Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wt babi na 17 pp. 151-158
  • Ka Kasance da Ibada a Gida

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance da Ibada a Gida
  • Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Shekara Nawa Auren Ya Kamata Ya Kasance?
  • Kowanne Yana Cika Nasa Hakkin
  • Inda Za a Samu Amsoshi
  • Yadda Kiristoci Za Su Yi Nasara a Aurensu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Aure, Kyauta ne Daga Allah Mai Kauna
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Ja-gora Daga Allah A Zaɓar Wadda Za A Aura
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Aure Kyauta Ne Daga Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Dubi Ƙari
Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
wt babi na 17 pp. 151-158

Babi Na Goma Sha Bakwai

Ka Kasance da Ibada a Gida

1. Ta yaya yin amfani da ja-gora daga Kalmar Allah ya shafi aure-aure?

JEHOVAH shi ne Tushen aure, kuma Kalmarsa ta yi tanadin ja-gora mafi kyau don iyalai. Saboda yin amfani da wannan ja-gorar, mutane da yawa sun yi nasara a aurensu. Abin farin ciki, wasu da suke zaman daduro kawai sun motsa su yi ragistar aurensu bisa ga doka. Wasu kuma sun daina yin jima’i da ba halal ba. Maza da suke zaluntar matansu da ’ya’yansu sun koyi su nuna alheri da kuma ƙauna.

2. Menene rayuwar iyali ta Kirista ta ƙunsa?

2 Rayuwar iyali ta Kirista ta ƙunshi abubuwa da yawa, yadda muke ɗaukan ƙarƙon aure, abin da za mu yi don mu cika hakkinmu ga iyalin, da kuma yadda za mu bi da waɗanda suke cikin iyalin. (Afisawa 5:33–6:4) Ko da mun san abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da rayuwar iyali, wani abu ne dabam a yi amfani da gargaɗin Littafi Mai Tsarki. Babu waninmu da yake so ya zama kamar waɗanda Yesu ya hukunta don sun karya umurnan Allah. Suna tunanin banza cewa ibada kawai ga addini ta isa. (Matta 15:4-9) Ba ma so mu kasance da lamunin ibada amma mu kasa yinta cikin iyalinmu. Akasin haka, muna so mu nuna ibada ta gaske, wadda take “riba ce mai-girma.”—1 Timothawus 5:4; 6:6; 2 Timothawus 3:5.

Shekara Nawa Auren Ya Kamata Ya Kasance?

3. (a) Menene ke faruwa ga aure-aure da yawa, amma me ya kamata ya zama aniyarmu? (b) Ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki naka, ka amsa tambayoyi da ke a jere a ƙasan izifin nan.

3 Aure-aure suna ƙara lalacewa da sauƙi. Wasu ma’aurata sun kasance tare na shekaru da yawa sai su yanke shawarar kashe auren don su auri wani dabam. Ba baƙon abu ba ma a ji matasa ma’aurata sun rabu bayan ɗan lokaci. Ko da menene wasu suka yi, ya kamata mu so mu faranta wa Jehovah rai. Saboda haka, bari mu bincika tambayoyi na gaba da nassosi mu ga abin da Kalmar Allah ta ce game da ƙarƙon aure.

Yayin da namiji da mace suka yi aure, shekaru nawa ake tsammanin za su kasance tare? (Markus 10:6-9; Romawa 7:2, 3)

Menene kaɗai dalilin kashe aure da samun izinin sake yin aure a wajen Allah? (Matta 5:31, 32; 19:3-9)

Yaya Jehovah yake ji game da kashe aure da Kalmarsa ta ƙi? (Malachi 2:13-16)

Littafi Mai Tsarki yana goyon bayan rabuwa ne domin a magance matsalar aure? (1 Korinthiyawa 7:10-13)

A wane yanayi ne za a iya rabuwa? (Zabura 11:5; Luka 4:8; 1 Timothawus 5:8)

4. Me ya sa wasu aure-aure suke daɗewa?

4 Wasu aure-aure suna nasara, kuma suna daɗewa. Me ya sa? Jira har sai mutane biyun sun isa aure zai taimaka, samun abokin aure da zai so ki kuma so ya tattauna abubuwa a fili yana da muhimmanci. Mafi muhimmanci ma shi ne, samun abokin aure da ke ƙaunar Jehovah kuma ke daraja Kalmarsa don warware matsaloli. (Zabura 119:97, 104; 2 Timothawus 3:16, 17) Irin mutumin ba zai kasance da halin cewa idan abubuwa ba su tafi daidai ba, sai su rabu ko kuma kashe auren. Ba zai yi amfani da kasawar matarsa ta zama hujjar ƙin cika hakkinsa ba. Maimako, zai fuskanci matsaloli ya kuma nemi maganinsu.

5. (a) Yaya aminci ga Jehovah ya shafi aure? (b) Ko idan ma an fuskanci hamayya, waɗanne amfani ke zuwa daga bin mizanan Jehovah?

5 Shaiɗan ya yi tuhumar cewa idan muka wahala, za mu yi banza da hanyoyin Jehovah. (Ayuba 2:4, 5; Misalai 27:11) Amma yawancin Shaidun Jehovah da suka wahala don abokin ko kuma abokiyar aure da ke hamayya bai sa su karya alkawarin aurensu ba. Sun ci gaba da kasancewa da aminci ga Jehovah da kuma umurnansa. (Matta 5:37) Wasu da sun nace sun yi farin cikin ganin abokin aurensu ya bi su a bauta wa Jehovah—har ma bayan shekaru da yawa na hamayya! (1 Bitrus 3:1, 2) Game da Kiristoci da abokan aurensu ba su da alamar za su canja ko kuma waɗanda abokan aurensu sun yasar da su saboda suna bauta wa Jehovah, waɗannan sun sani cewa za su samu albarka idan suka nuna suna da ibada a gida.—Zabura 55:22; 145:16.

Kowanne Yana Cika Nasa Hakkin

6. Don a kasance da aure mai nasara, wane tsari ne dole a daraja?

6 Hakika, domin aure ya yi nasara, ya wuci zama tare kawai. Bukata ta musamman a wajen kowanne cikinsu ita ce daraja tsarin Jehovah na shugabancin iyali. Wannan yana daɗa ga tsari mai kyau da kuma samun iyali mai kwanciyar rai. A 1 Korinthiyawa 11:3, mu karanta: “Kan kowane namiji Kristi ne; kan mace kuma namiji ne; kan Kristi kuma Allah ne.”

7. Yaya ya kamata a yi shugabanci cikin iyali?

7 Ka lura da abin da ayar ta ambata da farko? Hakika, kowanne namiji yana da Shugaba, Kristi, wanda duka suke bukatar yi masa biyayya. Wannan yana nufi ke nan cewa mijin zai yi shugabanci a hanyar da za ta nuna halin Yesu. Kristi yana biyayya ga Jehovah, yana ƙaunar ikilisiya ƙwarai, kuma yana yi mata tanadi. (1 Timothawus 3:15) Ya “bada kansa dominta” ma. Yesu ba mai fahariya ba da kuma marar la’akari, amma “mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya.” Waɗanda suke ƙarƙashin shugabancinsa suna samun “hutawa ga rayukan[su].” Yayin da miji ya bi da iyalinsa a hanyar nan, yana nuna cewa yana biyayya ga Kristi. Da haka ya kamata mata Kirista su ga yana da amfani da kuma ba da hutu ta ba da haɗin kai da yin biyayya ga shugabancin mijinta.—Afisawa 5:25-33; Matta 11:28, 29; Misalai 31:10, 28.

8. (a) Me ya sa ya zama kamar tafarkin Kirista ba ya ci a wasu iyalai? (b) Me ya kamata mu yi idan muka fuskanci irin wannan yanayin?

8 Amma, matsaloli za su zo. Wataƙila an saba da ƙin ja-gora daga wajen wani cikin iyalin kafin wani cikinsu ya fara yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Roƙo da kuma ƙauna wataƙila ba su kawo sakamako mai kyau ba. Mun sani Littafi Mai Tsarki ya ce mu yasar da “hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage.” (Afisawa 4:31) Amma idan wasu cikin iyalin ba sa jin gari sai hasala, me za a yi? To, Yesu bai yi koyi da waɗanda suke kashedi da kuma zafin rai ba, amma ya dogara ga Ubansa. (1 Bitrus 2:22, 23) Saboda haka, yayin da matsaloli suka taso a gida, ka ba da tabbacin ibada ta wurin yin addu’a ga Jehovah don taimakonsa maimakon bin hanyoyin duniya.—Misalai 3:5-7.

9. Maimakon neman fitina, menene magidanta Kirista da yawa suka koyi su yi?

9 Ba kullum ba ne canji ke zuwa da sauri, amma gargaɗin Littafi Mai Tsarki yana aiki da gaske idan aka yi haƙuri da kuma ƙwazo a yin amfani da shi. Magidanta da yawa sun iske cewa auren yana gyaruwa yayin da suka bi yadda Kristi ke shugabancin ikilisiya. Ikilisiyar ba ta kamiltattun mutane ba ce. Duk da haka, Yesu yana ƙaunarta, ya bar mata misali mai kyau, kuma ya yi amfani da Nassosi don yi mata gyara. Ya ba da ransa domin ikilisiya. (1 Bitrus 2:21) Misalinsa ya taimake magidanta Kiristoci da yawa su yi shugabanci mai kyau kuma yana taimaka ga ƙauna don a yi gyara a aurensu. Wannan yana kawo sakamako mai kyau maimakon neman fitina ko kuma ƙin magana.

10. (a) A waɗanne hanyoyi miji ko kuma mata—ko wadda take da’awar Kirista ce—za ta iya sa rayuwa ta zama da wuya ga wasu cikin iyalin? (b) Me za a iya yi don a gyara yanayin?

10 Idan maigidan ba ya damuwa da motsin ran iyalinsa ko kuma ba ya ɗaukar mataki ya yi shiri don tattauna Littafi Mai Tsarki da kuma wasu ayyuka na iyalinsa fa? Ko kuma idan mata ba ta haɗa kai da shi kuma ba ta biyayya fa? Wasu suna magance haka ta tattauna matsalolinsu na iyali cikin daraja. (Farawa 21:10-12; Misalai 15:22) Ko idan ba a samu sakamakon da ake so ba, kowannenmu zai iya daɗa ga yanayi mai kyau na iyalin don a samu ’ya’yan ruhu na Allah cikin rayuwarmu, yana nuna kulawa ga wasu da suke cikin iyalin. (Galatiyawa 5:22, 23) Za a samu ci gaba, ba ta jira wani ya yi wani abu ba, amma ta cika namu hakkin, muna nuna cewa muna yin ibada.—Kolossiyawa 3:18-21.

Inda Za a Samu Amsoshi

11, 12. Menene Jehovah ya yi tanadi don ya taimake mu mu yi nasara a rayuwar iyali?

11 Da akwai wurare da yawa da mutane suke zuwa don gargaɗi game da harkokin iyalinsu. Amma mun sani cewa Kalmar Allah tana ɗauke da gargaɗi mafi kyau, kuma muna murna cewa ta wurin ƙungiyarsa da ake gani, Allah yana taimakonmu mu yi amfani da shi. Kana amfana daga wannan taimakon kuwa?—Zabura 119:129, 130; Mikah 4:2.

12 Ban da halartan taro a ikilisiya, kana ayana lokaci don nazarin Littafi Mai Tsarki na iyalinka? Iyalai da suke yin haka za su iya aiki don su kasance da haɗin kai cikin bautarsu. Iyalinsu tana samun albarka yayin da suke amfani da Kalmar Allah a yanayinsu.—Kubawar Shari’a 11:18-21.

13. (a) Idan muna da tambayoyi game da al’amura na iyali, sau da yawa a ina za mu iya samun taimakon da muke bukata? (b) Me ya kamata ya bayyana a cikin dukan shawarar da muke yi?

13 Wataƙila kana da tambayoyi game da al’amura na iyali. Alal misali, me za a ce game da rage haihuwa? Daidai ne a zubar da ciki don wani dalili? Idan yaro ba ya cika son abubuwa na ruhaniya, har yaya za a yarda masa ya saka hannu cikin bauta ta iyali? An tattauna irin waɗannan tambayoyin cikin littattafan da Shaidun Jehovah suka buga. Ka koyi yin amfani da abubuwan yin nazari, haɗe da su index, don samun amsoshin. Idan ba ka da littattafan da aka nuna cikin index, ka duba laburare na Majami’ar Mulki. Ko kuma kana iya samun littattafan nan cikin kwamfuta naka. Kana iya tattauna tambayoyinka da ƙwararrun maza da mata Kirista. Amma ba kullum za ka yi tsammanin samun e ko a’a ga kowacce tambayarka ba. Sau da yawa, dole ka tsai da shawara, ko marar aure ne ko mai aure ne kai. Sai ka tsai da shawara da za ta nuna kai mai ibada ne ba a fili kawai ba amma kuma har a gida.—Romawa 14:19; Afisawa 5:10.

Maimaita Abin da Aka Tattauna

• Ta yaya aminci ga Jehovah ya shafi aminci ga abokin aure?

• Yayin da muke cikin matsi domin matsalolin iyali, me zai taimake mu yin abin da ke faranta wa Allah rai?

• Ko idan wasu cikin iyali sun kasa, me za mu yi don gyara yanayin?

[Hoto a shafi na 155]

Ya kamata shugabancin maigida ya nuna halayen Yesu

[Hoto a shafi na 157]

Yin nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali a kai a kai yana haɗa kan iyalin

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba