Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • hf sashe na 1 pp. 3-5
  • Ku Nemi Taimakon Allah don Ku Ji Daɗin Aurenku

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Nemi Taimakon Allah don Ku Ji Daɗin Aurenku
  • Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • 1 KU RIƘE MATSAYIN DA JEHOBAH YA BA KU
  • 2 KA MAI DA HANKALI GA ABIN DA KE DAMUN MATARKA
  • 3 KU TSAI DA SHAWARA TARE
  • Yadda Za Ka Daraja Matarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Kada Ku Ci Amanar Juna
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Zaman Aure
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Aure Kyauta Ne Daga Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Dubi Ƙari
Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
hf sashe na 1 pp. 3-5
Mata da miji a ranar da suka yi aure

SASHE NA 1

Ku Nemi Taimakon Allah don Ku Ji Daɗin Aurenku

“Shi wanda ya yi su tun farko, namiji da tamace ya yi su.”​—Matta 19:4

Jehobaha Allah ne ya ɗaura aure na farko. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa shi ya halicci mace ta farko kuma “ya kawo ta wurin mutumin.” Hakan ya faranta wa Adamu rai sosai, sai ya ce: “Wannan yanzu ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne daga namana.” (Farawa 2:22, 23) Har wa yau, Jehobah yana so mutane su ji daɗin aurensu.

Kana iya ganin kamar bayan ka yi aure kome zai tafi sumul. A gaskiya, ma’aurata da suke ƙaunar juna sosai ma suna iya samun matsala a wasu lokatai. (1 Korintiyawa 7:28) A cikin wannan ƙasidar, akwai ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da idan ka bi su, za ka ji daɗin aurenka kuma iyalinka za su zauna lafiya.—Zabura 19:8-11.​

1 KU RIƘE MATSAYIN DA JEHOBAH YA BA KU

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: Miji ne shugaban iyali.—Afisawa 5:23.

Idan kana da aure, Jehobah yana so ka kula da matarka da kyau. (1 Bitrus 3:7) Ya halicce ta a matsayin mataimakiya, kuma yana so ka ƙaunace ta kuma ka mutunta ta. (Farawa 2:18) Wajibi ne ka ƙaunaci matarka sosai kuma ka sa bukatunta gaba da naka.—Afisawa 5:25-29.

Idan ke matar aure ce, Jehobah yana so ki daraja mijinki sosai kuma ki taimaka masa ya cika hakkinsa da kyau. (1 Korintiyawa 11:3; Afisawa 5:33) Ki bi shawararsa kuma ki ba shi haɗin kai da dukan zuciyarki. (Kolosiyawa 3:18) Idan kika yi hakan, za ki kasance da daraja sosai a wurin mijinki da kuma Jehobah.​—1 Bitrus 3:1-6.

SHAWARA:

  • Ka tambayi matarka me ya kamata ka yi don ka zama maigida na kirki. Ka saurare ta sosai kuma ka ƙoƙarta ka yi gyara

  • Ka kasance da haƙuri. Zai ɗan ɗauki lokaci kafin ku fahimci yadda za ku riƙa faranta wa juna rai

2 KA MAI DA HANKALI GA ABIN DA KE DAMUN MATARKA

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: Ka sa bukatun matarka gaba da naka. (Filibiyawa 2:3, 4) Ka mutunta matarka kuma ka tuna cewa Jehobah ya bukaci kowane bawansa ya “zama salihi ga kowa.” (2 Timotawus 2:24, Littafi Mai Tsarki) Yin “magana da garaje” yana kama da “sussukan takobi. Amma harshen mai-hikima lafiya ne.” Saboda haka, ka lura da kalaman da kake furtawa. (Misalai 12:18) Ruhu mai tsarki zai taimake ka ka yi magana mai daɗin ji kuma cikin ƙauna.—Galatiyawa 5:22, 23; Kolosiyawa 4:6.

SHAWARA:

  • Ka roƙi Allah ya taimake ka ka guji yin fushi da kuma manne wa ra’ayinka sa’ad da kai da matarka kuke tattauna batutuwa masu muhimmanci

  • Ka yi tunani sosai a kan abin da za ka faɗa da kuma yadda za ka faɗe shi

3 KU TSAI DA SHAWARA TARE

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: Bayan aure, kai da matarka kun zama “nama ɗaya.” (Matta 19:5) Duk da haka, kowannenku yana da ra’ayinsa. Saboda haka, kuna bukatar ku yi ƙoƙari ku daidaita tunaninku da kuma yadda kuke ji. (Filibiyawa 2:2) Yana da muhimmanci ku tsai da shawara tare. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane ƙuduri a bisa shawara ya kan kafu.” (Misalai 20:18) Ku riƙa bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce sa’ad da kuke tsai da shawara mai muhimmanci.—Misalai 8:32, 33.

Ma’aurata suna aiki tare, suna wankin kayansu kuma suna wanke wanke a kicin

SHAWARA:

  • Ka ga wa matarka abin da ke zuciyarka, ba kawai ku yi taɗi ko kuma ka gaya mata ra’ayinka ba

  • Ka nemi ra’ayin matarka kafin ka tsai da shawara

a Jehovah is the name of God as revealed in the Bible.

KADA KU KUSHE JUNA KUMA KADA KU FID DA RAI

Kada ka ɗauka kai da matarka kun fi ƙarfin ku yi kuskure. (Zabura 103:14; Yaƙub 3:2) Ka riƙa mai da hankali ga halayen matarka masu kyau. Ku kasance da gaba gaɗi cewa idan kuka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma kuka yi haƙuri da juna, za ku yi nasara. (2 Timotawus 3:16) Jehobah zai albarkace ku yayin da kuke ƙoƙarin bin shawararsa kuma hakan zai sa ku ji daɗin aurenku.—Galatiyawa 6:9.

KA TAMBAYI KANKA . . .

  • Shin matata tana ganin na damu da ita kuwa fiye da kaina?

  • Ta yaya na nuna wa matata cewa ina ƙaunarta kuma ina daraja ta a yau?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba