“Ku Ƙarfafa Ga Ubangiji”
“Ku ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa.”—AFISAWA 6:10.
1. (a) Wane yaƙi mai ban al’ajabi ne ya faru shekaru 3,000 da suka shige? (b) Me ya sa Dawuda ya ci nasara?
SHEKARU 3,000 da suka shige, wasu mayaƙa biyu abokan gāba da rundunarsu suka fuskanci juna a filin daga. Ƙaramin ciki, yaro ne makiyayi mai suna Dawuda. A gabansa kuwa ga Goliyat a tsaye mutum mai tsawo da ƙarfi na musamman. Rigar sulkensa na da nauyin kusan kilo 57, kuma yana ɗauke da babban māshi da takobi. Dawuda bai sa kayan yaƙi ba, kuma makamin da ke hannunsa majajjawa ce. Katon Bafilisten Goliyat ya ji haushi sa’ad da ya ga ɗan Isra’ila da ya zo ya yi yaƙi da shi ƙaramin yaro ne. (1 Sama’ila 17:42-44) ’Yan kallo a ɓangarori biyun, sun riga sun kammala abin da zai faru. Amma jarumi ba kullum yake cin nasara ba. (Mai Hadishi 9:11) Dawuda ya ci nasara ne domin ya yi faɗān da ƙarfin Jehovah. Ya ce: “yaƙi na Ubangiji ne.” Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara da Bafilisten.”—1 Sama’ila 17:47, 50.
2. Wane irin yaƙi ne Kiristoci suke yi?
2 Kiristoci ba sa yaƙi na zahiri. Ko da yake suna zaman lafiya da kowa, suna yaƙi na ruhaniya da kowane abokan gāba. (Romawa 12:18) A sura ta ƙarshe ta wasiƙarsa zuwa ga Afisawa, Bulus ya kwatanta yaƙin da ya shafi kowane Kirista. Ya rubuta: “Famanmu ba da ’yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama—masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu ke hannunsu.”—Afisawa 6:12.
3. In ji Afisawa 6:10, menene muke bukatar mu yi idan muna son mu ci nasara?
3 Shaiɗan da aljanunsa su ne “mugayen ruhohi,” da suke son su halaka dangantakarmu da Jehovah Allah. Muna cikin irin halin da Dawuda ya shiga tun da sun fi mu ƙarfi, kuma ba ma iya samun nasara sai idan mun dogara ga ƙarfin Allah. Hakika, Bulus ya aririce mu mu “ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa.” (Afisawa 6:10) Bayan ya gama ba da wannan shawarar, manzon ya kwatanta taimako na ruhaniya, da halaye na Kirista da za su taimaka mana mu ci nasara.—Afisawa 6:11-17.
4. Waɗanne muhimman darussa biyu ne za mu bincika a cikin wannan talifin?
4 Bari mu bincika abin da Nassosi ya ce game da ƙarfi da dabarun maƙiyinmu. Sa’an nan za mu bincika yadda za mu kāre kanmu. Idan muka bi umurnan Jehovah, muna da gaba gaɗin cewa maƙiyanmu ba za su ci nasara a kanmu ba.
Kokawanmu da Mugayen Ruhohi
5. Ta yaya ne wannan yaƙi da aka ambata a yaren asali da aka yi amfani da shi a Afisawa 6:12 ya sa muka fahimci dabarar Shaiɗan?
5 Bulus ya bayyana cewa “famanmu [kokawa] . . . da mugayen ruhohi ne na sararin sama.” Ainihin mugun ruhun shi ne Shaiɗan Iblis, “sarkin aljanu.” (Matiyu 12:24-26) Yaren asali na Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yaƙin da muke yi da kokawa ko kuwa fama. A gasar kokawa a Helas na dā, kowane ɗan kokawa na ƙoƙarin ya ga cewa ya kayar da abokin kokawarsa. Hakazalika, Iblis yana son ya ga cewa mun yi hasarar ruhaniyarmu. Ta yaya zai iya yin hakan?
6. Ka yi amfani da Nassosi ka nuna yadda Iblis ke iya amfani da dabaru dabam dabam don ya yi wa bangaskiyarmu zagon ƙasa.
6 Iblis yana iya yi kamar maciji, zaki mai ruri, ko mala’ika na haske. (2 Korantiyawa 11:3, 14; 1 Bitrus 5:8) Yana iya yin amfani da mutane su tsananta ko kuwa jawo mana sanyin gwiwa. (Wahayin Yahaya 2:10) Tun da yake dukan duniya a hannun Shaiɗan take, yana iya yin amfani da sha’awace-sha’awace da abin kwashe hankali domin ya kama mu a tarkonsa. (2 Timoti 2:26; 1 Yahaya 2:16; 5:19) Yana iya amfani da tunanin duniya ko na ’yan ridda don ya yaudare mu yadda ya yaudari Hauwa’u.—1 Timoti 2:14.
7. Wace iyaka aljanu suke da ita, kuma waɗanne fa’idodi ne muke mora?
7 Ko da yake makamai, da ikon Shaiɗan, da na aljanunsa suna da girma, duk da haka suna da iyakarsu. Waɗannan mugayen ruhohi ba sa iya tilasta mana mu yi abubuwa marasa kyau da za su ɓata wa Ubanmu na sama rai. Mu mutane ne da aka ba mu ’yancin yin zaɓe, kuma muna da iko a kan tunaninmu da halayenmu. Bugu da ƙari, ba mu kaɗai ke yaƙin ba. Yadda yake a ranakun Elisha haka yake a yau: “Waɗanda suke tare da mu, sun fi waɗanda suke tare da su yawa.” (2 Sarakuna 6:16) Littafi Mai Tsarki ya ba mu tabbacin cewa idan muka miƙa kanmu ga Allah kuma muka yi tsayayya da Iblis, zai guje mu.—Yakubu 4:7.
Mun San Makidodin Shaiɗan
8, 9. Wane gwaji ne Shaiɗan ya yi wa Ayuba domin ya karya amincinsa, kuma wane haɗari na ruhaniya ne muke fuskanta a yau?
8 Mu ba jahilan makidodin Shaiɗan ba ne domin Nassosi ya bayyana mana ainihin dabarunsa. (2 Korantiyawa 2:11) Iblis ya harbi Ayuba adali da matsalar tattalin arziki, mutuwar ƙaunatattu, hamayya daga iyalinsa, wahala, da kuma sūka ba dalili daga abokansa na ƙarya. Ayuba ya yi baƙin ciki ƙwarai har ya ji kamar Allah ya yasar da shi. (Ayuba 10:1, 2) Ko da yake Shaiɗan ba zai fito kai tsaye ya haddasa irin waɗannan matsalolin a yau ba, waɗannan wahalolin suna shafan Kiristoci da yawa, kuma Iblis yana amfani da su ya cim ma moriyarsa.
9 Haɗari na ruhaniya yana ƙaruwa a wannan lokaci na ƙarshe. Muna zaune a duniyar da biɗan abin duniya ya sha kan makasudi na ruhaniya. Hanyar watsa labarai na nuna cewa lalata tana kawo farin ciki maimakon ɓacin rai. Kuma yawancin mutane a yau sun zama “ma-fiya son annishuwa da Allah.” (2 Timoti 3:1-5) Irin wannan tunanin na iya shafan daidaitarmu ta ruhaniya sai dai in mun “yi yaƙi domin imani.”—Yahuza 3.
10-12. (a) Wace faɗakarwa ɗaya ne Yesu ya bayar a cikin kwatancinsa na mai shuka? (b) Ka kwatanta yadda ake iya maƙure darajar ruhaniya.
10 Biɗan abin duniya da kuma shagala da wannan duniyar ɗaya ne daga cikin dabarun da Shaiɗan ke amfani da ita. A cikin kwatancinsa na mai shuka, Yesu ya yi gargaɗi cewa a wasu yanayin “taraddadin duniya da jarabar dukiya sukan sarƙe maganar [Mulki].” (Matiyu 13:18, 22) Kalmar Helenanci da aka fassara “sarƙe” tana nufin “maƙure gabaki ɗaya.”
11 A cikin kurmi, kana iya ganin ice mai kama da ceɗiya da ke yin toho a jikin wani ice. Yana nannaɗe icen. A hankali a hankali, sai icen mai kama da ceɗiyan ya kame jikin icen da jijiyoyinsa masu ƙwari. Sai jijiyoyin icen mai kama da ceɗiyan su tsotse abubuwan gina jiki da ke ƙarƙashin icen, bayan haka kuma sai ganyen icen mai kama da ceɗiyan ya sha kan icen ya hana shi samun hasken rana. A ƙarshe, sai icen ya mutu.
12 Haka nan ma, taraddadin wannan duniyar, neman dukiya da morewar rayuwa na iya janye mana yawancin lokacinmu da kuzari a hankali. Idan hankalinmu ya koma ga abubuwan duniya, muna iya yin watsi da nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma fasa zuwan taro na Kirista, da haka, sai mu rabu da abinci na ruhaniya. Abubuwa na duniya sai su sha kan ayyuka na ruhaniya, a ƙarshe sai mu faɗā hannun Shaiɗan da sauƙi.
Muna Bukatar Mu Dage
13, 14. Wane mataki ya kamata mu ɗauka sa’ad da Shaiɗan ya yi hamayya da mu?
13 Bulus ya aririce ’yan’uwa masu bi su “dage gāba da kissoshin Iblis.” (Afisawa 6:11) Hakika, ba ma iya halaka Iblis da aljanunsa. Allah ya ba Yesu Kristi wannan aikin. (Wahayin Yahaya 20:1, 2) Muna bukatar ‘dagewa’ domin kada harin Shaiɗan ya sha kanmu har sai lokacin da aka cire shi.
14 Manzo Bitrus ya nanata dalilin da ya sa muke bukatar dagewa gāba da Shaiɗan. “Ku natsu, ku kuma zauna a faɗake,” in ji Bitrus. “Magabcinku Iblis na zazzāgawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lanƙwame. Ku yi tsayayya da shi, kuna dagewa kan bangaskiyarku, da ya ke kun san ’yan’uwanku a duniya duka an ɗora musu irin wannan shan wuya.” (1 Bitrus 5:8, 9) Hakika, taimakon ’yan’uwanmu na ruhaniya na da muhimmanci domin mu dage sa’ad da Iblis ya kawo mana hari kamar zaki mai ruri.
15, 16. Ka ba da misali na Nassi da ya nuna yadda taimako na ’yan’uwa masu bi zai taimaka mana mu dage.
15 Sa’ad da zaki ya yi ruri a cikin dajin Afirka, gwanki yana gudun fitar rai har sai ya tsira daga halaka. Amma, giwaye na kwatanta misalin haɗin kai. Littafin Elephants—Gentle Giants of Africa and Asia ya bayyana: “Yadda garken giwaye ke kāre juna shi ne ta gewaye kansu, manyan za su fuskanci inda ake burgar, da haka ƙananan giwayen za su sami kāriya.” Da kyar zakuna su faɗā wa giwaye har ƙanana ma domin ƙarfi da kuma haɗin kansu.
16 Sa’ad da Shaiɗan da aljanunsa suka yi mana barazana, muna bukatar mu kasance tare da zuciya ɗaya da ’yan’uwanmu masu ƙaƙƙarfar bangaskiya. Bulus ya ce wasu Kiristoci ’yan’uwa sun “sanyaya [masa] zuciya” sa’ad da yake kurkuku a Roma. (Kolosiyawa 4:10, 11) Kalmar Helenanci da aka fassara “sanyaya mini zuciya” ta bayyana sau ɗaya ne kawai a Nassosin Kirista na Helenanci. Ƙamus na Vine’s Expository Dictionary of New Testament Words ya ce, “a zaman aikatau wannan kalmar tana nufin maganin da ke kawar da ƙaiƙayi.” Kamar māi mai sauƙaƙa ciwo, taimakon da masu bauta wa Jehovah da sun ƙware ke bayarwa na iya kawar da damuwa ko wahala da ke jawo azaba.
17. Menene zai taimaka mana mu riƙe amincinmu ga Allah?
17 Ba da ƙarfafa da ’yan’uwa Kirista suke yi a yau na iya ƙarfafa aniyarmu na bauta wa Allah da aminci. Mafi muhimmanci sune dattawa na Kirista da suke ƙoƙarin ba da taimako na ruhaniya. (Yakubu 5:13-15) Abubuwan da za su taimake mu mu kasance masu aminci sun haɗa da nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai, da halartan taron ikilisiya, manyan taro, da na gunduma. Dangantakarmu na kud da kud da Allah za ta taimaka mana mu kasance da amince gare shi. Hakika, dukan abin da muke yi, ko muna ci, ko sha, muna son mu yi kome saboda ɗaukakar Allah. (1 Korantiyawa 10:31) Muna bukatar mu dogara ga Jehovah cikin addu’a domin mu ci gaba a kan hanyar da za ta faranta masa rai.—Zabura 37:5.
18. Me ya sa ba za mu karaya ba har ma idan yanayi na wahala ya soma taƙure ƙarfinmu?
18 A wasu lokatai Shaiɗan na kawo mana hari sa’ad da muke jin mun raunana a ruhaniya. Zaki yana faɗā wa dabbar da ta raunana. Matsaloli na iyali, matsalar tattalin arziki, ko rashin lafiya na iya janye ƙarfin ruhaniyarmu. Amma kada mu daina yin abin da zai faranta wa Allah rai, domin Bulus ya ce: “Sa’ad da nake rarrauna, a sa’an nan ne nake da ƙarfi.” (2 Korantiyawa 12:10; Galatiyawa 6:9; 2 Tasalonikawa 3:13) Menene yake nufi? Yana nufin cewa ikon Allah zai iya sauya raunanarmu, idan muka juya ga Jehovah don ƙarfafa. Nasarar da Dawuda ya ci bisa Goliyat ta nuna cewa Allah yana ƙarfafa kuma zai ƙarfafa mutanensa. Shaidun Jehovah na zamani za su iya shaida cewa a lokacin tarzoma, sun sami ƙarfafa daga wajen Allah.—Daniyel 10:19.
19. Ka ba da misalin da ya nuna yadda Jehovah yake ƙarfafa bayinsa.
19 Game da taimakon da Allah ya ba su, wasu ma’aurata sun rubuta: “Fiye da shekara guda ke nan da muke bauta wa Jehovah a matsayin mata da miji, mun more albarka mai yawa kuma mun san muhimman mutane masu yawa. Jehovah ya koyar da mu kuma ya ƙarfafa mu mu jimre wa wahala. Kamar Ayuba, a wasu lokatan ba ma sanin dalilin da ya sa abubuwa suke faruwa mana, amma mun san cewa Jehovah zai taimaka mana.”
20. Wane tabbaci na Nassi ne ya nuna cewa Jehovah yana taimaka wa mutanensa a kowane lokaci?
20 Ikon Jehovah ba ya kasawa har da ba zai iya taimakawa kuma ya ƙarfafa amintattun mutanensa ba. (Ishaya 59:1) Dawuda mai zabura ya rera: “Ubangiji, yakan taimaki dukan waɗanda ke shan wahala, ya kan ta da waɗanda aka wulakanta.” (Zabura 145:14) Hakika, Ubanmu na sama yana “ɗaukar nawayarmu ta yau da kullum,” kuma yana ba mu ainihin abubuwan da muke bukata.—Zabura 68:19.
Muna Bukatar “Dukan Makamai na Allah”
21. Ta yaya ne Bulus ya nanata dalilin da ya sa muke bukatar makamai na ruhaniya?
21 Mun riga mun tattauna game da wasu dabaru na Shaiɗan kuma mun ga dalilin da ya sa muke bukatar mu dage saboda harinsa. Yanzu kuma dole ne mu yi la’akari da wani muhimmin tanadi da zai sa mu ci nasara wajen kāre bangaskiyarmu. Sau biyu a cikin wasiƙarsa zuwa ga Afisawa, manzo Bulus ya ambata wani muhimmin abu da zai taimaka mana mu dage da kissoshin Shaiɗan da kuma famanmu da mugayen ruhohi. Bulus ya rubuta: “Ku yi ɗamara da dukan makamai na Allah, don ku iya dage gāba da kissoshin Iblis. . . . Sai ku ɗauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa a muguwar ranan nan, bayan kuma kun gama kome duka, ku dage.”—Afisawa 6:11, 13.
22, 23. (a) Menene makamanmu na ruhaniya ke ɗauke da shi? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?
22 Hakika, muna bukatar sa ‘dukan makamai na Allah.’ Sojan Roma na tsare da Bulus sa’ad da yake rubuta wasiƙarsa zuwa ga Afisawa, wanda wataƙila ya sanya ɗamara na makamai. Amma dai, Allah ne ya hure manzon ya tattauna wani makami na ruhaniya da kowane bawan Jehovah ke bukata.
23 Makamin da Allah yake bayarwa ya haɗa da halayen da ya kamata a ce Kirista na da shi da kuma tanadi na ruhaniya da Jehovah ya bayar. A cikin talifinmu na gaba, za mu bincika kowanne cikin waɗannan makamai na ruhaniya. Wannan zai sa mu ƙudura niyyar sanin yadda muke a shirye domin yaƙinmu na ruhaniya. Har ila kuma za mu ga yadda misali mai kyau na Yesu Kristi zai taimaka mana mu ci nasarar ƙin Shaiɗan Iblis.
Yaya Za Ka Amsa?
• Wane yaƙi dukan Kiristoci suke yi?
• Ka kwatanta wasu cikin dabaru na Shaiɗan.
• Ta yaya ne taimakon ’yan’uwa masu bi zai ƙarfafa mu?
• A kan ƙarfin wa ya kamata mu dogara, kuma me ya sa?
[Hotuna a shafi na 11]
Kiristoci suna ‘fama da mugayen ruhohi’
[Hoto a shafi na 12]
Taraddadin duniyar nan suna sarƙe maganar Mulki
[Hoto a shafi na 13]
’Yan’uwa Kiristoci suna iya ‘sanyaya mana zuciya’
[Hoto a shafi na 14]
Kuna addu’a ga Allah ya ba ku ƙarfi kuwa?