AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI
Zai yiwu mutum ya fahimci Littafi Mai Tsarki kuwa?
Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce. Yana kama da wasiƙa daga Uba mai ƙauna. (2 Timotawus 3:16) A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya bayyana mana yadda za mu faranta masa rai, abin da ya sa ya ƙyale mugunta da kuma abin da zai yi wa ’yan Adam a nan gaba. Amma limaman addinai suna koyar da abin da ya saɓa wa koyarwar Littafi Mai Tsarki; shi ya sa mutane da yawa suna gani cewa ba za su iya fahimtar Littafi Mai Tsarki ba.—Ayyukan Manzanni 20:29, 30.
Jehobah Allah yana so mu san gaskiya game da shi. Shi ya sa ya tanadar mana da littafi mai sauƙin fahimta.—Ka karanta 1 Timotawus 2:3, 4.
Ta yaya za ka fahimci Littafi Mai Tsarki?
Jehobah ya ba mu Littafi Mai Tsarki kuma yana taimaka mana mu fahimci abin da ke ciki. Ya aiko Yesu don ya koyar da mu. (Luka 4:16-21) Yesu ya taimaka wa masu sauraronsa su fahimci Nassi yayin da yake bayyana aya bayan aya.—Ka karanta Luka 24:27, 32, 45.
Yesu ya kafa ikilisiyar Kirista don ta ci gaba da yin aikin da ya soma. (Matta 28:19, 20) A yau, ainihin mabiyan Yesu suna taimaka wa mutane su fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da Allah. Idan kana son ka fahimci Littafi Mai Tsarki, Shaidun Jehobah za su yi farin cikin taimaka maka.—Ka karanta Ayyukan Manzanni 8:30, 31.