Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp16 Na 1 p. 16
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Makamantan Littattafai
  • Har Yanzu Gaskiya Tana da Muhimmanci Kuwa?
    Karin Batutuwa
  • Kiristoci Suna Bauta Cikin Ruhu Da Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Yin Koyi Da Allah Na Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ta Yaya Muke Sauraron Allah?
    Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
wp16 Na 1 p. 16

AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI

Za mu iya sanin gaskiya game da Allah kuwa?

Wani Mashaidin Jehobah ya zauna a benci yana wa wani mutum wa’azi

Me ya sa Allah yake so mu san Gaskiya? Karanta Yohanna 17:3

Allah ya taɓa magana da mutane a dā. Ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki ko ikonsa don ya taimaka wa mutane su rubuta abin da yake so. (2 Bitrus 1:​20, 21) Za mu iya sanin gaskiya game da Allah ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki.​—⁠Karanta Yohanna 17:17; 2 Timotawus 3:⁠16.

Allah ya bayyana abubuwa da yawa game da kansa a cikin Littafi Mai Tsarki. Ya faɗi dalilin da ya sa ya halicci mutane da nufinsa gare su da kuma yadda za su yi rayuwa. (Ayyukan Manzanni 17:​24-27) Jehobah Allah yana so mu san gaskiya game da shi.​—⁠Karanta 1 Timotawus 2:​3, 4.

Me ya sa Allah yake ƙaunar masu son gaskiya?

Jehobah, Allah ne na gaskiya kuma ya aiko da Ɗansa zuwa duniya don ya koya wa mutane gaskiya. Saboda haka, mutane masu son gaskiya suna ƙaunar Yesu. (Yohanna 18:37) Jehobah yana son irin waɗannan mutanen su zama bayinsa.​—⁠Karanta Yohanna 4:​23, 24.

Shaiɗan Iblis ya hana mutane da yawa sanin Allah ta wajen yaɗa koyarwar ƙarya game da Allah. (2 Korintiyawa 4:​3, 4) Mutanen da ba sa son gaskiya ne suke amincewa da wannan koyarwar ƙarya. (Romawa 1:25) Amma miliyoyin mutane suna neman gaskiya game da Allah ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki.​—⁠Karanta Ayyukan Manzanni 17:⁠11.

Don ƙarin bayani, ka duba babi na 1 a wannan littafin, Shaidun Jehobah ne suka wallafa

Za ka kuma iya samunsa a dandalin www.pr418.com/ha

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba