Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • fg darasi na 15 tambayoyi na 1-4
  • Me Ya Sa Ya Kamata Ka Ci Gaba da Koyo Game da Jehobah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Ya Kamata Ka Ci Gaba da Koyo Game da Jehobah?
  • Albishiri Daga Allah!
  • Makamantan Littattafai
  • Ta Yaya Za Ka Kusaci Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Rayuwa Mafi Inganci Ke Nan
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • ‘Yana da Kyau Mu Yi Kusa da Allah!’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ta Yaya Za Ka Iya Zama Aminin Allah?
    Albishiri Daga Allah!
Dubi Ƙari
Albishiri Daga Allah!
fg darasi na 15 tambayoyi na 1-4

DARASI NA 15

Me Ya Sa Ya Kamata Ka Ci Gaba da Koyo Game da Jehobah?

1. Ta yaya za ka amfana idan ka ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki?

Mata biyu suna nazarin Littafi Mai Tsarki a lokacin shan iska a wajen aiki

Babu shakka, wannan fitattun koyarwa ta Littafi Mai Tsarki da aka tattauna sun sa ka ƙara ƙaunar Jehobah. Zai dace ka ci gaba da ƙarfafa wannan ƙaunar. (1 Bitrus 2:2) Za ka samu rai na har abada idan ka ci gaba da kusantar Allah ta wajen yin nazarin Kalmarsa.​—Karanta Yohanna 17:3; Yahuda 21.

Yayin da kake daɗa koyon abubuwa da yawa game da Allah, bangaskiyarka za ta daɗa yin ƙarfi. Bangaskiya za ta taimaka maka ka faranta wa Allah rai. (Ibraniyawa 11:1, 6) Hakan za ta motsa ka ka tuba kuma ka yi canja-canjen da za su amfane ka a rayuwarka.​—Karanta Ayyukan Manzanni 3:19.

2. Ta yaya mutane za su amfana daga abubuwan da ka koya game da Allah?

Wata mata tana addu’a ga Allah

Za ka iya more dangantaka ta musamman da Jehobah

Babu shakka za ka so ka faɗa wa wani abin da ka koya don kowane mutum yana jin daɗin gaya wa mutane albishiri. Yayin da kake ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka koya yadda za ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki don bayyana wa mutane game da Jehobah da kuma bishara.​—Karanta Romawa 10:13-15.

Mutane da yawa suna soma yin hakan ne ta wajen tattaunawa da abokansu ko kuma danginsu. Amma, ka yi magana da hikima. Kada ka ce musu suna cikin addinin ƙarya. Maimakon haka, ka yi magana a kan alkawuran da Allah ya yi. Ka kuma tuna cewa gani ya kori ji, wato, halinka mai kyau ne zai sa mutane su saurare ka.​—Karanta 2 Timotawus 2:24, 25.

3. Wace dangantaka ce za ka iya morewa da Allah?

Yin nazarin Kalmar Allah za ta taimaka maka ka kyautata dangantarka da Jehobah. Daga baya, za ka samu dangantaka na kud da kud da Jehobah. Za ka iya kasancewa cikin iyalinsa.​—Karanta 2 Korintiyawa 6:18.

4. Ta yaya za ka samu ci gaba?

Za ka kyautata dangantakarka da Jehobah ta wajen yin nazarin Kalmarsa. (Ibraniyawa 5:13, 14) Ka gaya wa wani Mashaidin Jehobah ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai da taimakon littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?Idan kana nazarin Kalmar Allah, za ka yi nasara a rayuwa sosai.​—Karanta Zabura 1:1-3; 73:27, 28.

Shaidun Jehobah suna gayyatar wasu don a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su

Allah mai farin ciki ne tushen wannan bisharar. Za ka iya kusantarsa ta wajen kusantar bayinsa. (Ibraniyawa 10:24, 25) Idan ka ci gaba da yin ƙoƙari don faranta wa Jehobah rai, za ka samu rai na har abada. Abu mafi kyau da za ka yi shi ne kusantar Allah.​—Karanta 1 Timotawus 1:11; 6:19.

Don ƙarin bayani, ka duba babi na 18 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba