Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 7/1 pp. 4-5
  • 1. Ka Nemi Taimakon Mawallafin

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 1. Ka Nemi Taimakon Mawallafin
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Ruhun Allah Ya Yi Ja-gora A Ƙarni Na Farko Da Kuma A yau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Me Ya Sa Ruhun Allah Zai Yi Mana Ja-gora?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 7/1 pp. 4-5

Yadda Za Ka Fahimci Littafi Mai Tsarki

1. Ka Nemi Taimakon Mawallafin

“Da akwai lokacin da nake karanta Littafi Mai Tsarki kafin na yi barci,” in ji Ninfa, wadda take da zama a ƙasar Italiya. “Na yi hakan ne domin na san cewa Kalmar Allah ce, ko da ba na jin daɗin karantata, ina son na san abin da Allah ya rubuta cikin Littafi Mai Tsarki. Na so na karantata gabaki ɗaya. Da farko abin yana da sauƙi, amma sa’ad da na kai wuraren da suke da wuya, sai na daina karantata.”

KA TAƁA fuskantar abin da ya faru da Ninfa? Mutane da yawa sun taɓa fuskantar irin wannan yanayin. Duk da haka, kamar yadda muka gani a talifin da ya gabata, mawallafin Littafi Mai Tsarki, Jehobah Allah, yana son ka fahimci Kalmarsa. Ta yaya za ka sami irin wannan fahimtar? Abu na farko shi ne ka nemi taimako daga Mawallafin.

An ɗauki manzannin Yesu kamar ‘marasa-karatu da talakawa’ domin ba su halarci makarantu na manyan malamai ba don samun koyarwa ta addini ba. (Ayyukan Manzanni 4:13) Duk da haka, Yesu ya ba su tabbaci cewa za su iya fahimtar Kalmar Allah. Ta yaya? Yesu ya bayyana: “Mai-taimako, wato Ruhu Mai-tsarki, wanda Uban zai aiko a cikin sunana, zai koya muku abu duka.” (Yohanna 14:26) Allah ya yi amfani da wannan ruhun mai tsarki, ko kuma iko, wajen halittan duniya da dukan rayuwa da ke cikinta. (Farawa 1:2) Ya kuma yi amfani da shi ya hure mutane wajen arba’in su rubuta nufinsa a cikin Littafi Mai Tsarki. (2 Bitrus 1:20, 21) Wannan ruhun yana nan don ya taimaka wa waɗanda suke son su fahimci Littafi Mai Tsarki.

Ta yaya za ka sami ruhu mai tsarki na Allah? Dole ne ka yi roƙo da bangaskiya. Hakika, wataƙila kana bukatan ka yi roƙo a kai a kai. Yesu ya ce: “Ku roƙa, za a ba ku. Idan . . . kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa?” (Luka 11:9, 13) Jehobah zai ba waɗanda suke roƙonsa da gaske ruhu mai tsarki kyauta. Wannan ruhun zai iya taimakon ka ka fahimci ma’anar hurarrun kalmomin da aka rubuta a Littafi Mai Tsarki dubban shekaru da suka shige. Ruhun Allah zai iya ba ka hikimar da kake bukata don ka yi amfani da saƙo mai iko da ke cikin Littafi Mai Tsarki a rayuwarka.—Ibraniyawa 4:12; Yaƙub 1:5, 6.

A duk lokacin da ka zauna don ka karanta Littafi Mai Tsarki, ka yi addu’a ga Allah, ka roƙe shi ya ba ka ruhunsa mai tsarki don ya taimake ka ka fahimci Kalmarsa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba