukan Halitta, Mai Nufi, kuma Allah mai gaskiya. Domin matsayin Jehovah, salama da lafiyar dukan waɗanda ke cikin sararin samaniya sun dangana ga sunansa da kuma abin da sunan ya ƙunsa cewa duka su yi masa biyayya.
4. Menene ke ƙunshe cikin nufin Jehovah ga duniya?
4 Bayan ya halicci Adamu da Hauwa’u, Jehovah ya ba su aikin yi. Ya bayyana sarai cewa nufinsa ba kawai domin a mamaye dukan duniya ba—a faɗaɗa iyakar Aljanna—amma don su cika ta da ’ya’yansu. (Farawa 1:28) Wannan nufin zai kasa cika ne domin zunubinsu? Lallai zai zama zargi ne ga maɗaukaki Jehovah idan ya kasa cika nufinsa ga wannan duniyar da kuma ga bil Adam!
5. (a) Da mutane na farko sun ci daga itacen sanin nagarta da mugunta, yaushe za su mutu? (b) Ta yaya Jehovah ya cika kalmarsa a Farawa 2:17 wajen la’akari da nufinsa game da duniya?
5 Jehovah ya gargaɗi Adamu da Hauwa’u cewa idan sun yi rashin biyayya kuma suka ci daga itacen sanin nagarta da mugunta, za su mutu “cikin rana da” suka ci. (Farawa 2:17) Kamar yadda ya ce, Jehovah ya yi musu hisabi a ranar da suka yi zunubi kuma ya yanke musu hukuncin kisa. A ra’ayin Allah, Adamu da Hauwa’u sun mutu a ranar. Amma, domin ya cika nufinsa game da duniya, Jehovah ya ƙyale su su samu iyali kafin su mutu a zahiri. Bugu da ƙari, da yake shekara 1,000 ga Allah kamar rana guda ce, sa’ad da Adamu ya mutu shekararsa 930, cikin “kwana” guda ne. (2 Bitrus 3:8; Farawa 5:3-5) Ta haka, aka daraja gaskiyar Jehovah game da lokacin da zai zartar da hukuncinsa, kuma mutuwarsu ba ta gurguntar da nufinsa game da duniya ba. Amma an ƙyale mutane ajizai, har da miyagu su ci gaba da rayuwa na ɗan lokaci.
6, 7. (a) In ji Fitowa 9:15, 16, me ya sa Jehovah ya ƙyale miyagu su ci gaba na ɗan lokaci? (b) Game da Fir’auna, yaya Jehovah ya nuna ikonsa, kuma ta yaya aka sanar da Sunansa? (c) Menene zai faru sa’ad da wannan mugun zamani ya ƙare?
6 Abin da Jehovah ya gaya wa sarkin Masar a zamanin Musa ya daɗa nuna abin da ya sa Allah ya ƙyale miyagu su ci gaba. Lokacin da Fir’auna ya hana ’ya’yan Isra’ila fitowa daga ƙasar Masar, Jehovah bai halaka shi nan da nan ba. An aika annoba goma bisa ƙasar, yana nuna ikon Jehovah a hanyoyi na ban mamaki. Da yake ba da gargaɗi a kan annoba ta bakwai, Jehovah ya gaya wa Fir’auna cewa da Ya share Fir’auna da mutanensa nan da nan daga doron ƙasa. “Amma hakika,” in ji Jehovah, “saboda wannan na tsayadda kai, domin in gwada maka ikona, a sanarda sunana kuma cikin dukan duniya.”—Fitowa 9:15, 16.
7 Hakika, yayin da Jehovah ya ceci Isra’ilawa, aka ji sunansa a duk faɗin duniya. (Joshua 2:1, 9-11) A yau, kusan shekara 3,500 ke nan, ba a manta da abin da ya yi ba a can da. Ba kawai an sanar da sunan Jehovah ba, amma an sanar da gaskiya game da Wanda yake amsa sunan nan. Wannan ya tabbatar da cewa Jehovah yana da suna mai kyau, Allah ne wanda yake cika alkawuransa kuma wanda yake tashiwa tsaye domin bayinsa. (Joshua 23:14) Ya nuna cewa saboda maɗaukakin ikonsa, babu abin da zai hana nufinsa. (Ishaya 14:24, 27) Saboda haka, za mu tabbata cewa zai aikata abin da ya kamata domin amintattun bayinsa ya halaka dukan waɗanda suke na Shaiɗan. Ba za a taɓa manta maɗaukakin ikon nan da kuma darajar da za ta kawo ga sunan Jehovah ba. Fa’idodin ba za su ƙare ba.—Ezekiel 38:23; Ru’ya ta Yohanna 19:1, 2.
‘Ya Zurfin Hikimar Allah!’
8. Waɗanne abubuwa ne Bulus ya aririce mu mu bincika?
8 A wasiƙarsa ga Romawa, manzo Bulus ya yi tambaya: “Da rashin adalci tare da Allah?” Sai ya amsa da babbar murya: “Daɗai!” Ya nanata jinƙan Allah kuma ya yi nuni ga abin da Jehovah ya ce game da dalilin ƙyale Fir’auna ya rayu na ɗan lokaci. Bulus ya sake nuna cewa mu kama muke da laka a hannun magini. Sai ya ce: “Ƙaƙa fa, idan Allah, da nufin ya gwada fushinsa, ya sanarda ikonsa kuma, da haƙuri mai-yawa ya jimre da tukwane na fushi shiryayyu ga halaka: domin kuma ya sanarda wadatar ɗaukakarsa bisa tukwane na jinƙai, waɗanda ya rigaya ya shirya su zuwa ɗaukaka, watau mu ne, waɗanda ya kira kuma, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba, amma daga cikin Al’ummai kuma?”—Romawa 9:14-24.
9. (a) Su wanene “tukwane na fushi shiryayyu ga halaka”? (b) Me ya sa Jehovah ya yi tsawon jimrewa ƙwarai ga ’yan hamayya, kuma ta yaya sakamakon zai zama albarka ga waɗanda suke ƙaunarsa?
9 Tun tawaye a Adnin, duk wanda ya yi hamayya da Jehovah da dokokinsa ya zama cikin “tukwane na fushi shiryayyu ga halaka.” Tun daga lokacin, Jehovah yana tsawon jimrewa. Miyagu sun yi wa hanyoyinsa ba’a, sun tsananta wa bayinsa, har ma sun kashe Ɗansa. Jehovah ya kame kai ƙwarai, wajen ƙyale isashen lokaci ga dukan halitta su ga mummunar sakamakon tawaye ga Allah da kuma sarautar ’yan Adam da ba ta dangana ba gare shi. Har ila, mutuwar Yesu ta yi tanadin ceto ga mutane masu biyayya kuma tana ‘kakkarya ayyukan Iblis.’—1 Yohanna 3:8; Ibraniyawa 2:14, 15.
10. Me ya sa Jehovah ya ƙyale miyagu cikin shekaru 1,900 da suka shige?
10 A cikin fiye da shekaru 1,900 tun tashin Yesu daga matattu, Jehovah ya sake ƙyale “tukwane na fushi,” yana jinkirin halaka su. Me ya sa? Domin yana ta shirya waɗanda za su yi tarayya da Yesu Kristi cikin Mulkinsa na samaniya. Adadinsu 144,000 ne, kuma su “tukwane na jinƙai” ne da manzo Bulus ya yi maganarsu. Da farko, an gayyaci mutane tsakanin Yahudawa su kasance cikin aji na masu zuwa sama. Daga baya aka gayyaci mutane daga Al’ummai. Babu ɗaya cikin waɗannan da Jehovah ya tilasta wa ya bauta masa. Amma a tsakanin waɗanda suka nuna godiyarsu ga tanadinsa na ƙauna, ya ba wasu cikinsu gata ta zama abokan sarauta da Ɗansa a Mulki na samaniya. An kusan gama shirya wannan aji na masu zuwa sama.—Luka 22:29; Ru’ya ta Yohanna 14:1-4.
11. (a) Wane rukuni ne ke amfana daga tsawon jimrewa na Jehovah? (b) Ta yaya matattu za su amfana?
11 Me za a ce game da mazauna duniya? Tsawon jimrewa na Jehovah ya sa ya yiwu a tara “taro mai-girma” daga cikin dukan al’ummai. Yanzu sun kai miliyoyi. Jehovah ya yi alkawari cewa wannan aji na duniya za su tsira a ƙarshen wannan zamani kuma su kasance da begen rai na har abada a cikin aljanna a duniya. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10; Zabura 37:29; Yohanna 10:16) A lokaci na Allah, za a ta da matattu da yawa kuma a ba su damar kasancewa talakawan Mulki na samaniya a duniya. Kalmar Allah ta annabta a Ayukan Manzanni 24:15: “Za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.”—Yohanna 5:28, 29.
12. (a) Menene muka koya game da Jehovah a yadda yake ƙyale mugunta? (b) Yaya kake ji game da yadda Jehovah ya bi da al’amuran nan?
12 Duk cikin wannan akwai wani rashin adalci ne? A’a, domin ta wurin kamewa daga halaka miyagu, ko kuma “tukwane na fushi,” Allah ya nuna jinƙai ga wasu cikin jituwa da nufinsa. Wannan ya nuna yadda yake cike da jinƙai da kuma ƙauna. Kuma, yadda muke da wannan zarafi na lura da nufinsa, muna ƙara koyo game da Jehovah kansa. Muna mamakin ɓangarorin mutuntakarsa da sun bayyana sarai—shari’arsa, jinƙansa, tsawon jimrewarsa, hikimarsa iri-iri. Hanyar hikima da Jehovah yake bi da wannan al’amari na ikon—ikonsa na sarauta—zai zama tabbaci na har abada ga gaskiyar cewa hanyarsa ta sarauta ce mafi kyau. Tare da manzo Bulus, muna cewa: “Ya zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa! ina misalin wuyan binciken shari’unsa, al’amuransa kuma sun fi gaban a bi sawu!”—Romawa 11:33.
Zarafi na Nuna Ibadarmu
13. Idan muka wahala, wane zarafi muke da shi, kuma me zai taimake mu mu mai da martani cikin hikima?
13 Bayin Allah da yawa suna cikin yanayi da ya ƙunshi wahala. Wahalarsu tana ci gaba domin har yanzu Allah bai halaka miyagu ba kuma bai maido da mutane ba kamar yadda aka annabta. Ya kamata wannan ya sa mu fusata ne? Ko kuwa za mu ɗauki yanayin nan zarafi ne na nuna cewa Iblis maƙaryaci ne? Za mu samu ƙarfin yin haka, idan mun tuna da wannan roƙo: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.” (Misalai 27:11) Shaiɗan, wanda yake zargin Jehovah, ya ce idan mutane sun yi hasarar dukiyarsu ko kuma sun wahala a jiki, za su ga laifin Allah, har su la’anta shi. (Ayuba 1:9-11; 2:4, 5) Muna sa Jehovah farin ciki yayin da, ta wurin amincinmu gare shi a cikin wahala, muna nuna cewa zargin ba gaskiya ba ce a zancenmu.
14. Idan mun dogara ga Jehovah yayin da muke cikin gwaji, waɗanne fa’idodi za mu samu?
14 Idan mun dogara ga Jehovah yayin da muke cikin gwaji, za mu koyi halaye masu tamani. Alal misali, ta wahalar da Yesu ya sha, ya “koya biyayya” a hanyar da bai taɓa fahimtarta ba dā. Mu ma za mu iya koyo daga gwajinmu da zai sa mu koyi tsawon jimrewa, jimiri, kuma mu ƙara fahimtar hanyoyin Jehovah.—Ibraniyawa 5:8, 9; 12:11; Yaƙub 1:2-4.
15. Yayin da muke jimre wa wahala, ta yaya za mu amfani wasu?
15 Wasu za su lura da abin da muke yi. Domin abin da muke ciki don ƙaunar adalci da muke yi, a kwana a tashi, wasunsu za su iya fahimta kuma su yi godiya game da waɗanda ke Kiristoci na gaskiya a yau. Ta wurin yin sujjada tare da mu, za su shiga matsayin samun rai na har abada. (Matta 25:34-36, 40, 46) Jehovah da Ɗansa suna son mutane su sami wannan zarafin.
16. Yaya ra’ayinmu game da wahalar da muke sha yake da nasaba da zancen haɗin kai?
16 Yana da kyau ƙwarai idan muka ɗauki yanayi masu wuya zarafi ne na nuna ibadarmu ga Jehovah kuma muka sa hannu wajen cim ma nufinsa! Yin haka zai ba da tabbaci cewa muna ci gaba zuwa haɗin kai da Allah da kuma Kristi. Yesu ya yi addu’a ga Jehovah domin dukan Kiristoci na gaskiya, yana cewa: “Kuma ba domin waɗannan [almajiransa na lokacin] kaɗai ni ke yin addu’a ba, amma domin waɗancan kuma da ke bada gaskiya gareni ta wurin maganarsu: domin su duka su zama ɗaya; kamar yadda kai, Uba, kana cikina, ni kuma a cikinka, domin su kuma su zama cikinmu.”—Yohanna 17:20, 21.
17. Wane tabbaci za mu kasance da shi idan muna da aminci ga Jehovah?
17 Idan muna da aminci ga Jehovah, zai ba mu lada sosai. Kalmarsa ta ce: “Ku kahu yadda ba ku kawuwa, kullum kuna yawaita cikin aikin Ubangiji, da shi ke kun sani wahalarku ba banza ta ke ba cikin Ubangiji.” (1 Korinthiyawa 15:58) Kuma ta ce: “Allah ba mara-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa.” (Ibraniyawa 6:10) Yaƙub 5:11 ta ce: “Duba, waɗanda suka jimre muna ce da su masu-albarka: kun ji labarin jimrewar Ayuba, kun ga ƙarkon Ubangiji kuma, Ubangiji da shi ke cike da tausayi, mai-jinƙai ne kuma.” Menene sakamakon haka ga Ayuba? “Ubangiji ya albar[ka]ci ƙarshen Ayuba, har ya fi farkonsa.” (Ayuba 42:10-16) Hakika, Jehovah “mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.” (Ibraniyawa 11:6) Lallai, muna zuba ido ga—rai na har abada a aljanna a duniya!
18. A ƙarshe me zai faru da duk wani tunanin azaba da muke da shi?
18 Mulkin Allah zai kawar da dukan lahani da aka yi wa iyalin bil Adam na dubban shekaru da suka shige. Farin ciki a lokacin zai fi wahala da muke sha a yanzu. Ba za mu damu ba game da wasu tunani na mugunta da muka sha. Tunani masu kyau da ayyuka da za su zama yanayi na yau da kullum cikin sabuwar duniya a sannu sannu za su kawar da dukan tunani na azaba. Jehovah ya ce: “Sababbin sammai [sabuwar gwamnati ta samaniya a kan mutane] da sabuwar duniya [jam’iyyar mutane masu adalci] ni ke halitta: ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba. Amma sai ku yi murna ku yi farinciki har abada da abin da ni ke halittawa.” I, a cikin sabuwar duniya ta Jehovah, masu adalci za su iya cewa: “Dukan duniya tana zaune a huce, da rai a kwance; fashe da rerawa su ke yi.”—Ishaya 14:7; 65:17, 18.
Maimaita Abin da Aka Tattauna
• Ko da ya ƙyale mugunta, yaya Jehovah ya nuna daraja sosai ga sunansa?
• Ta yaya yadda Allah ya ƙyale “tukwane na fushi” ya sa jinƙansa ya kai gare mu?
• Menene za mu yi ƙoƙari mu fahimta da ke cikin wahalar da muke sha?
[Hotuna a shafi na 67]
Jehovah ya “albar[ka]ci ƙarshen Ayuba, har ya fi farkonsa”