Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w15 1/1 p. 7
  • Rayuwa Mafi Inganci Ke Nan

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Rayuwa Mafi Inganci Ke Nan
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Makamantan Littattafai
  • Kana Ganin Ka Kusaci Allah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Me Ya Sa Ya Kamata Ka Ci Gaba da Koyo Game da Jehobah?
    Albishiri Daga Allah!
  • Za Ka Iya Zama Aminin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Ka Kulla Dangantaka ta Kud da Kud da Jehobah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
w15 1/1 p. 7
Wani mutum yana karanta Littafi Mai Tsarki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZA KA IYA KUSANTAR ALLAH

Rayuwa Mafi Inganci Ke Nan

Me za ka iya yi don ka kusaci Allah? Mun riga mun tattauna waɗannan matakai da za ka iya ɗauka don ka ƙulla dangantaka ta kud-da-kud da Allah:

  1. Ka san sunan Allah, wato Jehobah kuma ka riƙa amfani da shi.

  2. Ka riƙa yin addu’a ga Allah kuma ka karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai.

  3. Ka dāge wajen yin abubuwan da za su faranta wa Jehobah rai.

Wani mutum yana yin addu’a

Ka kusaci Allah ta wajen yin amfani da sunansa da yin addu’a da yin nazarin Kalmarsa da kuma faranta masa rai

Yanzu da ka san waɗannan matakan, shin za ka iya cewa kana yin abin da zai sa ka kusaci Allah? Shin akwai inda kake bukatar ka daɗa ƙoƙari? Hakika, yin hakan ba zai zama da sauƙi ba, amma ba aikin banza ba ne.

Jennifer daga Amirka ta ce, “Idan mutum ya yi ƙoƙari ya ƙulla dangantakata da Allah, ba zai taɓa yin da-na-sani ba.” Ta daɗa da cewa, “Irin wannan dangantakar tana kawo albarka sosai. Tana sa mutum ya dogara ga Allah sosai, ya san shi sosai kuma ya ƙaunace shi sosai. Hakika, rayuwa mafi inganci ke nan!”

Idan kana so ka ƙulla dangantaka ta kud-da-kud da Allah, Shaidun Jehobah za su taimaka maka ka yi hakan ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kai kyauta. Ƙari ga haka, za ka iya halartan taro a Majami’ar Mulki, wato inda suke taro a yankinku don su tattauna Littafi Mai Tsarki kuma za ka ji daɗin yin tarayya da waɗanda suke daraja dangantakarsu da Allah.a Yayin da kake hakan, za ka ji kamar wani marubucin zabura da ya ce: “Ya yi mani kyau in kusanci Allah.”—Zabura 73:28.

a Idan kana so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai ko kana so ka san inda Majami’ar Mulki take a yankinku, don Allah ka sanar da wanda ya ba ka mujallar nan ko ka shiga dandalinmu na www.pr418.com/ha kuma ka duba ƙarshen shafin farko, inda aka rubuta KA TUNTUƁE MU.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba