Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wt babi na 8 pp. 70-78
  • ‘Kokawa da Miyagun Ruhohi’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Kokawa da Miyagun Ruhohi’
  • Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Masu Sarautar Duniya a Sammai
  • Dabarun Yaudara na Mugun
  • Shiryayyu don Yin Nasara
  • Ta Yaya Za Mu Tsayayya Wa Aljanu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ka Yi Tsayayya da Shaidan da Kissoshinsa
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • “Ku Ƙarfafa Ga Ubangiji”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Wanene Ke Mulkin Duniya Da Gaske?
    Wanene Ke Mulkin Duniya Da Gaske?
Dubi Ƙari
Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
wt babi na 8 pp. 70-78

Babi Na Takwas

‘Kokawa da Miyagun Ruhohi’

1. Me ya sa musamman muke so mu san ayyuka na miyagun ruhohi?

MUTANE da yawa suna ba’a ga ra’ayin cewa da akwai miyagun ruhohi. Amma ba abin wasa ba ne. Ko mutane sun yarda ko ba su yarda ba, akwai miyagun ruhohi, kuma suna ƙoƙarin matsa wa kowa. Har da masu bauta wa Jehovah ma ba su bari ba. Hakika, sune ma ainihin ake fako. Manzo Bulus ya faɗakar da mu game da haka, yana cewa: “Kokawarmu ba da nama da jini ta ke ba, amma da mulkoki [da ba a gani], da ikoki, da mahukuntan wannan zamani mai-duhu, da rundunai masu-ruhaniya na mugunta cikin sammai.” (Afisawa 6:12) Matsawa da miyagun ruhohi suke yi a zamaninmu ya fi tsanani ƙwarai domin an jefo Shaiɗan daga sama kuma yana fushi, domin ya sani cewa lokacinsa gajere ne.—Ru’ya ta Yohanna 12:12.

2. Ta yaya zai yiwu mu yi nasara a kokawa da ruhohi da suka fi mutane?

2 Zai yiwu ne a yi nasara a kokawa da ruhohi? I, amma fa ta wurin dogara gabaki ɗaya ga Jehovah. Dole ne mu saurare shi kuma mu yi biyayya da Kalmarsa. Ta haka, za mu guje ma lahani na jiki, ɗabi’a, da kuma na sosuwar zuciya da waɗanda suke ƙarƙashin ikon Shaiɗan suke sha.—Yaƙub 4:7.

Masu Sarautar Duniya a Sammai

3. Su wanene Shaiɗan yake hamayya ta ƙwarai da su, kuma ta yaya?

3 Jehovah ya kwatanta mana sarai yanayin duniya daga wajensa mai ɗaukaka can a sammai. Ya ba manzo Yohanna wahayi da aka nuna Shaiɗan ‘babban jan dodo.’ A shirye yake ya halaka, idan ya yiwu, Mulkin Allah na Almasihu da zarar ya fara a shekara ta 1914 a sama. Da ya kasa yin wannan, Shaiɗan ya aza hamayya ta ƙwarai da wakilan Mulkin na duniya. (Ru’ya ta Yohanna 12:3, 4, 13, 17) Ta yaya ne Shaiɗan zai yi wannan yaƙin? Ta wurin wakilansa mutane.

4. Wanene tushen ikon gwamnatin bil Adam, kuma yaya muka san haka?

4 Aka kuma nuna wa Yohanna dabbar daji mai kai bakwai da ƙahoni goma, dabba mai iko “bisa kowace kabila da al’umma da kowane harshe da iri.” Dabbar tana wakiltar tsarin siyasa na dukan duniya. Aka gaya wa Yohanna cewa ‘dodon [Shaiɗan Iblis] kuma ya ba shi ikonsa da kursiyinsa da hukunci mai-girma.’ (Ru’ya ta Yohanna 13:1, 2, 7) Hakika, Shaiɗan ne tushen iko da hukunci na gwamnatin bil Adam. Saboda haka, yadda manzo Bulus ya rubuta, “mahukuntan wannan zamani” na gaske sune “masu-ruhaniya na mugunta cikin sammai,” da suke sarrafa gwamnatin bil Adam. Dukan wanda yake son ya bauta wa Jehovah na bukatar fahimtar muhimmancin wannan sosai.—Luka 4:5, 6.

5. Zuwa ga menene ake tattara masarauta na siyasa a yanzu?

5 Ko da yake shugabannan siyasa da yawa suna da’awar suna bin addini, babu al’ummar da ta miƙa kai ga sarautar Jehovah ko kuma na Yesu Kristi, Sarkinsa da aka naɗa. Duka suna kokawa sosai su riƙe nasu iko. A yau, kamar yadda Ru’ya ta Yohanna ta nuna, “ruhohin aljanu” suna tattara sarakunan duniya zuwa ga “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka” a Armageddon.—Ru’ya ta Yohanna 16:13, 14, 16; 19:17-19.

6. Me ya sa ake bukatar mai da hankali sosai don kada a ruɗe mu zuwa ba da goyon baya ga zamanin Shaiɗan?

6 Kowacce rana, jayayyar siyasa, ta zaman jama’a, ta tattalin arziki, da kuma ta addini suna ragargaje iyalan duniya. A cikin irin wannan jayayyar, yana da sauƙi mutane su ba da ɗaurin gindi—ta maganar baki ko kuma ta ayyuka—ga al’umma, yare, harsuna, ko kuma wasu rukunin mutane da suke a ware. Ko ma jayayyar ba ta shafi mutanen ba kai tsaye, sau da yawa suna ba da ɗaurin gindi ga ɓangare ɗaya fiye da ɗayan. Ko da wane mutum da kuma tafarki suka zaɓa, wane ne ainihi suke goya masa baya? Littafi Mai Tsarki a fili ya ce: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) To, ta yaya mutum zai guje wa ruɗewa tare da sauran mutane? Sai ta wurin ba da cikakken goyon baya ga Mulkin Allah da kuma ta wurin riƙe aminci na tsakatsakanci game da jayayya ta wannan duniyar.—Yohanna 17:15, 16.

Dabarun Yaudara na Mugun

7. Yaya haziƙancin Shaiɗan yake bayyane a yadda yake amfani da addinin ƙarya?

7 Duk cikin tarihi, Shaiɗan ya yi amfani da tsanantawa ta maganar baki da ta jiki ya rinjayi mutane daga bauta ta gaskiya. Ya kuma yi amfani da dabara—wayo da kuma yaudara. Cikin haziƙancinsa ya saka mutane da yawa cikin duhu ta addini na ƙarya, ya sa suna tunanin cewa suna bauta wa Allah. Domin ba su da cikakken sanin Allah da kuma ƙaunar gaskiya, ayyuka na asiri, da ayyuka masu sosa zuciya na addini ko kuma ayyuka na ban mamaki masu burgewa. (2 Tassalunikawa 2:9, 10) Amma an gargaɗe mu cewa har a cikin waɗanda suke bauta ta gaskiya dā, “waɗansu za su ridda . . . suna maida hankali ga ruhohi na ruɗani da koyarwar aljanu.” (1 Timothawus 4:1) Ta yaya hakan zai faru?

8. Ta yaya ne Shaiɗan zai jawo mu cikin addinin ƙarya ko ma idan dā muna bauta wa Jehovah?

8 Da wayo, Iblis yana amfani da kumamancinmu. Har ila muna jin tsoron mutum ne? Idan haka ne, za mu iya fāɗa wa matsawa daga dangi ko maƙwabta don mu sa hannu a ayyukan da tushensu daga addinin ƙarya ne. Mu masu fahariya ne? Idan haka ne, za mu iya yin fushi idan aka yi mana gargaɗi ko kuma idan wasu ba su yarda da ra’ayinmu ba. (Misalai 15:10; 29:25; 1 Timothawus 6:3, 4) Maimakon mu gyara ra’ayinmu ya yi daidai da misalin Kristi, ƙila za mu so mu juya ga waɗanda za su ‘sosa mana kunnuwa’ ta wajen cewa karatun Littafi Mai Tsarki kawai da rayuwa mai kyau sun isa. (2 Timothawus 4:3) Ko muna bin wasu rukunin addini ko kuma muna da namu addinin bai dame Shaiɗan ba, muddin dai ba ma bauta wa Jehovah a hanyar da ya ce cikin Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa bukatarsa ta biya.

9. Ta yaya Shaiɗan yake yaudara da jima’i ya cika nufinsa?

9 Shaiɗan kuma yana ruɗin mutane su cika sha’awarsu ta mummunar hanya. Ya yi hakan ta wajen jima’i. A yin banza da ɗabi’ar Littafi Mai Tsarki, mutane da yawa cikin duniya suna ɗaukan yin jima’i tsakanin waɗanda ba su yi aure ba nishaɗi ne ko kuma su nuna cewa sun kai mutum. Waɗanda suka yi aure kuma fa? Da yawa suna yin zina. Har inda babu rashin aminci cikin aurensu, da yawa suna kashe aure ko su rabu don su koma suna zaman daduro. Yadda Shaiɗan yake zuwa a ɓoye domin ya jarrabi mutane su yi rayuwar annashuwa yanzu, yana sa su yi banza da mummunar sakamako mai daɗewa da zai jawo ba ga kansu da kuma wasu kawai ba amma kuma har da dangantakarsu da Jehovah da kuma Ɗansa.—1 Korinthiyawa 6:9, 10; Galatiyawa 6:7, 8.

10. Ta wurin menene Shaiɗan yake ƙoƙarin ya lalata mana hankali game da lalata da kuma nuna ƙarfi?

10 Wata sha’awa kuma ita ce ta nishaɗi. Idan mai kyau ne, yakan wartsake jiki, hankali, da kuma sosuwar zuciya. Amma yaya za mu yi yayin da Shaiɗan cikin wayo ya yi amfani da lokatan hutun nan don ya sa mu rabu da tunanin Allah? Alal misali, mun sani cewa Jehovah yana ƙyamar lalata da nuna ƙarfi. Yayin da siliman, telibijin, ko wasanni a babban ɗakin wasa ke ɗauke da waɗannan, za mu zauna ne mu ci gaba da kallo? Ka kuma tuna cewa, Shaiɗan zai sa waɗannan abubuwan su daɗa muni idan lokacin da za a halaka shi ya yi kusa, tun da “miyagun mutane da masu-hila za su daɗa mugunta gaba gaba, suna ruɗi, ana ruɗinsu.” (2 Timothawus 3:13) Saboda haka, kullum ya kamata mu kasance a farke game da dabarun Shaiɗan.—Farawa 6:13; Zabura 11:5; Romawa 1:24-32.

11. A waɗanne hanyoyi ne wanda ma ya san gaskiya game da sihiri zai iya ruɗewa idan bai mai da hankali ba?

11 Mun kuma sani cewa waɗanda suke da hannu cikin kowanne irin sihiri—duba, maita, ko kuma ƙoƙarin yin magana da matattu—abin ƙyama ne ga Jehovah. (Kubawar Shari’a 18:10-12) Tunawa da wannan, kada mu yi tunanin zuwa wajen boka, kuma kada mu gayyace su zuwa gidajenmu don su yi dabo. Amma za mu saurare su ne a telibijin ko Intane namu? Ko da yake ba za mu amince da magani daga wajen boka ba, to za mu ɗaura laya a hannun jariri, da tunanin cewa za ta tsare jaririn daga lahani? Da sanin cewa Littafi Mai Tsarki ya haramta jifa, za mu yarda ne wani mai yin haka ya mallaki zuciyarmu?—Galatiyawa 5:19-21.

12. (a) Ta yaya ake amfani da kaɗe-kaɗe a sa mu yi mummunar tunani da muka sani ba daidai ba ne? (b) Ta yaya adon mutum, yadda yake barin gashinsa, ko yadda yake magana zai nuna yadda yake sha’awar waɗanda yayin rayuwarsu Jehovah ba ya so? (c) Menene ake bukata a gare mu idan za mu guji fāɗawa cikin dabarun Shaiɗan?

12 Littafi Mai Tsarki ya ce kada ma a ambaci fasikanci da kowanne (irin ƙazanta don mummunar nufi) tsakaninmu. (Afisawa 5:3-5) Amma idan cikin waƙa ce, da ke da daɗi, da kiɗa mai daɗi fa? Za mu fara bin waƙar ce da take ɗaukaka jima’i ba tare da aure ba, yin amfani da miyagun ƙwayoyi, da wasu ayyukan zunubi? Ko kuma yayin da mun san cewa bai kamata mu yi koyi da hanyar rayuwa na mutane da suke irin abubuwan nan ba, muna nuna kanmu muna tare da su ne, muna yin koyi da adonsu, yadda suke barin gashinsu, ko kuma yadda suke magana? Duba yadda yake hanya ta ruɗu ƙwarai da Shaiɗan yake amfani da shi ya sa mutane su bi mummunar hanyar tunaninsa! (2 Korinthiyawa 4:3, 4) Don kada mu fāɗa ga munanan dabarunsa, dole ne mu guji komawa cikin duniya. Muna bukatar mu riƙa tuna waɗanda sune “mahukuntan duhun nan” kuma mu yi kokawa ta ƙwarai da rinjayarsu.—1 Bitrus 5:8.

Shiryayyu don Yin Nasara

13. Ta yaya zai yiwu waninmu, duk da ajizancinsa, zai iya nasara bisa duniyar da Shaiɗan ke sarauta?

13 Kafin mutuwarsa, Yesu ya gaya wa manzanninsa: “Ku yi farinciki, na yi nasara da duniya.” (Yohanna 16:33) Su ma za su iya zama masu nasara. Shekaru 60 daga baya, manzo Yohanna ya rubuta: “Wanene mai-nasara da duniya fa, sai shi wanda yana bada gaskiya Yesu Ɗan Allah ne?” (1 Yohanna 5:5) Irin bangaskiyar nan ta wajen biyayyarmu ce ga umarnan Yesu da kuma dogara a kan Kalmar Allah, yadda Yesu ma ya yi. Menene ake bukata? Mu kasance kusa da ikilisiya wadda shi ne Shugabanta. Yayin da muka yi kuskure, dole ne mu tuba kuma mu nemi gafara ta Allah ta wurin hadayar Yesu. Ta haka, duk da ajizancinmu da kurakure, mu ma za mu yi nasara.—Zabura 130:3, 4.

14. Ka karanta Afisawa 6:13-17, kuma ka yi amfani da tambayoyi da nassosi da aka tanadar cikin wannan izifi don tattauna amfani daga kowanne cikin makaman nan na ruhaniya.

14 Don mu yi nasara, muna bukatar mu sanya “dukan makamai na Allah,” kada mu bar wani. Sai ka buɗe Littafi Mai Tsarki naka zuwa Afisawa 6:13-17, kuma ka karanta kwatancin makaman. Sai kuma, ta wurin amsa tambayoyi na gaba, ka bincika yadda za ka amfana daga kāriyar kowanne cikin waɗannan makamai.

“Ɗaure gindinku da gaskiya”

Ko da ma mun san gaskiya, ta yaya nazari a kai a kai, yin bimbini a kan gaskiyar Littafi Mai Tsarki, da halartar taro za su kāre mu? (1 Korinthiyawa 10:12, 13; 2 Korinthiyawa 13:5; Filibbiyawa 4:8, 9)

“Sulke na adalci”

Mizanan adalci na wanene wannan? (Ru’ya ta Yohanna 15:3)

Ka ba da misalin yadda ƙin bin hanyoyin adalci na Jehovah ke barin mutum ga lahani na ruhaniya. (Kubawar Shari’a 7:3, 4; 1 Samu’ila 15:22, 23)

“Ɗaura ma sawayenku shirin bishara ta salama”

Me ya sa kāriya ce mu shagala wajen gaya wa mutane game da tanadin da Allah ya yi don salama? (Zabura 73:2, 3; Romawa 10:15; 1 Timothawus 5:13)

“Garkuwa ta bangaskiya”

Idan muna da bangaskiya da take kafe, me za mu yi a lokacin ƙoƙarce-ƙoƙarce a sa mu mu yi shakka ko mu tsorata? (2 Sarakuna 6:15-17; 2 Timothawus 1:12)

“Kwalkwali na ceto”

Ta yaya begen ceto ke taimakon mutum ya guje wa fāɗawa cikin tarko na damuwa ainu game da abin duniya? (1 Timothawus 6:7-10, 19)

“Takobin Ruhu”

Ga wa ya kamata mu dogara kullum yayin da muke kokawa game da ruhaniyarmu ko na wasu? (Zabura 119:98; Misalai 3:5, 6; Matta 4:3, 4)

Me kuma ke da muhimmanci a yin nasara a yaƙinmu na ruhaniya? Sau nawa za mu dinga amfani da su? Domin wa? (Afisawa 6:18, 19)

15. Ta yaya za mu riƙa kai farmaki a wannan yaƙi na ruhaniya?

15 Tun da mu sojojin Kristi ne, muna cikin runduna mai girma da ke yin yaƙi na ruhaniya. Idan mun kasance a farke kuma mun yi amfani mai kyau da makamai na Allah, ba za mu mutu a wannan yaƙin ba. Maimakon haka, za mu kasance abin ƙarfafa ga ’yan’uwa bayin Allah. Za mu kasance a shirye kuma muna ɗokin kai farmaki, muna shelar bisharar Mulkin Almasihu na Allah, gwamnati ta samaniya da Shaiɗan yake hamayya da ita ƙwarai.

Maimaita Abin da Aka Tattauna

• Me ya sa masu bauta wa Jehovah suke riƙe cikakken aminci na tsakatsaki game da jayayya ta duniya?

• Waɗanne dabaru ne Shaiɗan yake amfani da su ya halaka ruhaniyar Kiristoci?

• Ta yaya makamai na ruhaniya da Allah ya yi tanadinsa ke kāre mu a yaƙi na ruhaniya?

[Hotuna a shafi na 76]

Ana tattara al’ummai zuwa Armageddon

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba