RAYUWAR KIRISTA
Hanyoyin Yin Amfani da JW Library
DON NAZARI:
Ka karanta Littafi Mai Tsarki da nassosin yini
Ka karanta Yearbook da mujallu da kuma wasu littattafai. Ka yi amfani da sashen ma’ajiyar rubutu
Ka shirya taro kuma ka maka amsoshin
Ka kalli bidiyoyi
A TARO:
Ka buɗe nassosin da mai jawabi ya ambata. Ka yi amfani da sashen rumbun bayani don ka koma wani nassin da ka buɗe
Maimakon zuwa taro da littattafai da yawa, za ka iya zuwa da na’urarka kawai kuma ka riƙa bin sashe dabam-dabam na taron har da waƙoƙinmu ma. JW Library yana ɗauke da sabbin waƙoƙinmu da ba sa cikin littafin waƙarmu
A WA’AZI:
Ka nuna ma wani da yake son saƙonmu wani abu a JW Library kuma ka taimaka masa ya sauko da wannan manhajar da kuma wasu littattafanmu a cikin na’urarsa
Ka yi amfani da sashen bincike don neman wani nassi
Ka nuna bidiyo. Idan masu gida suna da yara, za ka iya nuna musu ɗaya daga cikin bidiyoyin Ka Zama Abokin Jehobah. Ko kuma ka nuna bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? don ka sa mutumin ya so a yi nazari da shi. Idan ka haɗu da wani da yake wani yare, za ka iya nuna masa bidiyo a yarensa
Ka nuna wa mutane nassi a wani yare ta yin amfani da wasu juyin Littafi Mai Tsarki da ke na’urarka. Ka buɗe nassin sai ka danna ayar don ka ga fassara a wasu harsuna