Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • hf sashe na 2 pp. 6-8
  • Kada Ku Ci Amanar Juna

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ku Ci Amanar Juna
  • Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • 1 KU BA WA AURENKU FIFIKO
  • 2 KU KĀRE ZUCIYARKU
  • Ku Nemi Taimakon Allah don Ku Ji Daɗin Aurenku
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Zaman Aure
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Ku Manne wa Wa’adin da Kuka Ɗauka a Aurenku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Yadda Za Ka Daraja Matarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
hf sashe na 2 pp. 6-8
Miji yana rike wa matarsa lema don ta shiga mota, kada ruwan sama ya jike ta

SASHE NA 2

Kada Ku Ci Amanar Juna

“Abin da Allah ya gama fa, kada mutum ya raba.”​—Markus 10:9

Jehobah ya umurce mu da cewa: “Kada ku ci amana.” (Malakai 2:16) Wannan ya nuna cewa riƙon amana yana da muhimmanci sosai a aure domin idan babu riƙon amana a aure, ma’aurata ba za su yarda da juna ba. Kuma sai da yarda ake ƙauna.

A yau, cin amana tsakanin ma’aurata ya zama ruwan dare gama-gari. Idan kana so ka kāre aurenka daga wannan matsalar, wajibi ne ka yi abubuwa biyu masu muhimmanci.

1 KU BA WA AURENKU FIFIKO

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: Ku zaɓi “mafifitan al’amura.” (Filibiyawa 1:10) Ɗaya daga cikin abubuwa mafifita a rayuwarku shi ne aurenku. Saboda haka, kuna bukatar ku ba aurenku fifiko.

Jehobah yana so ka kula da matarka sosai kuma ku yi ‘farin ciki’ tare. (Mai-Wa’azi 9:9) Ya bayyana sarai cewa bai kamata ku yi watsi da juna ba ko kaɗan, amma ku nemi hanyoyin faranta wa juna rai. (1 Korintiyawa 10:24) Ka nuna wa matarka cewa tana da muhimmanci sosai a rayuwarka kuma tana da tamani.

Miji yana kawo wa matarsa shayi; miji ya iske matarsa tana dahuwa

SHAWARA:

  • Ka tabbata cewa kana keɓe lokaci a kai a kai don ka kasance tare da matarka kuma kada ka bar kome ya janye hankalinka yayin da kuke tare

  • A duk abin da za ka yi, ka riƙa tunawa da matarka

Mata da miji sun fita liyafa tare

2 KU KĀRE ZUCIYARKU

BIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: ‘Duk wanda ya dubi mace har ya yi sha’awarta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.’ (Matta 5:28) Idan mutumin da yake da aure yana tunanin abubuwan da za su riƙa tayar masa da sha’awa, to yana cin amanar matarsa ke nan.

Jehobah ya ce “ka kiyaye zuciyarka.” (Misalai 4:23; Irmiya 17:9) Idan kana so ka yi hakan, wajibi ne ka kiyaye idanunka. (Matta 5:29, 30) Ka yi koyi da Ayuba, wanda ya ƙulla yarjejeniya da idanunsa cewa ba zai taɓa kallon wata mace har ya yi sha’awar ta ba. (Ayuba 31:1) Ka ƙudura cewa ba za ka yi sha’ani da duk wani abin batsa ba ko kuma ka yi sha’awar wata da ba matarka ba.

Miji ya ajiye hoton matarsa akan teburinsa a wajen aiki

SHAWARA:

  • Ka nuna wa kowa cewa ka ƙuduri anniyar kasancewa da aminci ga matarka

  • Idan matarka ba ta son zumuncin da ke tsakaninka da wata, ka yanke zumuncin nan da nan

KA CIKA HAKKINKA

Ka gaya wa kanka gaskiya kuma ka yi ƙoƙari ka san kasawarka. (Zabura 15:2) Kada ka ji kunyar neman taimako. (Misalai 1:5) A duk lokacin da ka soma tunanin yin lalata, to, ka yi ƙoƙari ka canja tunanin. Kada ka karaya. (Misalai 24:16) Idan ka ci gaba da ƙoƙartawa don ka kasance da aminci ga matarka, Jehobah zai albarkace ka.

KA TAMBAYI KANKA . . .

  • Me zan yi don in daɗa samun lokacin zama tare da matata?

  • Shin matata ce aminiyata?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba