Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ll kashi 1 pp. 4-5
  • Ta Yaya Muke Sauraron Allah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Muke Sauraron Allah?
  • Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
  • Makamantan Littattafai
  • Sashe na 1
    Ka Saurari Allah
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Littafi Mai Tsarki Maganar Allah Ne
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
ll kashi 1 pp. 4-5

SASHE NA 1

Ta Yaya Muke Sauraron Allah?

Sa’ad da muka karanta Littafi Mai Tsarki, kamar dai Allah yana yi mana magana ne. 2 Timotawus 3:16

Daga kursiyinsa a sama Jehobah ya hore ’yan Adam su rubuta Littafi Mai  Tsarki

Allah na gaskiya ya ja-goranci mazaje su rubuta nufinsa a cikin wani littafi na musamman. Wannan littafin shi ne Littafi Mai Tsarki. Yana ɗauke da saƙo masu muhimmanci da Allah yake son ka sani.

Allah ya san abin da ya fi dacewa da mu kuma shi ne Tushen dukan hikima. Idan ka saurare shi, za ka kasance da hikima sosai. —Misalai 1:5.

Littafi Mai Tsarki a yaruka da yawa; wani mutum yana karatun Littafi Mai Tsarki da yarensu

Allah yana son kowane mutum a duniya ya karanta Littafi Mai Tsarki. Za a iya samunsa a harsuna masu yawa a yau.

Idan kana son ka ji abin da Allah yake cewa, dole ne ka karanta Littafi Mai Tsarki kuma ka fahimce shi.

Mutane a ko’ina a duniya suna koyo game da Allah. Matta 28:19

Wani mashaidi yana karanta wa wani mutum Littafi Mai Tsarki, daga baya sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki

Shaidun Jehobah za su iya taimaka maka ka fahimci Littafi Mai Tsarki.

Suna koyar da gaskiya game da Allah a dukan duniya.

Ana taro a Majami’ar Mulki Shaidun Jehobah

Ba ka bukatar ka biya ko sisi don samun wannan koyarwar. Kana kuma iya samun koyarwa game da Allah a Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah da ke yankinku.

  • Kalmar Allah gaskiya ce.—Yohanna 17:17.

  • Me ya sa za mu iya dogara ga Allah?—Litafin Lissafi 23:19.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba