Za Ka Iya Fahimtar Littafi Mai Tsarki Kuwa?
“Iyalinmu tana karanta Littafi Mai Tsarki a duk ranar Lahadi. Amma ba na jin daɗinsa sosai. Na gaskata cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce, amma yawancin abubuwan da na karanta suna da wuyan fahimta sosai.”—Steven, Biritaniya.
“Sa’ad da nike ’yar shekara 17, na yi ƙoƙarin na karanta Littafi Mai Tsarki. Amma na ga cewa yana da wuyan fahimta, sai na daina karanta shi.”—Valvanera, Spain.
“Na karanta Littafi Mai Tsarki sau ɗaya kawai domin na ga cewa a matsayi na na ’yar Katolika, ya kamata in karanta shi. Na yi shekara uku kafin na kammala shi! Amma ban fahimci yawancin abin da ke ciki ba.”—Jo-Anne, Ostareliya.
LITTAFI MAI TSARKI ne littafin da aka fi sani a duniya. Shi ne littafin da aka fi saye, mutane da yawa za su iya samun shi a harsuna masu yawa, kuma a fasaloli dabam-dabam fiye da dā. Duk da haka, yawancin mutanen da ke da Littafi Mai Tsarki ba sa fahimtarsa sosai. Yadda kake ji ke nan?
Mawallafin Yana Son Mu Fahimci Kalmarsa Ne?
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane nassi hurarre daga wurin Allah” ne. (2 Timothawus 3:16) Hakika, Jehobah ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki. Yana son mu fahimci Kalmarsa kuwa? Ko kuwa ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi wuyan fahimta ne ga yawancin mutane, amma ya ba wasu, kamar malamai da masu bincika Littafi Mai Tsarki ingancin fahimtarsa?
Ka yi la’akari da waɗannan ayoyi daga Littafi Mai Tsarki:
“Wannan doka wadda na dokace ka da ita yau, ba ta fi ƙarfinka ba, ba ta kuwa da nisa.”—Kubawar Shari’a 30:11.
“Buɗen zantattukanka yana bada haske; yana bada fahimi ga sahihai.”—Zabura 119:130.
“A cikin wannan sa’a [Yesu] ya yi murna ta wurin Ruhu Mai-tsarki, ya ce, Ina gode maka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, da ka ɓoye ma masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai.”—Luka 10:21.
Hakika, Mawallafin Littafi Mai Tsarki yana son ka fahimci Kalmarsa! Amma, gaskiyar ita ce, mutane suna ganin wuyan fahimtar wannan littafin. Menene zai taimake su? Talifi na gaba ya bayyana hanyoyi guda uku da za su iya taimaka maka ka fahimci Littafi Mai Tsarki.