Ku Yi Amfani da Su Maimakon Ku Tara Su
Ikilisiyoyi da yawa sun tara tsofaffin littattafai da yawa. Zai dace ka karɓi wasu don ka adana su a ma’adanan littattafanka. Shin kana nazari ne da ɗalibin Littafi Mai Tsarki da yake samun ci gaba? Zai dace ka ƙarfafa shi ya karɓi waɗannan tsofaffin littattafai kuma ya soma ajiye su a nasa ma’adanan littattafai. Dattijo Mai Kula da Makarantar Hidima Ta Allah ya tabbata cewa ma’adanan littattafai da ke Majami’ar Mulkin yana ɗauke da tsofaffin littattafai da aka tara a ikilisiyar. Har ila, waɗannan littattafai suna da daraja. Zai fi dacewa mu yi amfani da waɗannan littattafan maimakon a ajiye su a kantar littattafai ta ikilisiyar!