Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • jl darasi na 27
  • Yaya Laburaren da ke Majami’ar Mulki Zai Amfane Mu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yaya Laburaren da ke Majami’ar Mulki Zai Amfane Mu?
  • Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Yi Amfani da Su Maimakon Ku Tara Su
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Shin Kana Amfani da JW Library?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Wani Sabon Kayan Bincike
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Hanyoyin Yin Amfani da JW Library
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
jl darasi na 27

DARASI NA 27

Yaya Laburaren da ke Majami’ar Mulki Zai Amfane Mu?

Wani mutum yana amfani da laburaren Majami’ar Mulki

Isra’ila

Wani Mashaidi yana taimaka wa wani matashi yadda ake yin bincike

Jamhuriyar Czech

Wata ƙaramar yarinya tana rubuta sunanta a littafin rera waƙa nata

Bini

Wani mutum yana bincike ta wajen amfani da Watchtower Library

Cayman Islands

Za ka so ka yi wasu bincike don ka ƙara sanin Littafi Mai Tsarki? Kana son ka san wani nassi ko mutum ko wuri ko wani abu da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki? Ka taɓa tunanin ko Kalmar Allah za ta taimaka maka ka warware damuwarka? Ka je ka yi amfani da laburaren da ke Majami’ar Mulki.

Ana samun littattafan yin bincike a cikin laburaren. Wataƙila ba ka da dukan littattafan da suka bayyana Littafi Mai Tsarki, waɗanda Shaidun Jehobah suka wallafa a harshenku. Amma laburaren da ke Majami’ar Mulki yana ɗauke da yawancin littattafan da aka wallafa kwanan nan. Wataƙila akwai fassarar Littafi Mai Tsarki dabam-dabam da ƙamus mai kyau da wasu littattafan yin bincike a laburaren. Za ka iya yin amfani da laburaren kafin a soma taro ko bayan an kammala taro. Idan akwai kwamfuta a wurin, kana iya samun Watchtower Library a ciki. Watchtower Library wata fasaha ce da ake sakawa cikin kwamfuta kuma tana ɗauke da littattafanmu masu yawa, tana da sauƙi wajen bincika batu ko kalma ko kuma nassi.

Yana da amfani ga ɗalibai na taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu. Za ka iya yin amfani da laburaren da ke Majami’ar Mulki sa’ad da kake shirya aikin da aka ba ka a taro. Mai kula da taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu ne zai riƙa kula da laburaren. Shi ke da hakkin tabbatar da cewa an saka sababbin littattafai a laburaren kuma an tsara su yadda ya kamata. Mai kula da makaranta ko kuma malamin da ke koya maka Littafi Mai Tsarki zai iya nuna maka yadda za ka samu bayanin da kake so. Amma kada ka ɗauki littattafai daga laburaren Majami’ar Mulki ka kai gida. Hakika, bai kamata mu yi sakaci da littattafan ba, kuma kada mu yi rubutu a cikinsu.

Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa idan muna so mu samu “sanin Allah,” dole ne mu biɗe shi ‘kamar yadda ake biɗar ɓoyayyun dukiya.’ (Misalai 2:1-5) Laburaren da ke Majami’ar Mulki zai iya taimaka maka ka soma binciken da kake so.

  • Waɗanne kayan bincike ne ake samu a laburaren da ke Majami’ar Mulki?

  • Wane ne zai iya taimaka maka ka yi amfani da laburaren yadda ya kamata?

KA ƘARA BINCIKE

Idan kana son ka kafa naka laburaren, ka duba irin littattafan da ake da su a kantar littattafai. Malamin da ke nazarin Littafi Mai Tsarki da kai zai gaya maka littattafai da ya kamata ka fara ajiyewa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba